DAN KARUWA Writen by zahra surbajo Page 1-2mujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Sunday, January 13, 2019

Home DAN KARUWA Writen by zahra surbajo Page 1-2

Subscribe Our Channel



DAN KARUWA
Da sunan Allah zan fara da sunanshi zan gama da ikon Allah,surbajo sabon salo na kudine,wannan da sauran masu zuwa agaba bana kudi bane,Allah yasa sakon dake ciki ya isa inda zaa amfana dashi

Page 1-2

"Mummy don Allah kiyi hakuri ki rufamin a siri kar kije club dinnan don Allah ki tausayawa rayuwata da taki"cewar wani matashin yaro da shekarunshi bazasu wuce goma sha biyar ba,

Tsugune yake rike da kafafuwanta yana kuka,kallo daya zaka masa ka fahimci yana cikin tashin hankali me tsanani.

Cikin halin ko in kula matar ta fara magana cikin isa da izza tace. "Sultan kenan,wlh lamarinka ya fara bani tsoro,taya ina kasuwanci dan in rufa maka asiri amman kai kullum kawo min nakasu kake ga kasuwanci na," Hawaye ya share yace bakinshi na rawa. "Mummy kiyi hakuri don Allah abokaina tsokanata suke suna kirana DAN KARUWA, sunce kin cika yawo mummy ki zauna agida don Allah ki taimakeni"yakarasa maganar cikin matsanancin kuka.

Murmushi tayi sannan tace. "In kace ta mutane zakabi zaka mutu da talauci, niko yau wlh ba abinda ze hanani fita,in zakaje ka kwanta kaje ka kwanta,danni se dare"

Bin jikinta yayi da kallo yana kuka,sanye take cikin riga da wando masu matukar bayyana surarta,wanda sam bedace ta fita dasu ba.

Baki na rawa yace. "To mummy kidaura zani akan kayan kan ki fita kinji"

Dariya tayi tace. "Sultan problem,je ka daukomin zanin"

Ba musu ya mike da gudu yaje dakinta ya dauko mata zanin harda hijabi ya mika mata.

Bata musa mishi ba ta daura zanin tasa hijabin sannan ta dauki handbag dinta ta shafa gefen fuskarshi tace. "Ka kulle kofa kayi addua kaji,se na dawo"

Jiki ba kwari yace "Adawo lfy mummy"

Yanaji yana gani ta fice daga gidan,rushewa yayi da kuka ya fada kan kujera yana kuka me tsuma zuciya.

Ita ko tana fita, wani lungu ta samu ta cire zanin da hijabin daya bata tasa ajaka tayi gaba abunta.

Tana tafiya tana juya jiki,har ta isa bakin titi ta hau mashin.

Tana isa gurin club din tundaga bakin kofa matasa ke mata ihu suna kiran. "Lokacinki ne khady baby," Gaba daya gurin se tafi ake mata itako se juyi take cikin kartin mazan suna tafawa wasu kuma su rungumeta.

Cikin gurin ta karasa shigewa,inda ta nufi mashaya,

Kwalba uku ta siya na cordine bata bata lokaci ba ta shanyesu,mintuna kadan ta mike ta fara hada hanya,

Isa zakara ne ya hangota tana hada hanya da sauri ya nufeta,

DAN KARUWA

Writen by zahra surbajo

Page2

Yana zuwa janyota jikinshi yayi yana dariya,yace. "Khady baby kinyi wuyar gani"

Murmushi tayi tace tana kara shigewa jikinshi. "Zakara,kacika takura ne yasa nake maka wasan buya,kai bakasan kayi abu na marmariba,kai cinye du ne shiyasa bana son alaka dakai wlh,gaka da hannun yan dambe"

Murmushi yayi ya fara shinshinata yana laso wuyanta kamar wani mayunwacin kare,yace. "Khady baby yau zan miki biya me kyau dan akwai kudi ajikina,karkiji komai,wlh kishin ruwanki nake narasa ina zan ganki se yau Allah ya hadamu"

Dariya tayi ta lakace mishi hanci tace. "Shaidan de ya hadamu ba ruwan Allah"

Dariya shima yayi yace. "You are right"

Daga haka jan hannunta yayi suka nufi gurin masu bada daki,biyan kudin yayi ya karbi key suka shige dakin.

Suna shiga dakin suka shige jikin juna,kowa na kokarin nunawa dan uwansa shi gwanine.

Sautin numfashinsu kawai kakeji yayinda suka isa kan gado.

Sosai zakara ya dirji kudinshi dan sun kwana biyu basu hadu ba.

Itako tuni bacci yay gaba da ita me nauyi bata farka ba seda garin Allah ya waye.

Koda ta tashi wanka tayi tai sallah,sannan ta tashi isa zakara dan ya sallameta zata wuce.

Koda ya farka,yaganta sabuwar shaawarta ce ta kamashi,duk yadda taso ya barta yaki seda ya sake kauda bukatarshi.

Mikewa tayi ta maida kayanta,isa dubu talatin ya bata.

Wanda sosai taji dadin su.

Sallama tai masa ta dauki jakarta ta fice ta nufi gida.

Tana isa unguwarsu yara suka fara mata ihun karuwa,itako ko ajikinta,haka ta dunga wuce mutane sanye cikin shigar diban albarka.

Sultan dake cikin gida yana mata wanki,jiyo hayaniyar yaran dayaji ne yabashi tabbacin mahaifiyatshi ce ta dawo.

Jikinshi ne yayi sanyi,sanda ta shigo gidan batare da zani da hijab din daya bata ba.

Wasu hawaye ne masu zafi suka fara biyo fuskarshi Dakyar ya iya yima ta sannu da zuwa.

Amsawa tayi cikin walwala,tace. "Sultan ka ganni se yanzu ko wlh wani sabon kamu nayi shine na tsaya tare dashi kayi hkr kaji yarona,Allah yayi maka albarka"

Shuru yayi yakasa bata amsa,yana kallo ta shige dakinta baa jimaba yafara jiyo karar ruwa alamun wanka takeyi, Rasa abunyi yayi dan haka kawai rushewa yayi da kuka,

Muje zuwa. .surbajo for life daga mujallarhausa


No comments:
Write Comment