SIYASA KO K'ABILANCI
Number 34
Rayuwa tacigaba da tafiya cikin Nasarori da fuskantar k'alubale irinna rayuwa, wani mai dad'i wani akasin hakan, zuwa yanzu kam Amatallah tashigo gari, itama tazama 'yar hannu, yanda matan Uncle ke taku d'ai-d'ai da rawa da bazarsu haka itama takeyi, rayuwar gidan takoma ta competitions, kowa so take tazama gaba a zuciyar maigidan.
Iya k'ok'ari Uncle yanayi akan matan nasa, k'yautatawa iya gwargwado yanama kowacce, baki isa kisan wadda yafi soba a zuciyarsa, dan kowacce takasance agabansa nuna mata yakeyi babu ya ita, wannan yasa kowacce takejin kanta on top.
Duk abinda zakiyi mara k'yau agaresa bazaiyi gulmarki agaban 'Yar uwarkiba, sannan bazaici mutuncinkiba, Indai kun ke6e dagake saishi zaiyimiki kam, hakan yabada taimako Na musamman wajen hana kawoma juna raini a tsakaninsu, saidai kowacce tana tsantsar kishin mijinta, musamman ma Aneesa dabata iya 6oyewa, a salon iya taku kuwa sai Amatallah ta nunama Fateema bata iya komaiba, Dan ko agaban maigidan Amatallah bata ta6a nuna kishi ga 'Yar uwarta, har mamaki yakeyi, wani lokacin yakanyi wani Abu danyaga ko zata nuna 6acin ranta amma ko alamar hakan baya ta6a gani (dukda kuma tanajin haushin amma saita danne) wannan duk Anty maijiddah Ce ke d'orata a network😀.
Sukansu su fateemar abin nabasu mamaki, Aneesa takansha yima Amatallah abu amma koda afuska bata nuna mata tasan tanayi balle ma ta 6ata ranta, duk sun rasa gane lagon Amatallah.
Duk hanyar da Fateema zatabi ta 6atama Aneesa rai tasanta, amma takasa samun Na Amatallah, salon yarinyar Na bata mamaki da d'aure kanta, gashi kota k'udiri k'untatama yarinyar saita karya mata tanadinta ta hanyar son 'ya'yansu datakeyi, yanda Amatallah kema yaransu bazaka ta6a d'auka yaran kishiyoyinta bane, yanzu haka mah-mah (Aminatu) saita wuni a hannunta inhar batada makaranta.
Amatallah kuwa dukda tana kishinsu hakan baisa ta d'auki damuwar k'untata musuba a zuciyarta, gaba d'ayama hankalinta nakan karatunta, ta dage sosai kamar yanda kullum Anty maijidda da Nazeefa ke bata shawara, ita saima suyi Abu sau nawa batasanma sunyiba, harkar gabanta takeyi basu isheta kalloba, a salon kulada mijikam hummm, sukansu sunfara zama 'yan kallo, to kullum Fa'iza tsaye take akan Amatallah wajen koya mata salo-salo Na kissar kama miji, hakama Anty maijidda, gasu Anty furera agefe, kowadai tausayinta yakeji, ga maraici ga zama da kishiyoyi wad'anda suka girmeta nesa ba kusaba.
Nasarorikam ana samunsu fiyeda zaton mai tunani, Dan Uncle koda bai fito ya fad'aba musan Amatallah takafa bishshiyar gamji a zuciyarsa, wadda tasaki rassa da 'ya'ya tako'ina😉🤪.
Fa'iza ta haihu kusan wata hud'u kenan, su Amatallah ansha sunan baby (Munirat). Fa'iza ALLAH ya raya mana to.
A 6angaren Uncle ma abubuwa suna tafiya akan nasarori, yanzu haka suna rik'eda matasa masu yawa kusan 50 wad'anda shaye-shaye yafara ruguza rayuwarsu, suna kar6ar magani da horaswa akan wasu sana'oi. Saikuma masu lafiya wad'anda ayanzu haka suketa cuku-cukun sama musu wajen aiyuka a 6angarori daban-daban, sunkuma bud'e islamiyya daza'a ring a koyar da matasan ilmin addini da dabaru Na rayuwar, dukda k'arancin kud'i dasuka fara fuskanta hakan bai hanasu fara fad'ad'a ayyukan nasu zuwa wash local governments ba, musamman akan matasa 'yan shaye-shaye da had'a daba ta 'yan gani kasheni.
Wad'annan nasarorinne suka maida Uncle d'in busy sosai, ga iyali ga ciwon baba dukda Alhamdllh akwai sauk'i, ga harkar kasuwancinsa da Aikinsa, idan kagansa dolene ka tausaya masa har wata rama yayi ta yawaita zirga-zirga.
K'alubale kam suna fuskantarsa musamman wajen manyan k'usoshin k'asar, wasu suna ganin kamar wata jam'iyyar siyasa sukeson kafawa a kaikaice, suna yawanjin sukarsu da akeyi a gidajen redio ko talabijin musamman in ana hira dawani d'an siyasa.
Kokad'an hakan baya damunsu, saima alkairi yake zamo musu, Dan yakansa wasu masu nagartatattun halaye Dason cigaban k'asar da kishinta sukan kawo Kansu cikin tafiyar domin a dama dasu suma. aifa kafin kace mi sai manufofinsu suka fara fitowa fili, ayanzuma basai sunyi kiranyeba matasan dakansu suke kawo Kansu saboda suma fatarar babu da yawon tazubar ya ishesu, masu kwalayen result a akwati saisuka fara lalubowa suna kakka6ewa danufo ofishin dasu Uncle d'in suka bud'e domin kar6ar k'orafe-k'orafen Masan, masu raunin kasuwanci ko rashin madafa ma gaba d'aya suma suka fara tururuwar gangamin shigowa wannan k'ungiya.
Hummm hakanfa bak'aramin shankan su Uncle lamuran suka faraba, sunyi kiranye kuma an amsa harma amsawar tafi k'arfin bitalmaninsu, Dan ayanzu babu abinda sukafi buk'ata samada zunzurutun kud'in Shiga a tafiyar tasu. A 6angaren Islamiyya kam tagama cika mak'il da matasan da suke damuwa da raunin ko k'ishirwar rashin ilimin addinin Nasu su Kansu, malamai kuma magadan annabawa sunyima lamarin caffar fisabilillahi, dansu ajiye wasu daga cikin ayyukansu sun d'aura d'ammarar yad'a ilimi ga matasan koda hakan zai kawo mana raguwar wasu masifun, kullum nasiha da wa'azi maishiga jiki da 6argo shi Malaman kan zazzaga bayan kammala karatu a ajujuwanin dasuka kasance uku kacal, duk suncika harma sun batse ana Neman tallafin k'arin wasu.
Tofa ahankali lamarin wannan k'ungiya yafara haskawa, taurarinsu suka fara haske, dattijai da iyaye mata suka fara d'okantuwa daganin 'ya'yansu a tafiyar suma, hakama k'ananu 'yan siyasa masu Neman madafin iko da jama'a suka fara shirin k'utse cikin wannan k'ungiya danufin samun mabiya a matasan, saidai kuma tuni su Uncle sukayi tsawar datasaka masu rawar k'afa a 'yan siyasar ja baya koyin likimo Dan tsorata da gargad'in su Uncle Na ik'irarin Suba 'yan siyasa baneba.
Hakan kuma sai yaso zama k'ilu zata jawo bau, Dan masu ri6a66iyar zuciya kuma suka sami abun fad'a da kayayatu akafafen tazo mujita irinnan talabinjin rediyo da yanar gizo.
Kunnan uwar shegu su Uncle sukayi da kowa, tamkarma basusan anayi dasu baneba, sai suka bar karnika NATA haushinsu sukama sunata aikinsu dukda bitalmali Na neman agajin tallafin wasu 'yan kud'ad'e a tafiyar.
Amma abin birgewa su Uncle basukai wani k'orafi ga wani shahararre komai mulkiba, sai suka duk'ufa wajen baje hajarsu a kasuwa dawasu 'yan abubuwa dazasu kawoma k'ungiyar kud'in shiga koda babu yawane, aka kuma had'a hannu da matasan dasuka sami wasu k'ananun sana'oi a hannu ko aikinyi tasanadin k'ungiyar, haraji aka yankama kowannensu Na naira d'ari biyar akowane k'arshen sati, da wannan kuma za'a tallafi 'yan baya masu tasowa suma.
A wannan tsakanin ba'a cewa komai akan Uncle da sauran shugabannin k'ungiyar, Dan kowanne yaji ajikinsa, hattada kasuwancin wasinsu saida yad'an girgiza musamman ma Uncle daya maida komai nasa Na taimako, to ALLAH dai gafurin rahimun yacigaba da rik'e k'ungiyar da ikonsa dukda k'alubalen kud'i dasuka tsinci kansu. a yanzu dai haka dole sun ajiye ranar ashirin gawata domin zaman meeting akan k'ungiyar da fatara irinta kud'i datake fuskanta, yazamana dole su k'yalla idanu wajen lalubo mafitar kubta koda cigaban cimma manufofinsu da burukansu.
Yau takama Juma'a, kuma Amatallah ce da miji, dukda Aneesa ma tanata ahirye-shiryen ziyartar k'asarta ta haihuwa Dan ganin gida da danginta (Ghana).
Bayan sun fito daga lecture ta k'arshe Rita da goodness sukayoma Amatallah da Fa'iza rakkiya dansu sami abun hawa.
Tafiya suke suna zabga hira tamkar ba kusan a tare suka yiniba, Amatallah Na rik'eda muneerah wada tad'an fara woyo masha ALLAH.
Sund'an dad'e tsaye kafin su sami abin hawa, kasancewar yau juma'a anata hada-hadar masallaci.
Bankwana sukayi dasu goodness kafin kowacce tashiga napep tanufi gidanta.
***********
Kusan atare suka iso da yara wad'anda aka d'akko daga makaranta, duk suka rungumeta suna mata oyoyo, itama cikin farinciki ta rungumesun kafin ta tasasu gaba su shiga cikin gidan.
Babu kowa a falon, gidan shiru kamar babu mutane, watak'il matan gidan barci sukeyi kowasu uziri acikin d'akunansu.
Yaran kowa yashige 6angaren Uwarsa, Amatallah ma jakka da takardun hannunta kawai ta ajiye ta cire hijjab tashiga kichin Dan Neman abincin rana.
Tana tsaka da girki Fateema tashigo kitchen d'in, gaisheta Amatallah tayi kafin tace, "ina mah-mah?".
" mah-mah tana barci aunty yara, ya makaranta?".
"Wlhy Alhmadllh".
Ruwa Fateema ta d'auka tafita, a bad'ini kuma bawai d'aukar ruwanne yakawotaba, tazagayone taga mi Amatallah ke girkawane, Dan tasan yau maigidan zai dawo hannunta, agida kuma zaiyi lunch saboda inya dawo sallar juma'a baya sake fita kuma. fita tayi tana d'an ta6e baki, caraf kuma suka had'a ido da Aneesa da fitowarta kenan daga 6angarenta, itama da alamar gulmarce ta fiddota, (hakan yazame musu tamkar al'adar gidan, ranar girkinki sauran matan idonsu nakanki, kowa sotake taga yanda kikayi idan mijin yadawo nata tamasa mafiyinsa😆).
Kauda ido Fateema tayi tashige 6angarenta batareda ta tankama Aneesar ba, itama saitaja guntun tsaki tanemi kujera ta zauna a falon.
Amatallah kanta Fateema na fita tarakata da harara dafad'in magulmata anfara ma mutane lek'en asirinne, aiko k'afafunku sagaji babu maiganin mizanyi saiyaje kula.
Hohoho matan Muhammad Ahmad Labbo! Kuna shagalinku wlhy🤸🏻♀🤸🏻♀😂.
Har Amatallah tagama girkinta babu wadda tasake lekota, hakan kuwa yamata dad'i, tana tsaka da gyaran kitchen d'in tajiyo horn d'in boss, bata fitaba Dan tasan bama zai shigo da motar cikiba tunda zai sake fitane.
Bata kuma jiyo horn d'in nasaba kuwa sai takun tahowarsa, ta ajiye moper d'in hannunta ta d'auraye hannun dad'an goge fuskarta tagyara zaman d'ankwalinta sannan tafito, a falo suka had'u harya shigo, har yanzu Aneesa Na zaune afalon. Ko kallo bata ishi Amatallah ba tanufi mijinta suna sakarma juna murmushi.
Ta kashe masa ido d'aya yayinda sukazo gab da juna, murmushin yakuma mata, tawani kashe murya can k'asa yanda komin kusancinka dasu bazakaji mitaceba, tace, "barka da dawowa my jaan!".
Kad'an ya rankwafo ya sumbaci la66anta, kafin yace, "yauwa my heartbeat!".
Harga ALLAH Uncle baiga Aneesa ba, Amma Amatallah tanakan Sani, itama hannunsa takami ta sumbaci tsakkiyar tafin hannun.
Ya wani narke mata yana fad'in my best karki kaini k'asa a falonnan fa".
Jakar hannunsa ta kar6a tana wata shu'umar dariya, tai wani far da ido tajuya tana taku d'ai-d'ai, bayanta yabi da kallo kafin yafara takawa shima.
Aneesa da zuciyarta keneman fitowa ta danne da k'yar tace sannu da zuwa dear?".
Da sauri yakalli sashen da akayi maganar, cikin d'an kame-kame yace, " my Nessa dama kina falonnan?".
Wani murmushin takaici tayi tace, "a'a yanzu nazo". tana gama fad'a ta harari Amatallah tabar wajen.
Amatallah ma Harar tata tayi batareda tabari Uncle yaganiba balle Aneesar, suna had'a ido dashi kuma tasaki murmushi, " Uncle kafayima Anty Aneesa laifi".
Yad'an yamutse fuska yana kallon Ama...., "laifinmi my best?".
Step d'in tafara takawa tana murmushin mugunta dafad'in " saika shigo".
Binta yayi da kallo kawai, a zuciyarsa yace zaki kasheni da salonki khadeeja, ked'in tadabance......
Fitowar yaran yasashi maida hankali garesu, harsunyi wanka anmusu shirin masallaci, duk suka gaidashi ya amsa cikeda so da k'aunarsu. ''Yauwa my sweet children's ku zauna kar Wanda ya6ata jikinsa naje nima nayi wanka karmu makara salla, ina Ummah?".
Sahib yace, ''Abbu tana wanka".
"OK, to nima bara naje nayi ko".
A tare sukace to " Abbu ".
Tunda yashigo falon mayataccen k'amshin turaren da Amatallah ke saka masa yabugi hancinsa, shak'a yayi ya lumshe idanu kafin yak'arasa bedroom d'in. A toilet yajiyo motsinta, dan haka yafara cire babbar rigarsa.
Yana ajiyewa tafito itama, k'arasowa tayi inda yake, kowanne idonsa akan d'an uwansa, yana k'aunar yarinyarnan harma baisan iyakaba, sometimes idan tana Abu saita ringa d'ebe masa kewar Brother d'insa...
K'ok'arin cire masa bottles d'in rigarsa datakeyine yasashi dawowa hankalinsa, tamkar wani yaro haka ya koma mata, itace tamasa komai hatta da wankan da shirin masallacin cikin milk color d'in shadda, ta fesheshi da turare, shidai kallonta kawai yakeyi, 'Yar k'arama da ita sai wayon tsiya, abaya yana ganin kamar Amatallah zatana cutuwa agidan saboda k'ank'artatrta da k'arancin wayo, amma a yanzu yakula koda za'a cuceta saidai tawani fannin amma bawajen kulawa da mijiba, ta kowanne fage tagama kwarewa, har yana mamakin tamkar wadda ake koyamawa, dukda har yanzu salonta Na nuna kunyarsa tana nan tanayin kayanta, (wadda kunyar tata nakuma sakashi a shauk'in k'aunarta) dan idan 'yan kunyar nakanta takan masa Abu tamkar ranar suka fara had'uwa amatsayin miji da mata, shikansa saiyanjin kamar ranar aka kawo masa ita........
Yanata zancen zuci har tagama kimtsashi tsaf.
"Kayi k'yau my Uncle". tafad'a tana shafa fuskarsa.
Hannun yarik'e ya sumbata, kafin yajawota jikinsa ya rungume tana shak'ar dadd'an k'amshinsa.
Cikin sassanyar muryarsa yace, " ALLAH yamiki albarka khadeeja, yajik'ansu brother kinji".
Tana murmushi ta jinjina masa kanta, kafin tad'ago tana kallon fuskarsa, "my lollipop bara nabaka ko fura kad'ansha mana? banason kafita da yunwa".
Yanda ta narke masa haka shima ya narke mata, " no my heartbeat karmu makara fa, idan nadawo naci abinci kawai....."
Bata bari ya k'arasaba ta tashi daga jikinsa tana tura baki gaba. Saurin rik'o hannunta yayi ya maidota baya yana fad'in sorry my beat karki fushi, haba Amintacciya 'ya daga ALLAH, banito nasha ko kad'anne".
Tad'an kalleshi tana turo baki gaba, a shagwa6e tace, "really?".
Gira ya d'aga mata kawai danya kasa magana.
hannunsa takamo suka fito galo, ta zaunar dashi a kujera sannan tad'iba furar a frighte d'insa tasaka suga kad'an ta motsa, kusadashi tadawo, (hummm) mai makon ta zauna gefensa saita zauna a cinyarsa tana kashe masa ido d'aya.
Wani lalataccen murmushi ya sakar mata, ya sak'alo hannunsa a k'ugunta, " my beat karfa kimin Squeezing da kaya nida zanje masallaci".
Kofin furar tasaka masa abaki tana 'Yar dariya. amma batace komaiba.
Haka taita basa furar saida ya shanye bai saniba, ta ajiye kofin a Center table tana fad'in Uncle kafa shanye tas".
Bakinta ya sumbata, "yazanyi tunda 'Yar shagwa6a ta turkeni".
" wato Uncle turkekama nayi ko? Shikenan munyima fad'a karka kumamin magana harka dawo masallaci ehe.
Da sauri yakamota yana dariya, ya manne bakinsa kan nata. (Hummm dagananfa.....babu ruwana🤭).
Da k'yar tasamu ya saketa yafice yana kashe mata ido d'aya da d'aga mata yatsun hannunsa biyu alamar bye bye.
Gira ta d'aga masa itama tamasa alamar I love you da hannunta.
Tsayawa yay cak yana kallonta, harya d'an juyo zai dawo takoma bedroom d'insa da gudu tarufo k'ofar, tasan inhar ya kamata bakinta saiyaci k'aniyarsa, gashi time d'in masallaci nakuma k'urewa.
Sauka yay yana murmushi, dakumajin k'aunar Amatallah dake Shiga jininsa da 6argo. har yanzu yaran Na falo inda yabarsu, Shiga yay 6angaren Fateema suka gaisa, sannan yashiga wajen Aneesa itama, dukda tanata shamasa k'amshi bai damuba danyasan laifinsa.
Yana masallaci amma dukkan tunaninsa naga Amatallah, burinsa kawai a idar Yakoma gareta............✍🏻
_Ama.... kina zamani, walla banga laifinkiba,😉 murd'a kanbunki dak'yau karki saka wasa🤸🏻♀😻🤸🏻♀._
🤩👎🏻
One Luv my sweet fan's
*_ALLAH ka gafartama iyayenmj🙏🏻😭_*
No comments:
Write Comment