AUREN FARI kashi na tara page 9mujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Monday, January 14, 2019

Home AUREN FARI kashi na tara page 9

Subscribe Our Channel



AUREN FARI


         

KO KUN SAN INA DA WATA BOYAYYAR MASOYIYA A SOKOTO? DON ALLAH KU SA MATA ALBARKA SUNAN TA BILKISU ABDULLAHI GADA INA MATUKAR GODIYA BILKY WALLAHI TA NA GYARA AURE SOSAI

AI KUN SAN ME NAKE NUFI TUNDA NA AMBACI SOKOTO DA GYARA KUMA



Jikin ta yayi mugun sanyi, zuciyarta ta ringa tukuki, a yanda taji tarihin biyan ma'aikatan gidan a dubu talatin ita ce mai karamin albashi ma kamar yanda tafi kowa karancin aiki, dalilin biyan ma'aikata albashi mai tsoka shine don a fidda musu kwadayin sata a gidan, yana daya daga cikin gargadin da akeyi ma duk wata mai aiki banda sata. Amma ga mamakin umaimah sai dai taji labari ita kam ba a mata ba, wannan wane irin rashin tausayi ne?
   Ko yaya Abba ya ce ta ware mishi dubu cikin albashinta. Ta runtse ido *Ya Allah duk sharrin da ke cikin wadannan kudin ka fidda mun shi, ka kuma kareni da duk wata fitina*
  Ya kura mata ido jikin sa yayi mugun sanyi wani tausayi ya diri zuciyar sa bai daya, 
  Ya kalleta *sharri?* wane sharri kuddin ke dasu?
  Yanayin muryar da yakeyi ma mamee idan yayi laifi ya bada hakuri yayi mata. Ta kara tsanar sa a zuciya ko kallon sa bata kaunar yi.
  Ta mike tsaye ya daga hannu zai kara fizgota ta fincike ta watsa mishi dubu ashirin da da biyar jikin sa.
  Wannan kudin tattare suke da sharri don ba da zuciya daya kaban ba yau ka tabbatar mun da kai din mugu ne baka kuma da tausayi.....ya yunkura zai kamota tayi baya, ka lissafa ka ajiye magana yanzu na fara, kasan dukiyar taka bata gama isar ka ba ka kawo ma'aikatan da suka fi karfin ka? Can kudi, can kudi can kudi duk basu isheka ba sai ka ci hakkina?
   To kayi a banza wallahi dukiyar ka bata dada ni da kasa ba aiki ne ba kai nakewa ba wallahi kasan wacce ta kawo ni to darajar ta ko naira daya ka bani zan karba haka kuma zan iya mata aikin kyauta amma wallahi kai ko zaka biyani miliyan dari inshigo gidan nan kawai in fita kasan kayi kadan......wuf ya chafko ta..shut up!!!!!!! Ya daka mata tsawa.
  Ko gezau batayi ba, ji hargagi to cinyeni damisa ka tsaya ga yar cikinka kana wannan kurarin duk bai isheka ba aikin da nake kuma su ka sanya wa ido.......waje ya bankada ta ya janyo kofa ya rufe,
   Ya dafe kansa hannuwa biyu biyu ya runtse ido *Why why why????* kalmar da yake maimaitawa kenan.
   Ya kife bisa gado look at maganganun da yarinyar nan ke fada man  me ta dauke ni wai? 
  Ya runtse ido why all this rainin?
   Tafe takeyi tana rokon Allah ya kubutar da ita daga sharrin mutanen gidan amma abin mamaki gidan ba kowa yara duk sun tafi islamiya, goggo jummai kuma taje suna, goggo hansatu ce kadai zaune a tabarma tana jin redio, tayi sallama ta shigo, ko da ta dago taga umaimah sai ta kawar, ko ajikinta domin ta saba da hakan da kuma rashin bata abinci a gidan tun da ta fara aiki kullum ta dawo bata da kwano. 
 Ta zukunna can karshen tabarma goggo barka da yammaci. 
  Ta dalla mata harara an dawo?
 Eh, gashi anbiyani yau ta mika mata dubu biyar jikin ta na rawa, tana ganin kudi ta wangale baki, haba?
  Nawa suka Baki? Tayi shiru don ta gani da kanta sai kawai taga ta mike tsaye ta makure jikin ta taji ta inda dukan zai fara, sai kawai taga goggo na tikar rawa.
  Ta zaro ido ta bude baki.
  Wane gidan arziki ne kike aiki haka? 
   Umaimah tayi shiruuu au kai gidan fa ba'asan ina aiki gidan *Umar madaki* ba fa kawai sun tsaya a ina aiki gidan matar tazo 'yar uwar hajiya basu san wacece ba.
  Da na kawo dubu talatin din nan goggo yau sai ta goya ni. Mugu ya mun bakin ciki....... Ta dafa ta sauraranni ungo dubu boye taki ce, idan kowa ya dawo kice dubu biyu ne albashin    ki gata na ware har babanku kice haka ake biyan ki idan za a raba kuma damu ciki idan sun dawo.
  Duk wata zan ringa baki dubu ina daukar dubu biyu ina Sana'a kinga nice matsayin uwarki idan kin tashi aure 'yan siyayyar uwa ni zanyi. 
  To goggo umaimah ta fada tana washe baki da ajiyar zuciya. Bari in shiga wurin hajiya in dawo....jeki maza adawo lafiya.
   Ohhh ji goggo anga abin duniya, ta tabe baki ta fice zuciyarta fes!
     Ta biya shago ta siyo jikkar klin babba ta dari uku  ta kaima hajiyar. Ta ce kisa albarka an bani albashi ko kewaye kya wanke.
  Ta dunga sa mata albarka, akwai kudin ki fa wurina. Hajiya kiyi amfani dasu. A a wallahi ai na rantse bazan taba ba. Tayi murmushi ajiye mun tsaron lalura, kayan ma na dauki atamfa daya sauran da zaran naji zakuyi wani abu zan dunka miki ince ni na miki ko kuma can gidan *madakin* na sansu da shagali.
  Tayi godiya ta tafi ta siyo lalle na dari biyu. Ta fito kenan ta hadu da yaya Abba. Ta kwala mishi kira ta mika mishi dari biyar ba zato ya buga tsalle don yanzu ya gama maular hamsin. Ta ce albashi na dubu biyu ne nawa aka raba aka bani na baka kasan bazaka sami dubu.....ke share na gode ya watsa da gudu. Ta bishi da kallo wani abin sai aikin shaye shaye, 
    Kai kace gidan biki ake ko suna tun a kofar gida take jiyo hayaniya na rabon kudi. Ina ma yaban kudina chif, yau da nasha dadi gidan nan ta buga tsaki mugu kawai, 
    Dari biyu ta samu cikin kasafin da akayi tana karba ta yi daki ta kwaso tulin wankinta ta hau yi.
   *Madaki* kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye abubuwan da suka faru yau ke dawo mishi daya bayan daya, ko abinci ya kasa ci da ya zauna ko ya kwanta sai ya tuno gashi nan bisa umaimah ya haye ta da suka fadi,
  Ya fada kewaye ya sakar ma kansa shower amma da ya runtse ido hakan yake gani. Da ya bude sai maganganunta su dunga tariyo mishi.
   Ya dunkule hannu ya hada kanshi da bango ya fasa kara *wai tunanin na uban meye*
   Ya ga wannan bata fissheshi ya fito ya koma falon mamee amma bata dawo ba, ya dauki waya
 Mamee wai kina ina?
  Gani a hanya lafiya?
Ni kadai ne fa a gida......ina tafe ai nace kayi aure kakiya da kana da matarka yanzu wane kewa?
    Ya tsinke wayar kawai ya runtse ido *she won't understand* 
    Yan aiki keta kara kaina ya kalli wannan ya kalli waccen Sam ita bata wannan safa da marwan aikin ta tafiyin na zaune ko tsaye bata yawan motsa jikin ta .......ya buga tsaki kuma fa da yarinyar nan ce da yanzu mun gwabza fada, to wai meke sanya mu fadan? duk sai suka bashi haushi ya daka musu tsawa *kar wacce ta kuma fitowa idan ta shiga wacce ta fita kuma karta dawo*
  Zuwa yayi falon don ya sarara da tunanin umaimah amma suna Neman rikita shi.
   Me yasa na hanata kudin ta duka?
Ranta fa ya sosu, da alama bakinta yaso furta wani abu na lura da hakan, gobe me zata fadawa mamee? Nasan tabbas sai ta tambayeta.  
 Ba karamin 6aci ranta zaiyi ba kuma yarinyar nan tunda ta kirani da mugu babu dalilin da zaisa ta 6oye mata shaida zatayi man.
   Ya danna abin kiran yan aiki, agurguje suka karaso don basuji dawowar mamee ba .
    Waye ke da number uwani? Duk suka ce babu.
 Ya ce su tafi.
  Mamee na shigowa ya karbi wayarta, ya kuwa yi sa'a uwanin tayi saving da no.
   Ya na dauka yayi sama da sauri. Ta bishi da kallo. Ta girgiza kai agogo sarkin aiki wani abun ya tuna baiyi ba tayi ciki.
     Gidan yau gaba daya cikin nishadi ake. Umaimah tsumu tsumu ana fira da ita hada su dariya. Abin kara armashi kowa ya karbi number ta sun sa mata nasu.
   Mamaki kawai takeyi gidan ya zame mata sabo.
  Wayarta tayi kara har sau biyu taga number kawai ba sunan. Mamee kadai ke kiranta tayi tunanin ita ce, duk akayi tsit, hankalin kowa ya dawo kanta, tana dauka ta ce mamah biki kikaje halan naji shiru shiru.......
Ke natsu magana zanyi dake ya daka mata tsawa, tayi jimm
 Gabanta ya fadi . Kowa ita yake kallo 
Gobe idan kinzo.....eh mama..To sannu da zuwa ba komi goben da wuri zanzo.... Ke saurareni madaki....ta latse wayar.
 Ya hasala *What?* ya zaro ido yana kallon wayar. Ya kara kira zata fara ringing kenan yaga number busy
   Ransa yayi mugun baci ya kara kira a hasale the mtn  number you are trying to call is currently... yayi wurgi da tasa wayar..............

maman Abdallah



No comments:
Write Comment