lya Gani lya Kyalewa labarin wani ma harbimujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Sunday, January 13, 2019

Home › › lya Gani lya Kyalewa labarin wani ma harbi

Subscribe Our Channel



Daga mujallar hausa Wata rana wani maharbi yana yawo, sai ya tarad da wani maciji dutse ya danne shi, yayi yayi ya kubuta, ya kasa. Da macijin nan ya ga maharbi sai ya dube shi, ya ce, “In kana kaunar ka gana da Ma’aikin Allah, wannan mutun, ka tsarshe ni daga halaka. Kai kuwa
Allah ya saka maka da alheri.” Maharbi ya ce, “Ba fisshe ka ba na ke gudu, halinku na halittar duniya na ke jin tsoro, a yi muku rana ku kuwa ku yiwa mutum dare. Maciji ya lan kwasad da kai ya ce Subuhanalillahi, bawan Allah yaya za a fara wannan aiki? Haba, Allah ya sawaqa!”
Maharbi ya ce, “Tun da ka yi alkawari ba ka cutata, bari in taimake ka. Ai kowa da ranarsa Ban san inda Allah zai nufa kai kuma ka rama
mini ba.” Ya sa hannu ya dauke masa dutse. Cire dutsen nan ke da wuya, sai ya nuho shi fuu zai sare shi. Ya sa wani tsumman
gwadonsa ya tsare shi, ya kai wa gwadon sara kaf. Maharbi ya ce, “Da gaske ka ke yi ko wasa? in wasa ka ke yi dani don Allah bari,
irin wannan wasa ban gane masa ba.”
Maciji ya ce, “A’a’ wasa fa ina? To, bari ka
gani in wasa na ke yi. Kiyayyar da ke
tsakanimmu da ku ’yan Adam har 6oye ta ke? Ai ni idona idon mutum sai sara.” Ya sake kai masa sari kaf, ya tare da zane. Maharbi ya ce, “Tuna fa yadda muka yi, ka yi
alkawari ba za ka cuce ni ba. Ashe haka halin ’yan duniya ya ke yanzu?”
Maciji ya ce, “A to, ko da ya ke na yi maka wannan alkawari, ai ka san da mai hankali ya ji haka daga gare ni ya san ba ta kai ciki ba,
ko cikin littattafanku na mutane kuwa ma ai an
yarda idan mutum ya ga macucinsa ya hallaka
shi tun bai cuce shi ba. Ka san kuwa
tsakanimmu da ku kamar wuta da sa6i ne, in
akwai aminci.
Maharbi ya ce, “Duka abin nan da ka fadi bisa
hanya ya ke, amma ina rokonka abu guda.”
Maciji ya ce, “Mene ne? Fadi maza in ji in na
iya.”
Maharbi ya ce, “Yadda ka gama ni da Allah
har na yarda na tserad da kai, ni kuma ina son
kai kuma don Allah ka yarda mu shiga daji mu
sami Alkalai uku su yi mana shari’a. In sun ce
shari’a ta bayar a kashe ni, ka kashe ni. In sun
ce shari’a ba ta bayar a kashe ni ba, ka kyale
ni.”
Maciji ya ce ya yarda, a tafi. Ya shiga gaba,
maharbi na biye. Duk abin nan maharbi ba shi
da ko sanda balle baka, duk ya ajiye su cikin
bukkar gonarsa. Ba shi kuma da damar ya
karya, don kada maciji ya gane abin da zai yi
ya riga shi.
Suna cikin tafiya sai suka gamu da wani
tsohon doki. Maharbi ya bayyana masa yadda
suka yi da maciji, ya kuma tambaye shi abin
da ya gani a cikin wannan al’amari.
Doki ya ce, “Af, ba wani abin da na gani sai maciji ya cinye ka. Ai ku mutanen yanzu ba
ku kula da a yi muku rana ku yi wa mutum
dare ba. Ni da sa’an nan ina tsakar karfina
wajen wani Bature na ke, ya sa ni cikin
sukuwa. A lokacin nan daga in ciwo masa fam
hamsin sai in ciwo masa dari. Im mun tafi
filin sukuwan nan, in na dubi nisan wurin sai in
yi kamar in ki zuwa, sai in tuna da azabar
kaimi da bulala. Ka san filin nan kome karfin
mutum, in ya yi kuwwa, na wancan gefen ba
ya ji. Duk da haka sai dai in jure in yi ta gudu
kamar raina zai fita, Baturen yana bisa
dafa’an, sai buguna ya ke yi, yana suka
kamar bawansa. In dai tattake sai na wuce
saura.
“A lokacin nan fa ba ya son abin da ya taba
ni ko kadan, ko dan haki ya gani ya like mini a
gashi sai ya cire mini, in na yi dauda ya sayi
sabulu ya sa wani bakin mutum maketaci ya je
rafi ya yi mini wanka. Yana fita da ni sai ya
haye ya je cikin daji ya yi ta sukuwa da ni a
banza, wai yana more wahalarsa, don Baturen
ba ya biyansa kudin aikinsa sosai, bayan ya
gaji ya wankeni im fita fes. Abinci kuwa sai irin
wanda na ke so a ke ba ni. Ka ga duk kudin
nan da na ke ci masa wajen sukuwa bai ishe
shi ba, sai da ya sa ni cikin wani irin aikin
banza, sai su hau mu, su dauki sanduna su
riqa bin wani makodi suna bugu. Im ma
makodin nan ya sami kafarka sai ka yi kamar
ka ce wayyo Allah don zafi. Da yawa ana cikin
yi sai wani ya rauka maka sanda. Ka ga yanzu
don ya ga na tsu fa, ya kuwa bubbuge mini
kwauri, ya sude ni sarai har ba na iya ci wajen
sukuwa sai nema ya kashe ni, wai in huta ko
an ta6a hutu da mutuwa? Da na ga ran nan ya
jawo bindiga sai na sheko. Ka ji butulcin ’yan
Adam.”
Maciji ya ce wa mutumin, “Ka ga wannan
Alkali wajena ya ke.
Mu ci gaba, mu ji na sauran biyun.”
Za su wuce, doki ya ce wa maciji, “Me ka
ke jira da shi? Kai dai ba ka san halin
jemammen nan ba. Tsaya kadan in gaya maka
tarihinsu. Ka san kunne ya girmi kaka.” Maciji
ya tsaya.
Doki ya ce, “Da sa’ad da mutane ba su gane
dabarar yin gari su gina gidaje su yi benaye su
shiga ciki ba, cikin dawa su ke zaune tare da
kakannimmu. Abin da namun daji ke ci, shi su
ke ci. Ran nan da kirinkinsu na mutane, ba sai
daya ya sami wani katon dutse ba ya jefi dan
manyan dawa, har ya fasa masa ido? Da
manyan dawa ya ga haka ya ce namun daji su
bazu, duk inda aka gan shi a kashe shi. Da
kakannimmu suka ji haka, sai suka nemeshi
suka tsegunta masa abin da a ke ciki, don in
zai 6oye ya 6oye. Ka san mutum ba wanda ya
fi shi tsoro, sa’an nan kuma ga mugum aiki,
duk sai maganan nan ta ruda shi, ya durkusa
kamar da lalama, ya roki kakannimmu su 6oye
shi, ya dauki alkawarin kome su ke so ya yi
musu. Suka kai shi gida suka hoye.
“Suna nan, da ya ga kamar za a gane shi, ya
rarrashe su su gudu su koma wani wuri. Suka
yarda suka tashi. Ya dauki ’yan kayansu suka
koma wani dawa, suka sami wani fili, ya nemi
ganyaye ya yi musu bukkoki. Shi kuwa da
sauran ’yan danginsa suka tsaya daga waje
suna gadinsu. Ka ga yanzu don tsananin
butulcinsu na ’yan Adam, da suka ga sun yi
karfi, sun kuma fi kakannimmu yawa, sai suka
kore su daga cikin bukkokin nan, su suka
maye. Kakannimmu suka so su koma su gaya
wa manyan dawa, suka ga ko sun koma ba za
a yarda da su ba, don kurarsu ta rigaya ta yi
kuka a kan munafunci. Sabo da haka suka
dangana bisa ga wannan hukuncin Allah, na
gaba ya koma baya. Dubi don Allah yanzu, im
ba don butulcin ’yan Adam ba, bawammu na
gado ya ce wai shi zai tona mini asiri haka, har
ya dauko bindiga wai zai harbe ni? Ka san
yanzu in da abin shari’a ne, muna da iko mu
sayad da ’yan Adam mu ci abinci.”
Maciji ya kama hanya za su wuce, doki ya
waiwayo ya ce, ”Ba kasan wani abin haushi
ba kuma.”
Maciji ya ce, “Me?”
Doki ya ce, “Wai ashe duk kyale su da muka yi
suna wahalshe mu, tsammani su ke tsoro ne.
Ba su san mun kyale su don mu more su ba
ne. Ka ga yanzu dole ko ana ruwa sai su fita
su yiwo mana ciyawa, su yi noma su ba mu
hatsin mu ci. In sun ki kuma mu kama su dai
dai mu sayar, halal dai ne.” Ya dubi
mutumin nan, ya ce, “Don Allah dube shi ya yi
saqo sai ka ce mummuni, amma butulcinsa ya
fi shi.” Ya juya ya kama hanyarsa, yana
cewa, “Ku qare can, an dai gaya maka gaskiya
ka ki, wai kai son shari’a. Ka san dai kowa ya
bar naman kura, ba zai sa kura ta bar nasa
ba.”
Maciji ya shige gabe mutum na biye, har
suka tarad da wani biri kan itace. Da
ganinsa maciji ya sa baki ya kira shi. Da
ya zo ya kwashe duk abin da ya gudana
tsakaninsa da maharbi ya gaya masa.
Biri ya ce, “Af, cikin wannan har sai ka tsaya
neman Alkali? Hala ba ka san mutum ba. Dube
shi fa da kyau ka gani. Duk duniyan nan akwai
wanda ya fi mutum butulci? Dan'uwammu ne
fa, an halicce shi da kafa hudu kamarmu, don
tsananin rigima kaga yadda ya dage biyun na
gaba, ya rika yawo bisa na baya. In ka dubi
fuskarsa tsai, ka dubi tawa, ka ga lalle akwai
dangantaka a tsakanimmu. Duk cikin dabbobi
ba mai kai irin namu sai mutum. Dubi hancina
da hannuwana, ka kuma dubi nasa. Amma
yanzu fa tsakanimmu ba ko gaisuwa. Da
manyan dawa zai yarda mu gama kammu mu
fadawa mutane duk mu halaka su, mu shige
benayen nan nasu, mu yi ta cin duniyarmu a
huce.” Biri ya sake duban mutum, ya ce, “Allah
wadan naka ya lalace! Don Allah yaya ka qona
gashinka haka? Ina wutsiyarka? A! Wannan
akwai kirinki. Dubi fa da sunammu daya biri,
amma ka ga shi sai ya ce a riqa kiransa wani
abu wai shi mutum.” Ya harari mutum ya ce,
“Ho dan nema, mummunin kare mai cizo! M,
kada in tsaida ku, in kana kashe shi ka kashe
shi, da wani son a sani, yaji da kwarin miji. Ka
ji dai an ce kashe macucinka tun bai cuce ka
ba.” Ya fada cin ’ya’yan itace abinsa.
Maciji ya dubi mutumin, ya ce, “To, yanzu fa
Alkalai biyu ke nan wajena, saurammu daya a
zartad da hukunci.”
Idanun maharbi suka cika da kwalla, ya ce, “I,
mu tafi gaba, Allah ya kyauta.”
Suna tafe, maharbi na kirfa abin da zai yi wa
maciji ya rasa. Sun fiara gaba kadan sai
suka gamu da kare. Da hango shi maharbi
ya ce, “Ya kai, wannan kare, don
Allah ka zo ka ji wannan al’amari. Ina
yawona sai na tarad da wannan maciji dutse
ya danne shi, yayi yayi ya fita, ya kasa. Ya
gama ni da Allah in taimake shi, na duka na
cire dutse, ya fito. Ka ga da ya fito sai ya ce
wai ba wanda zai sara sai ni. Don Allah fa ka
ga an tasam ma gaskiya wurin nan?”
Da kare ya ji sai ya ce, “In kuna so in yi muku
shari’a, sai mu koma in ga yadda ka same shi.
Don bai kamata ba Alkali ya yi shari’a sai bisa
ga abin da ya kyauta ganinsa, ko kuwa ya sami
adalai da suka shaida.”
Mutum ya ce, “Gaskiya ne.” Suka dunguma su
duka uku zuwa wurin dutsen nan.
Da suka isa, kare ya ce wa maciji, “Kwanta
yadda ya tarad da kai.” Maciji ya kwanta. Ya
kuma dubi mutum, ya ce, “Kai kuma mai da
dutsen yadda ka tarad da shi bisansa.”
Maharbi ya ciccibi dutse ya ji6a bisa maciji.
Kare ya dubi maciji, ya ce, “Haka ya same ka?”
Maciji ya ce, “I.”
Kare ya ce, “To, zauna nan har Allah ya
kawo maka wani wanda karambani ya yi
masa yawa ya fid da kai.”
Suka watse suka bar shi nan ya mutu. Maharbi
ya yi ta murna bisa ga wannan hukunci na
kare. Shi ya sa yanzu maharbi bai gama
kowa ba da karensa, da ka bugam masa kare
gwamma ka bugam masa da.
Da Waziri ya qare wannan labari, don
dadinsa sai Sarkin Sirika ya dauko jaka guda
ya ba shi. Da Hazik ya ga haka sai ya ce,
“Au! Ni ma abin da ya sa aka ka da ni ai don
ba a koma wajen almara ba ne.”
Waziri ya ce, “Ita ka iya?”
Hazik ya ce, “I mana.”
Waziri ya dubi Sarakunan nan ya ce, “Gobe in Allah ya so da almara za mu cika labarimmu Allah ya ba ku nasara. Kai ko, Sarkin Sirika, in kana son labarai ka je gida ka huta ka aiko in zo har can garinka, im mun kare sha’anin haraji in gaya maka labarai sai ka gaji, ka ga dai su na ke, Ubangiji kuwa bai hana mini kwakwalwar tunawa ba.” Mutane suka watse, suna “Allah ya kai mu gobe.”
Da aka koma gida Hazik ya ce wa Sarkin Sirika, “Gobe, Allah ya ba ka nasara, kana shirin ganin inda gwanin rawa zai fadi.” Sarkin Sirika ya ce, “Hazik, don Allah raba kanka da wuya Hazik ya ce, “In kana tsammani ba’a na ke,
Allah ya kai mu goben, ai ka gani da
idanunka Sarkin Sirika ya ce, “To, amin wannan labari daga mujallarhausa.com.ng

No comments:
Write Comment