NA
khadija usman
Domin samun complete Hausa novel tame gari a shiga nan
shiganan na daya 1
A koda yaushe bazan gaji da bawa masu bina pc akan in tura musu tame gari hakuri ba,wallahi banida time din wannan kuyi hakuri abin ne dayawa kunada yawa sosai kuma kowa da wanda yake so,ya kk so inyi ina iyakar kokarina wajen ganin na saurari kowa,amma duk da haka ban tsallake zagi da cin zarafi ba a gurin wasu,amma nagode sosai kuma ni yanzu ba abinda zai batamun rai insha Allah yadda nafara littafin nan tunda ni nayi niyya to saina karasa shi da yardar mai duka dan haka ina mugu mugun sonki all tame gari fans
Qara dubawa tayi sosai ko kayan sun zube kasa ne,amma taga wayam ga sanyi daya fara kodar ta yana shiga jikinta,to ya kenan? ko tantama batayi tasan kayan baya suka fada,to ya zatayi kenan,yankewa kanta tayi kawai tayi wankan inta gama ta leko intaga wannan me siffar aljanun tace ta miko mata kayan,in kuma bataga kowa ba tayi shahada ta dauko da kanta,da wannan tunanin ta qara sa hannu cikin ruwan dan ta fara wankan,yana nan dai da zafin sa ga sanyi da iska nata busowa abu ya hadar mata goma da ashirin.
Wani dutse data gani ajiye gefe ta dan raba ta zauna akai,tana jiran ruwan ya huce tayi wankan,ta jima a zaune jin sanyi na niyyar illata ta yasa ta matso da ruwan ta dinga diba kadan-kadan tana watsawa tana gantsarewa tare da rutse ido.
******
Tana fita direct gidan maigari tayi tana zuwa kuwa gida ya amsa kuwwar zuwanta inda aka shiga hirar yaushe gamo ,har maigari suka shigo shida su Habeeb suna biye dashi nan suka zauna aka dasa sabuwar hira.
Ganin dare nayi ne yasa maigari cewa Dije "ke tawajena!! anan zaki kwana ne?,dan naga dare yafara yi.
Ai kaima kasan dole in kwana a gidanka,shekara ta nawa marabin da in kwana, kaga kuwa dole in barje haushina.
Ja'ira baki abin magana,to su 'yan gidan naku ai cewa sukayi inda kike nan zasu zauna to kuma gashi kin gudo kin barsu ya kenan?
To ai nayau ne kawai yanzun ma inada dalilin kwanan anan, dan haka ka kwantar da hankalinka gobe tun da asuba zan koma.
Miye abin tashin hankalin acikin kwanan naki uwar magana!!!
cewar Baba Habiba matar maigari uwar gida,
to ai naga duk kamar bakwa farin ciki da kwanan da nace zanyi ne,duk da mun jima bamuga juna ba.
to ai kece Dije ba'a kewarki wlh duk inda kika zauna sai an so ki karawa motarki mai, saboda addabar mutune da kike yi da rashin jin ki,ai ni naga kokarin wannan yaron (Daddy)da sauran mutanen gidan da suka iya zama dake har tsawon wannan lokacin banji ance kin sabauta wani ba.
Inji wa ya fada miki bata sabauta wani ba ?
cewar Naseer dasai yanzu yayi magana,shi kuwa Habeeb nacan yanata dannar waya ,Sajida yake kira amma bata daga ba,jira yakeyi data daga ya tashi ya basu wuri danshi baya son yawan surutu.
Au ta gwada muku halin kenan ya cewar Baba.
kallon Dije Naseer yayi yaga yadda ta tsareshi da ido saiya tuno duk artabun da akayi da su abaya,ya so kora jawabi amma ya waske yace,
Ai Baba ba karamin dadin zama ke da khadija ba,yarinya ba ruwanta salaha da ita nutsatstsiya,ga hakuri da sanin ya kamata ga.......
ai tun a nan yakamata ka tsaya dan in jikina duk kunne ne ban yadda ba tunda naji ka ambaci kalmar hakuri nasan kadai fada ne kawai ammaina Dije take da hakuri,yarinyar da tun tana goye ko kallonta kayi indai bai gamsar da ita ba saita rama,bare kuma data fara tasawa,dan haka sai dai ka fadawa wasu halin Djje badai ni ba, dan duk wanda ya kwana da sanin haihuwar Dije a garin nan,to yasan da zamanta,dan in tana guri bata buya
managed mujallarhausa.com.ng
managed mujallarhausa.com.ng
Salam please where can I get the complete book
ReplyDelete