AUREN FARI NA 33
........ Duk ka tsorata 'yar mutane don ubanka.
Ya kyalkyace da dariya, yarinyar can wallahi bazaku gane ba gwala ni takeyi kamar kwallon kafa.
Karya kakeyi kai da kace babu macen da zaka bi, baka ba mace hakuri, baka......Alhaji anji.
Suka kwashe da dariya. *waya fada maka barno gabas take*
Umaimah nata, kuka mamee sai lallashi takeyi, jamila ta turo baki *Yaya dubi mutanen ki*.... Ta tabe baki sa ji dashi kilibabbu.
Kinga sarkar da ta sanya jiya? Murja ta fada tana tabe baki.
Jamila ta ce ki duba wuyanta kiga ta yau tafi ta jiya sau hudu.
Aikin banza waccen figaggar yarinyar cinye su zatayi har babu.
Ai kunji tayi shiru har yau taki cewa da mu komai saboda munafunci da shegen zurfin ciki. Yaya ta fada tana mazurai.
Ku jira Ku gani waccen maryam din data fifita fiye da mu zanci ma uwa munafukan banza..... Yo yaya bakiga kudi ma ita take ba ajiya ba?
( uwa daya uba daya gaskiya basu duba wa mamee ba. Allah ya raba mu da hassada )
Hassada ciwo ce wallahi, uwa daya uba daya akwai ta kawai ta wasu tafi ta wasu fitowa,
Mamee ta ringa raba atamfofi super, da barguna masu kyau na kasashen waje, ga wasu robobi, bokitai, glass cups, kai kaya barkatar, su yaya sai tabe baki sukeyi *Karyar banza*
( wai arziki kamar na madaki a kirashi da karya )
Akayi budar kai, kowa na ba umaimah kudi kamar yanda al'ada ta nuna su yaya na zaune turus!
Bayan an maida umaimah sama suka baje bisa carpet, yaya ce me korafi *Naga ana wucewa da tuwo mu banda mu?*
Hafsat tayi tsagal, tuwo zakuci? Yanzu kuwa, ta lodo masu har sai da yaya ta ce wannan tuwo kamar rugaye?
Ta yi dariya tare da yada masu magana ta ce wai don kuci Ku dauka kamar kullum* Duk sukayi damama ta wuce bata bi ta kansu ba ta ciko wata yar roba da man shanu ta kawo masu da ruwa da lemu sannan ta rike kugu da yake takadara ce ta ce *Sai me?
Yaya cikin yake ta ce tuwon ya mana yawa da akwai leda dana dauki biyu saboda dumame....... Jamila ta yi karaf nima zan dauki biyun nan........ Hafsat ta ce baku da matsala yanzu zaku ga tuwo, ta je ta sami ledoji hada Wanda zataci ta lodo masu sannan ta ciko wasu robobi da miya ta ce duk gashi ai tuwo baya hada fada gidan mamee.
Duk abin nan mamee ma bata San wainar da ake toyawa ba. Kawai masu tare fada ne Allah ya kawo mata.
Dama hafsat hake take dasu wurin party ance iyaye su fito kawai su yaya suka kalleta suka ce *Sai kuje iyaye* haka kuwa akayi ta tafi ta dunga rawa daman mamee ta bata himilin kudi ta ringa watsama ango da amarya.
Ganin yanda hafsat keyi duk sai suka tsargu rashin kyautawa ya dan damesu. Suna gama cin tuwon suka sulale ko bankwana.
( kai Allah ya ganar da masu irin wannan hali ).
Karfe tara abokai sukayi sukayi su rakashi ya ce wallahi shi zai kai kansa.
Sai da ya sallami kowa sannan. Suka mishi addu'a sosai saboda sunji dadin bikin sa yanda ba a zato ya bada gidan man shi daya duk Wanda zai tafi yaje yayi full tank.
Banda kayayyaki da ya raba, generator, spare tire , mashin mashin, kai abubuwa barkatai.
Ya shigo karfe goma da kwata, mamee na ciki ita dasu hafsat, ya leka suka gaisa ya fito mamin ta biyoshi, ya zauna falo, mamee na gaji.
Ta yi dariya da gajiya *madaki* sannu da kokari wallahi ka cika *Da* na gode Allah ya shirya maka iyalinka ya baka zuri'a dayyiba.
Ammkinnnn mamee love, ya kukayi da mutanen ki?
Tayi yar dariya kai lafiya qalau, girgiza kai kawai kawai yayi yasan fada mishi ke bata son yi.
Uwani duk ta tayar da hankalin ta. Ta fada tare da langabe kai.,
ya danyi murmushi kawai,
Ta kalleshi don Allah ka dubi maraicin yarinyar nan kaji tsoron Allah. Wallahi rikon maraya yana da matukar muhimmanci ga rayuwar dan Adam. Da mutane zasu gane falala da kuma dunbin rabon da mutum ke samu idan ya kyauta ta wa maraya lallai da wasu sun ringa bi gida gida suna sallamawa duk in da yake su dauko.
Mamee zan kwatanta na sani.
Ta harareshi na san ka da zafin kai madaki uwani yarinya ce kada ka biye mata don Allah.
Kadai ji yan surutan da yan uwana keyi idan ka rike kanka idan kuma ka banzatar wallahi zan dauki mataki....... Zan kiyaye mamee.
Jikin sa duk yayi sanyi.
Ta mishi nasiha sosai yayi shiru kawai.
Ta mike mu kwana lafiya sakonka nacen sama an kai. Ta shige ciki.
Ya mike a hankali yana zuwa yaga katon tire cike da gasassun kaji an rufe da foil paper.
Gaban sa ya fara faduwa, kamar bazai iya Shiga ba.
Tana zaune bisa gado kuka kawai takeyi , kukan maraici na ban tausayi.
Ya bude kofar a hankali.
Ta hadiye wani miyau dunkulalle cikin ta ya kada ya bada kulululu.......
Ya zauna shiruuuuu...
Ya dake ya fara magana cikin kakkausar murya . idan kin gama kukan zo nan in magana dake.
Tayi shiru ya daka mata wata tsawa..... Ta matso da sauri.
Ya yaye gyalen malama ki man shiru kinji.
Ta sunkuyar da kai.
Yayi kasa da murya, umaimah kamar an miki auren dole? Wannan kukan naki yayi yawa gaskiya, ya kamota ya maidota kusa dashi.
Umaimah wallahi ba abinda zan miki kinji har na rantse, zan tafi dakina ma in kwana, amma sai kin mun alakwarin zaki daina wannan kukan kuma zaki ci abinci...... Tayi saurin daga kai. Yayi murmushi good.
Sha re hawayen toh, ya fada yana gogewa da hannu.
Jeki yo alwala muyi sallah tukun .
Ta mike tayo alwala sannan shima ya shiga, bayan sunyi raka'a biyu kamar yanda sunna ta koyar ya dafa kanta yayi mata addu'ar da manzo SAW ya koyar sai ya fita ya dauko naman da ice cream.
Tana zaune ta zabga uban tagumi ya dan kalleta, ni zan baki ko zaki...... Tayi saurin kai hannu ta dauko ta fara ci.
Yayi yar dariya *Mrs madaki*...... Ta harareshi ya kyalkyace da dariya ba injini ba inji *yan jarida*
Da ta janye hannunta sai yace au kin koshi? To kawai in kwana anan......sai ta mayar da hannu haka har taci sosai, ya mika mata ice cream din sha kiban muyi kama kama inji yara.
Ta dan harareshi kadan, yayi murmushi.
Ya kalli jerin akwatunan lefenta ya ce *umaimah an bani da rowa* haka kika dawo da kayan baki ba dangi ba? Ana rabawa iyaye da yan uwa fa,
Ai na basu, ta fada kamar mai koyon magana.
Haba? Ya fada ganin ta danyi magana.
Ta ce Allah.
Su wa kika ba?
Ta dan kalli jakunkunan
Na ba baba shadda goma, su goggo atamfofi uku uku, itama luba na bata lesuka da kayan shafa, baba ma na bashi turaruka, an dibar ma dangi yankunnaye da atamfofi suma, sannan na bada *Hajiya ta* leshi uku, atamfofi biyar.
Cewa zakiyi kin rabar da kaya kaf! Sai kawai Tayi murmushi shi fa ya kirata da mai rowa yanzu kuma ta bayar yace ta rabar.
Ya kalleta yaushe rabon da ya ga murmushin ta?
Haka ya dan jata da fira har daya saura sannan ya ja mata kofa ya tafi dakin sa.
Yana fita ta saki ajiyar zuciya *Ohh madaki ikon Allah*
Barci ya dauketa saboda gajiya ga kuma kuka anci.
Shi ko sai kusan uku ya samu yayi barci yana ta gyare gyare.
Cikin kunnenta aka kira sallah, ta tashi da sauri ta shiga tayo wanka gudu gudu ta sanya wani material ruwan kwaiduwar kwai,sai da ta gama sallah sannan ta dan shafa mai ta zauna lazimi, shidda da rabi ta shiga ta wanke kewaye, sannan ta zo ta gyara gadon ta jera jakun kunan duk ta dan gyara fasalin dakin sannan ta kunna abin turaren kamshi mai kamar kwanon glass ga sanyin A.C, ta dauko wasu turarukan ta na cikin lefe ta feffesa ma labulan daki., nan da nan dakin ya rikice da wani irin kamshi.
Ya dan kwankwasa, tayi saurin zama kamar tana lazimi kafin ta ce *Shigo*....Yana sanye da jallabiyar da ta siyo mishi, ya dan turo a hankali sanyi da kamshin dakin ya daki hancin sa,
.......ina kwana, ya dan lumshe ido *Morning sweetheart* yayi suka bisa gadon mamee ta ce idan kin gyara gado baki so a bata miki, ta mike tana ninke abin sallah tana murmushi.
Shi ne kika bari na makara ko? To Alhaki kanki.
Ta dan saci kallon sa kadan, ya tashi zaune miko mun littafin can, tana zuwa ya damko hannunta, kilibabba kina ta wani satar kallon miji kedai umaimah baki waye ba, ta kyalkyace da dariya tana noke fuska,
Ya cacumota bari dai in fidda miki kunyar nan ta daina takura mu........ Ta fasa ihu wayyo na shiga uku wallahi na daina wayyo mameee.......... Ke tsaya saurara wasa nakeyi ya tallabo fuskarta, wasa nakeyi ya jaddada mata da kai.
Duk illahirin jikin ta ya rikice da kyarma.
Ya kwantar da ita bisa kirjinsa yana bubbuga bayanta, ya hakuri wallahi wasa nakeyi.
Ya dan runtse ido, lallai yana da babban aiki wannan tsoron na umaimah yayi yawa.
Ya dagota, ki saki jikin ki dani ki yarda dani please bana son wannan tsoron da dararewar.
Ta danyi murmushi, ya ja hancin ta yar rainin wayo kamar ba matsiwaciyar yarinyar nan ba.
Kwanta muyi barci...... Ta zaro ido mamee zan gaido.
Ya dan muskuta ya cire jallabiyar daga shi sai vest da dogon wando ta dan basar don tana motsawa zai jata jikin sa.
Ya mika mata, malama to lunke tunda cirewar ma kin kasa taimakawa, ke kam kina ban kunya, idan miji zai cire riga sauri akeyi a cire mishi kar ya wahala...... Ta danyi murmushi . ita dai duk bata amince da shi ba.
Ya maida kansa bisa filo don Allah kizo mu koma barci....... Bana ji. Ta ce a hankali.
Ya fizgota ke bazan dauki wannan gidadancin ba.
Na shiga.....yayi saurin rufe mata baki da hannu shiru kiyi barci.
Tayi lamoooo kirjinta na harbawa, ya kai hancin sa a wuyanta lallai amaryar nan kina zuba kamshi. Gabanta ya fadi ta fara raba ido.
Yana ta faman zolayarta, a hankali a hankali taji ya fara saukar da numfashi alamar barci ya daukeshi.
Ta saki ajiyar zuciya ciki ciki a hankali. Ta bashi kamar minti biyar sannan ta zame jikinta a hankali ta maida mishi filo, har zata fita taga yadan ja kafarsa alamar kamar yana jin sanyi, sai ta koma a hankali ta rufe shi da bargo sannan taja kofar ta fice,
Ta sauka, dakin mamee tayi ma tsinke, bata ciki ta zagaya dakin baki wadanda basu kai ga tafiya ba su naryam hamza, hafsat, Aunty Aisha, duk dai aminan ta suna nan.
Sai kawai ta fada toilet ta wanko shi fes!
Sannan ta shiga gyara mata dakin, duk wani sako da loko sai da ta sharo shi,
Sa'annan ta goge ta feffesa abun kamshi, ta kusa karasa gyaran wodrop kenan taji mamee ta rafka salati bayanta.
Mi zan gani ni *Rabi*, uwani??????
Ta yi sauri ta isa kusa da ita tana murmushi tare da zukunnawa *Mamah* Ina kwana,.
Ta kamota ta mike, wanene ya turo ki wannan aika aika? Ina madakin?
Ta dan dukar da kai *Yana barci*........koma sama maza ga kalaci can an hau dashi...... Kuji mun yarinya ni jikar buzaye kai *Uwani* al'amarinki sai ke.
Ta danyi dariya kai mamah bari in karasa gyaran...... Ke bani son iyashege kinji zaki koma daki ki huta ko sai..... *Kai mamah* ta fada kamar zatayi kuka, ta dauko kwadon zuba shara ji fa abinda na sharo dakin nan in banyi ba waye zaiyi?
Su mansurah ta bata amsa. Ta zumbure baki ta juya tana ci gaba da lunkewa.
Ta matso kusa da ita, zaki wuce ko sai na kwakkwada miki wannan ludayin da ke hannuna. Maza kije ki tado mun shi kice yazo su Aunty salma zasu tafi dasu Hafsa....
Ta danyi murmushi Allah dawowa zanyi ko na kirashi ta wuce ...... Ta bita da kallo tana yar dariya *Uwani* ....... *Uwani* ikon Allah.
Allah dai ya baku zuri'a dayyiba. Wannan kuruciyar taki gara yazo ya daukeki kubar kasar can kya dan natsu kisan kin girma ja'ira.
Tana buda kofa ya farka, amma sai yayi shiru cikin bargo.
Ta zo tayi tsaye kansa tana alwalar kuda, ya fara dariya saboda tabbas yasan kiransa zatayi.
Ta dan juya *Kazo inji mamee*, yayi shiru
Ta kara cewa, shima ko motsi,
Ta ce *Madaki*........ Ya lumshe ido kamar bakinta sunan ya fara fitowa,
Kaji mamee na kira shima yayi shiru,
Ta dan sa hannu ta yaye bargo kawai ya fizgota ta fada saman sa,
Innalillahi dama kana jina?
Ba'a sani ba, ke dai ba kauya ce an fada miki ko a kauye yanzu ana tada miji haka?
Ya kara matseta, haka zaki dan hawo sannan ki dan mun kiss kamar haka...... Ya mata a goshi sai ki fara cewa *Honey*......... Kina dan shafani.......ta wuntsula ta sauka ya kyalkyace da dariya.
Mikon rigar in saka, tana daukowa ta wulla mishi ta sauka da gudu ya fara dariya.
Shi ya kai su Aunty bintar airport da kan sa.
Kiri kiri mamee ta hana umaimah saukowa dole ta tafi daki tayi zaune.
Ya shigo da sauri rike da kayan kalaci, yarinyar nan abinki akwai son kai shine kika gama cika cikin ki ni ko in gane?
To zo muci mamee ta koroni yau. Tayi murmushi nima koroni tayi.
Ya kyalkyace da dariya kyaleta gobe kamar yanzu mun bar mata gidan.
Ta kalleshi da sauri,
Ya kai dankali a baki Dubai zamu honeymoon......................
Good morning Maman Abdallah
Godiya ta musamman ga *Salamatu dahiru* ( MZ) Ayi mun uzuri yau post daya zanyi. Wannan.
No comments:
Write Comment