Hakika zakayi kuka in kaka karanta.
Sayyada Aisha (RD) ta tambayi manzon Allah (SAW) akan saukan wannan ayar:
(Ranar da za a canza qasa banda wannan qasar da sammai)
Tace masa to a wannan ranar(rananr da ba qasa b sama) ina zamu kasance(yan Adam)? Se manzon SAW yace ranar zamu kasance akan SIRADI(Ma'anar kalmar:hanya)
A lokacin da za'a wuce siradi lokacin babu wani abu babu kuma ko wani guri se guri uku kawai:
JAHANNAM(ALLAH KA KIYAYEMU
ALJANNAH(ALLAH KA SA DAMU
SIRADI
Manzon Allah yana cewa :
Wanda ze fara tsallaka siradi ranar ni ne da al'ummata. Farkon al'ummar da zata fara wuce siradi shine alummar Annabi MUHAMMAD(SAW) ALLAH MUN GODE MAKA.
Ma'anar siradi;
Shin wai menene ita wannan siradin????
Itace ranar da babu sama babu qasa ba komai se wuta da Aljannah.
Sannan kafun ka kai aljannah dole se ka wuce jahannama don haka za'ayi wani bridge a saman jahannama wanda ake kiranta"SIRADI"(WATO HANYA) tana saman jahannama wanda se ka bi takanta har qarshenta sannan ka isa qofar aljanna
Alokacin da ka isa kofar Aljannah za ka tarda manzon Allah SAW a gaban yana tarban yan Aljannah(Allah ka bamu Ajannarka)
Siffofin siradi:
1 siranta tafi gashin kai siranta
2 tana da kaifi tafi wuqa kaifi
3 tana da matsanaicin duhu kuma a qarqashin ta jahannama ne baqiqqirin
(Wuceta ma babban azaba ne
4 kowa zai dauki zunibinsa a bayansa ya goya. Idan zunubanka suna da nauyi to zata sanya maka tafiya a slow WA IYAZUBILLAH
idan kuma zunubanka basu da nauyi zaka wuce da sauri kamar walqiya
5 a kanta akwai manyan karnuka a kasanta kuma qayoyi ne masu kaifin gaske suna yayyanka maka qafa
6 zakaji sauti me tsananin qara ga duk wanda qafarsa ta kufce ya fada a jahannama (Allah ka kiyayemu)
A lokacin manzon Allah ze kasance a qofar Aljannah yana kallon duk wanda ya daura kafarsa akan farkon siradi yana masa addu'a yana cewa: Ya Rabbi Sallim. Ya Rabbi sallim
MASOYINMU MANZON ALLAH
A ranar ko wani bawa yana ganin mutane a gabansa wasu suna fadi wasu suna tsira amma ranar ba ruwan kowa da kowa
Ranar da bawa ze ga babansa,mamansa, amma ba ruwansa dasu(sbd tsananin ranar) saboda a lokacin kowa ta kansa yakeyi.يوم ﻻ ينفع مال و ﻻ بنون إﻻ من أتى الله بقلب سليم
An ruwaito cewa sayyada Aisha wata rana ta tuno da ranar Alqiyamah se ta fashe da kuka se manzon Allah ya tambayeta me sata kuka?? Se tace na tuno ranar alqiyamah ne shin kuwa a ranar zamu tuna da iyayenmu?? Ranar masoyi ze tuna masoyinsa??
Se manzon Allah yace eh se de a wuri uku kawai: lokacin da ake auna mizani, da lokacin da za'a bawa kowa littafinsa, da kuma a gurin siradi
Kuyi haquri(inji masoyinmu manzon Allah S A W akan fitintinun duniya muyi jihadin kanmu kuma mu taimaka ma juna sbd mu hadu aljannah... girmanta yafi sama da qasa
Allah ka sanyamu daga cikin masu tsallaka siradi lafiyaaaa
Bayan wannan duka (ya kai dan Adam me hankali) kana tunanin akwai wanda ya cancanci ka yi masa bakin ciki ko hassada ko tsana ka batar da ayyukanka a banza????
NASIHA(ka bar halitta ga mahaliccinsu)
Ka tambayi kan ka shekarana nawa? nawa ya ragemun? Shin kana da guarantee zaka rayu bayan awa daya?
Ko bayan minti daya?
Kai ko bayan second daya nan gaba??
Kar ku manta iblis(la'annanne) yana cewa Allah na rantse da izzarka da jalalarka se na batar dasu muddin rayukan su na jikinsu
Allah kuma yana cewa Na rantse da izza ta da jalala ta se na gafarta musu muddin suna neman gafara ta (ASTAGFIRULLAH WA ATUBU ILAIKA)
Yan uwana yawaita istigfari
ALLAH KASA WANNAN TUNATARWA DA NAYI YA ZAMA SADAKA A GARENI DA IYAYENA DA YAN UWANA GABA DAYA da duk wanda ya tura wannan sako ga yan'uwansa da kuma wanda ya karanta
No comments:
Write Comment