MATA AYI HAKURi Idan aurenki yayi jinkiri ko kika rasa miji da wuri mujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Friday, January 11, 2019

Home › › MATA AYI HAKURi Idan aurenki yayi jinkiri ko kika rasa miji da wuri

Subscribe Our Channel


MATA AYI HAKURi Idan aurenki yayi jinkiri ko kika rasa miji da wuri tuna sayyida khadija (r.a), da tayi hakuri sai Allah ya azurta ta da mafi alkairin mazaje a gidan duniya kuma Annabin Allah (s.w.t.)..

🧕 Idan Allah bai nufeki da yin aure ba gabaki daya  tuna da nana maryam (a.s) da yadda Allah ya mata albarka a gidan duniya da lahira, kuma
ya yabeta da kamewa a cikin littafinsa mai tsarki, dukda cewa batayi aure ba...

🧕idan Allah (s.w.t) bai azurtaki da haihuwa ba kiyi hakuri kada ki daga hankalinki ko ki damu da zancen mata: ki tuna matar Annabi Zakariyya (a.s) da tayi hakuri sai Allah ya dubi zuciyarta ya azurta ta da haihuwa dukda da cewa ta tsufa
shekarunta sun tafi...

🧕🏼 Idan Allah ya jarrabeki da azzalumin miji mai sabawa Allah da bijerewa hanyarsa  sai ki tuna
Asiya matar fir'auna, da Allah ya dubi zuciyarta sai ya sanyata ta zamto daka cikin shuwagabannin matan Aljannah..

🧕dan Allah ya kaddara miki rabuwa da mijinki ko ya sake ki sai ki tuna fadin Allah (s.w.t) Idan suka rabu to Allah zai azurta kowa da rabonsa

Idan Allah yayiwa mai gidanki rasuwa kada kiyita sanya damuwa a zuciyarki har ki rinka furucin cewa bazaki taba samun wani wanda ya*
*fishi alkairi ba:* ki tuna ummu salma matar Abu- salma, (r.a), da mijinta yayi wafati sai Allah ya canja mata da wanda ya fishi shine Annabi Muhammad (s.a.w.), sabida kasancewarta daka cikin masu cewa:Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, a lokacin musiba...

Ki sanya a zuciyarki cewa arzikin Allah yana zuwa.. Kada ki kwallafa ranki ko kisa ido ga arzikin da Allah yayiwa wata ta kusa dake ko yar'uwarki..

Ki sani cewa Allah yana sane da halin da kike ciki, domin shi ya halicceki, kuma ya fiki sanin kanki da damuwarki...

Kada ki damu da abunda mutane ke furtawa a kanki, domin basuda abinda suka isa su miki idan ba wannan zancen ba, kuma shi baya cutarwa...

Allah ya shiryar da bisa tafarkin Shari'a....

No comments:
Write Comment