Kiwon lapiya Iya kibarka iya kankantar kwakwalwarkamujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Sunday, January 13, 2019

Home › › Kiwon lapiya Iya kibarka iya kankantar kwakwalwarka

Subscribe Our Channel






Daga mujallar hausa Wasu kwararrun masana a fannin kwakwalwa na nahiyar Turai sun gano cewa kwakwalen masu
kiba 'yar kankanuwa ce,kuma tana ci gaba da rage girma a duk lokacin da jikin mutum ya kara nauyi. Masanan sun dai wallafa sakamakon wani zurfaffen bincike da suka yi a mujjalar kiwon lafiya ta Neurology Kwararrun dai sun gudanar da gwaje-gwaje kan akalla mutane dubu 9,600 wadanda suka gabatar da kawunansu a gare su a matsayin
zakarun gwajin dafi.Yawancin wadannan mutanen na da shekaru 55 zuwa sama kana kashi 19 cikin dari masu kiba ne. A tashin farko,

masanan sun auna nauyin jiki,
fadin cinya da kuma tsayin kowane mutum,inda daga bisani suka auna girma yawan fararen sinadaren da ke cikin kwakwalwar kowane daga
cikin ta hanyar amfani da fasahar MRI. Mutanen da aka yi wa wadannan gwaje-gwajen sun bada cikakkun bayanai ta'ammalinsu da
taba-sigari,motsa j,ki karfin gudanuwar jini a jiyoyin jikinsu da kuma shekarunsu na haifuwa.
An gano cewa dukannin wadanda kibar jikinsu ta wuce iyaka, kwakwalwarsu 'yar kankanuwa ce
duba da ta 'yan lenge-lenge wadanda ke motsa jiki lokaci zuwa lokaci


No comments:
Write Comment