ABUBUWAN DA SUKE HADDASATA CIWON HANTA Hepatitis A:- Abinda Yake Haddasata Shine Wani Kwayar Cuta da Ido Baya Iya Gani Mai Suna”
Hepatitis A Virus” (HAV). -Hepatitis B:– Hepatitis B Virus (HBV). -Hepatitis C:- Hepatitis C Virus (HCV).
Sannan Yawan Shan Giya, Guba (toxic substances), Matsalar Garkuwar Jiki (Autoimmune diseases), Yin Amfani da Kwayoyin
Magani Ba Bisa Ka’ida Ba, Gado (Genetic cause), da sauransu Na Iya Haddasa ciwon Hanta..HANYOYIN KAMUWA DA CUTAR CIWON HANTA
-Hepatitis A:- Gurbatuwar Abinci Ko Ruwan Sha Wanda Ya Gaurayu da Kashin Wani Mai Dauke da Cutar, Wanda Kwaruna (Flies) Ke Yadawa, da Kuma Hada Jiki (Body Contact) da Sauransu. -Hepatitis B:- Idan Aka Sanyawa Mutum Jinin Mai Dauke da Ita (Transfusion of infected blood),
Yin Amfani da Allura Ko Razor Masu Dauke da Kwayar Cutar (Use of infected sharp objects), Daga Uwa Zuwa Danta (Mother to Newborn),
Lokacin Saduwa da Mai Dauke da Cutar (Sexual contact), da Sauransu.
-Hepatitis C:- Sanyawa Mutum Jinin Mai Dauke da Cutar (Transfusion of infected blood), Amfani da Allura Ko Razor Mai Dauke da Kwayar Cutar
(Use of infected sharp objects), Musayar Abubuwan Tsafta Wanda Mutum Dayane Ya Kamata Yayi Amfani Dashi ( Sharing of personal
hygiene implements), da sauransu.
YADDA AKE GANO CUTAR A JIKIN DAN ADAM Ana Iya Gano Cutar Hepatitis (ciwon Hanta) Ne A Jikin Mutum Bayan Alamunta Sun Fara
Bayyana, Daga Nan Sai Ayi Gwajin Jini Biyo Bayan Zukar Jinin Mutum.
.
YADDA AKE MAGANCE CUTAR HEPATITIS Maza garzaya asibiti mafi kusa da kai/ke don saduwa da ma’aikacin lafiya da darar ka/kin fara
Jin alamomin dana ambata a sama.
HADURAN DAKE TATTARE DA WANNAN CUTA Babban Hatsarin Dake Tattare da Wannan Cuta
Shine; Hantar Mutum Zata Iya Lalacewa ta Yanda Dole sai Dai A Chanza Masa Wata, Idan Kuma back Allah Ne Ya Kiyaye Ba to Mutum Na
Iya Rasa Ransa. YADDA AKE KARE JIKI DAGA AFKUWAR CUTAR
Ana Iya Kare Afkuwar Wannan Cutane ta Hanyar Yin Allurar Rigakafi. Hepatitis Vaccine sunan
Allurar. Ita Kuma Ana Yiwa Mutum Ne da Zarar An Haifeshi, Sai Kuma A Sati Na Shida, Sati Na Goma, da Kuma Sati Na Goma sha Hudu da
Haihuwar Jariri/Jaririya. A Dunkule Ana Kiran Alluran da Takwarorinsu da Suna “Pentavalent Vaccine”. Sai Kuma Inganta Tsaftar Jiki Data
Muhalli, da Kuma Kiyaye Hanyoyin Kamuwa da Cutar.Allah ya gyara
No comments:
Write Comment