Banbancin duniya da lahiramujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Saturday, January 5, 2019

Home Banbancin duniya da lahira

Subscribe Our Channel


BAMBANCIN DUNIYA DA LAHIRA

DUNIYA: babu tabbas
LAHIRA : akwai tabbas
DUNIYA: akwai mutuwa
LAHIRA : babu mutuwa
DUNIYA: akwai samu idan aka rasa
LAHIRA : babu samu idan aka rasa
DUNIYA: akwai rashi idan aka samu
LAHIRA : babu rashi idan aka samu
DUNIYA: karya ce
LAHIRA : gaskiya ce
DUNIYA: akwai najasa
LAHIRA : babu najasa
DUNIYA: tana gushewa
LAHIRA : bata gushewa

DUNIYA: akwai tsanani ga muminai
LAHIRA : akwai dadi ga muminai

DUNIYA: akwai dadi ga mushrikai
LAHIRA : akwai tsanani ga mushrikai
DUNIYA: masu tsoron Allah sune ake wulakantawa LAHIRA : masu tsoron Allah sune ake girmamawa

DUNIYA: mafi yawan masu kudi suna cikin jindadi LAHIRA: mafi yawan talakawa suna cikin jindadi
DUNIYA: gidan da ba'a bambanta mumini da kafiri LAHIRA : gidan da ake bambanta mumini da kafiri

wannan shine kadan daga cikin bambancin duniya da lahira,
ya kai 'dan uwana a musulunci, ina maka nasiha da kaji tsoron Allah kayi adalci a cikin addininka ka guji zalunci, domin zalunci yana kama da shirka, ka guji karya domin tana kama da bautawa gumaka.

ya kai musulumi ka sani cewa ba zaka zama mumini ba, har sai ka kasance kamar haka:

1 sai kaji tsoron Allah a cikin sallar ka
2 sai ka hakura da yawan wasanni
3 sai ka zama mai bada zakka
4 sai ka kiyaye farjin ka daga zina
5 sai ka zama mai alkawari
6 sai ka zama mai amana
7 sai ka zama mai kiyaye sallolinka

haka kema 'yar uwa sai kin kiyaye da wadannan abubuwan sannan zaki zama mumina kuma kamilar mace a cikin al'umma sannan kuma ki zama uwa ta gari

Allah yasa mu dace, idan ka samu dama ka tura wannan bayanin zuwa, wasu al'umma, yin hakan zai sanya ka samu lada mai yawa a wajen Allah, domin ka yada abun da yake mai kyau, amma idan baka tura ba babu laifi a gareka, sai dai kawai ka zama marowaci, kuma ka zama daga cikin wadanda basa hani da mummuna, kuma basa umarni da kyakkyawa,  Ya Allah kajikanmu ka yafe mana kura-kuranmu kada ka vssanya riya a cikin ayyukanmu 

No comments:
Write Comment