SABUWAR SHEKARA TASU'A DA ASHURA DA CIKA-CIKImujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Saturday, January 5, 2019

Home › › SABUWAR SHEKARA TASU'A DA ASHURA DA CIKA-CIKI

Subscribe Our Channel


Darasi na Biyar-(5)

‘YA’YANSA ANNABI SAW;

*1-Abdullahi R.A*

Abdullahi R.A: Ana masa laqabi da Dahir da Dayib abin da yasa ake masa laqabi da Dahir da Dayib saboda an haife shi cikin musulinci,ya rasu yana yaro dan qanqani.

*2-Al Qasim R.A*

 

Qasim R.A:Wannan Da na manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasalam da shi ake masa alkunya (AbulQasim) an haife shi kafin manzanci ya kuma rasu kafin manzanci yana yaro.

*3-Ibrahim Mu’azzam R.A*

Ibrahim Mu’azzam R.A,An haife shi a madina ya rayu shekara biyu babu wata biyu ya rasu kafin rasuwar Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam da wata uku,ranar da ya rasu rana tayi kusufi, Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya tashi ya yi huduba mai tsanani domin kada mutane su Dauka rana ta yi kusufi ne saboda mutuwar dansa. 

Ibrahim Mu’azzam ba Nana Khadija bace ta haife shi,Nana Mariyatu Kibdiya ce mahaifiyarsa.

*4-Zainab R.A*

Zainab R.A :Ita ce babba acikin ‘ya’yansa an haifeta shekara goma kafin Annabta Dan innanta ya aure ta (Haulatu bintu Kuwailidu) sunan mijinta Abu Asim ta rasu a Madina shekara takwas bayan hijara.mijinta ya rasu zamanin kalifanci Sahabi Umar. 

*5-Rukayyatu R.A*

Ruqayyatu R.A :Ta auri Usman ibn Affan Khalifa na uku,ta haifan masa da AbdulLahi wanda ya rasu yana da shekara biyar ko hudu. Ruqayyatu ta rasu bayan yaqin Badar da kwana uku.

*6-UmmuKulsum R.A*

UmmuKulsum R.A: Ita ma bayan rasuwar ‘yarta Nana Ruqayyatu sai ta auri mijin ‘yarta wato sahabi Usman ibn Affan ta rasu a wurin sa shekara ta uku bayan hijira,ba ta haihu da shi ba.Saboda auran ‘ya’yan manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam guda biyu yasa ake ma sahabi Usman laqabi da Zunnurain, amincin Allah ya qara tabbata a gare su baki daya.

*7-Fatimatu Zahara R.A*

Fatimatu Zahara R.A: Mace ce wadda take duniyar kallo ce a wajen kyau,saboda Allah ya yi mata tsananin kyau.Ta yi kama da Manzon Allah sallahu alayhi wa alihi wasallam kama ta qarshe da ka ganta kaga Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam, tafiyarta irin na Annabi ta auri sahabi Aliyu ta haifan masa ‘ya’ya guda biyar *Hassan da Hussain da Zainab da UmmuKulsum da Muhusin,Muhusin ya rasu yana qarami.Zainab ta auri AbdulLahi dan Jaafar wan sahabi Aliyu, ita kuma UmmuKulsum ta auri sahabi Umar bn Kattab kalifa na biyu.Ta rasu bayan mutuwar babanta da wata goma sha shida,shekara ta sha daya bayan hijira ranar talata uku ga watan Ramadan*

Nana Fatimatu ita ce shugaban mata agidan aljanna.

*JIKOKIN ANNABI SAW*


*1-Hassan R.A*

Hassan ibn Aliyu ibn Abi Dalib: mahaifiyarsa ita ce Nana Fatimatuz Zahara ‘yar Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam an haife shi a Madina 15 ga watan Ramadana shekara ta uku bayan hijira,Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ne ya rada masa suna Hassan ya kuma yanka masa rago da hannunsa,Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam yabar duniya sahabi Hassan na da sheka goma.Sahabi Hassan kyakkyawa ne matuqa ya yi kama da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam daga fuska zuwa cibiya, yana da fara’a sosai ga haquri da kwarjini, kuma mutum ne mai kyauta.Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam yana tsananin sonsa sosai har yana yin masa kirari da shugaba yana cewa *“Wannan dan nawa shugaba ne zai sasanta tsakanin jama’ar musulmai.Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya ce shi ne shugaban matasa a Aljannah yana da hangen nisa da kaifin tunani,lokacin da babansa sahabi Aliyu ya yi niyyar zuwa Kufa sahabi Hassan ya hana shi zuwa ya ce “ina mai baka shawa baba kar kaje. Shine kalifa na biyar bayan mutuwar Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya zama kalifa ne bayan mutuwar babansa, kuma da kansa ya sauka ya ba sahabi Muawiyya shugabanci domin maslaha* Ya rasu shekara ta arba’in da biyu 42 bayan hijira sakamakon guba da ya ci a abinci,ana zargin tsohuwar matarsa ce tasa masa guban.Kafin ya rasu ya roqi Nana Aishatu da tayi masa alfarma a rufe shi a dakinta kusa da kakansa Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam Nana Aishatu ta yarda a rufe shi kusa da kakansa,amma Marwan ya hana a rufe shi kusa da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam sai aka kai shi maqabartan baqia.

*2-Hussain R.A*

Sahabi Hussaini an haife shi shekara daya bayan haihuwar wansa Hassan,shima ya yi kama da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam daga cibiya zuwa qasa, shima Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ne ya sanya masa suna Hussaini.Lokacin da ‘yan tawaye suke qoqarin kashe sahabi Usman bn Affan sayidina Aliyu ya tura Hassan da Hussaini su je suyi gadin gida khalifa Usman bn Affan.Ya yi shada 10 ga watan Muharram a Karbala sakamakon wasiqu da ‘yan Shia suka aiko masa ya zo za su yi mashi mubaya’a da ya zo sai ya gane yaudaran sa suka yi,bai ga kowa ba sai rundinar UbaidulLahi ibn Ziyad,ranar 9 gawatan Muharram sahabi Hussaini ya ce ma jama’arsa gobe akwai yaqi tsakani na da gwabnan Kufa duk mai son komawa gida ya bi dare ya tafi,rundunar gwabnan Kufa su 4000 shi ko sahabi Hussaini ‘yan rikiyarsa 72,gari na waye wa sai yaqi ya varke,aka fafata aka fafutuka sahabi Hussaini ya nuna shima barde ne domin ya kashe jama’a masu yawa kafin yayi shahada.  Ga sunayen wadanda suka kashe sahabi Hussaini *(A)Zur’atut Tamimi ya fara saransa a kafada daga nan sai*

*(B)-Sinanu Dan Annas ya soke shi da mashi a maqogwaronsa ya kuma qara cakansa da mashin a qirginsa*

*(C)-kafin Sahabi Hussaini ya kai qasa sai Khuli al-Asbahi ya sa takobi ya sare kan sahabi Hussaini.( Ya Allah kar kai rahama ga wadannan mutanan da suka kashe sahabi Hussaini Ya Allah ka tabbatar da la’antarKa ga wadan da suka kashe Hussaini) kafin a kashe sahabi Hussaini ya nuna jarunta matuqa* 

Wannan yaqin ya faru ne bayan mutuwar sahabi Muawiyya da shekara biyu shi kuma Yazidu Dan sahabi Muawiyya yana Sham.Bayan sun sare kansa sai suka dauki kan sahabi Hussaini suka tafi da shi Sham daga baya aka kai kan Sahabi Hussaini Madina aka rufe shi bayan kusan sati da faruwan yaqin.Ya Allah ka qara aminci ga jikan Annabinka ya Allah Ka qara Daukaka darajansa amin.Ibn Taymiyyah ya yi mummunar addua ga waxanda suka kashe sahabi Aliyu da dansa sahabi Hussain duba Minhajuj Sunnah na bn Taymiyyah.


*3-Muhsin R.A
*4-UmmuKulsum (matar Sahabi Umar) R.A*

Wannan ya nuna mana a fili cewa sahabi Aliyu da sahabi Umar babu tirjiya tsakaninsu domin ga shi har sahabi Aliyu ya aurar da ‘yarsa Ummu Khulsum ‘yar Fatimatu jikar Mazon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wasallam ga abokinsa Khalifa Umar Allah Ya qara ma su yarda baki Dayansu,har kuma ta haifar masa yara guda biyu Zaidu da Ruqayyah,suma Ahlul Baiti ne kuma ta kasance matarsa har lokacin da aka kashe shi kisan gilla yana sallah a masallaci da subahi.

Duk wadannan Nana Fatimatu ce ta haife su
.5-Ummatu R.A*, ita kuma Nana Zainab ce ta haife ta.

*6-Abdullah R.A* Dan Usman,shi kuma da ne a wajen Nana Ruqayyatu  Allah ne mafi sani
Mu hadu a darasi na gaba insha Allah.

No comments:
Write Comment