AUREN FARI kashi na takos page 8mujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Monday, January 14, 2019

Home AUREN FARI kashi na takos page 8

Subscribe Our Channel


AUREN FARI

           

UWA MAI BADA MAMA  YOU ARE THE BEST MOM EVER AUNTY HADIZA YAHAYA TUKUR MAMAN AMINA I LOVE YOU SO MUCH YA ALLAH YA KARA DAN KON KAUNA TSAKANIN KI DA UNCLE YA SHIRYA MIKI ZURI'A

Mamee idanun ta nakan waya bata lura da kidimewar da umaimah tayi ta. Tana ci gaba da latsa wayar cikin laluben wata number ta ce maza kije ki karbo babu ruwanki da shi da kin karbo ki sauko abinki. Ta karasa maganar tare da juyowa ta kalleta.
   Tsayi tsaye tana zare ido mamee ko dai muje tare dake.......... Bani hawa sama yanzu don kaniyarki. Kije ki karbo idan kuma kin yafene to.
    Tayi sukutii......kafin dabara ta fado mata, ta shige can kuryar dakin mamee ta dauko wayar ta don koda yana kara kulleta ta kirata, tasanya cikin zani bisa ciki taja riga, ta bude wata durowa inda take ajiye kayan gyaran kumba ta Ciro reza ta damtse a hannu, ta fito mamee na zolayar ta *yau uwani baki har ummarun kunne ta lissafi ta kare za'a sha kudi*
   Duk sukayi dariya ta haye saman, baya ko ina ta duba, gabanta ya kara faduwa, kilibabbe yana daki kwance kamar mace duk ya shirya kayan mata cikin daki shi ga mai kudi ta yatsina fuska da ta6e baki sannan ta banka kofar, ya zabura zaune. Yana ganin ta ya daka mata tsawa, *Are you mad*? ke baki iya sallama ba kuma bazakiyi knocking ba a baki izini zaki fado man daki haka gatsal idan kika tarar dani cikin wani hali fa?
  Wane hali bayan wannan dana sanka dashi na masifa? Daga bude kofa ka hayayyako mani da bala'i kamar ka haifeni....... *are you serious?* ya fada tare da dirkowa . koma kiyi sallama. Ta rike kugu bazan koma ba yau dai kam sai kuma a tari wani jikon ya tunkaro ta a hasale ta fara kwana, suka fara zagayen dakin yana son tsafko ta taki tsayawa, kaban kudina in fita ni yau naga jaraba kai kullum kamar kana jirana?
   Jiranki nake don ubanki ya yunkoro zai kamata ta haye gado tayi tsaye. Ni kike takawa gado? Ya zaro ido naje na taka kaban hakki na mana in tafi ko zan tsaya ne ka gana man azaba? Yayi tsalle ya haye gadon ta dirko kasa hannunta ya kado wata robar mai da bai rufe dai dai ba a dressing mirror ya fara zuba.
   Rezar da ke hannunta ta yanketa Sam ta manta da ta dauko reza tayi saurin wurgi da ita jini ya fara zuba ya zaro ido muguwaaaa yau ma zuwa kikayi ki yanka ni?
   Ta balla mishi harara hannunta dafe, haka nan zaka kirani inzo ne ta kai duba ga hannun ta, Rannan ma mamata kayi..... Ya mameta ya dirko gabanta tare da damko ta amma sai sulbin mai ya kwasheshi dashi din da itan suka fadi rikichaaaaa tayi baya ya haye ruwan cikin ta.
  Na shiga uku ta fada da karfi. Jikinsa ya wani bada tsammmm... Tunda yake a rayuwarsa bai taba rike hannun mace ba, ko gaisawa ba yayi dasu a duk inda suka hadu kuma  ko wace kasa yaje, kallabin ta ya cire an mata sabuwar kalaba kana duk ta rufe mata fuska, ya kura mata ido *Me yasa yarinyar nan bata tsoro na ne?*
Tayi kichin kichin malam dalla daga ni kada ka karya ni.
  Ko motsi baiyi ba ya kura mata ido ta samu da kyar ta zaro hannun da ta danne. Tayi tayi ta tureshi ta kasa,
  Kai dai mugu ne wallahi ta fada da kyar, da azaba ta isheta sai ta wawuro kuncinsa da karfi ta cije, ya wuntsila a wahale yana fadin kai kai kai ni kika ciza?
  Ta dauki kallabinta zata kwasa a guje ya riko hannunta da karfi, ta fado bisa shi sai kawai ta rushe da kuka. Ya kura mata ido kawai yana kallon ta.
   Kuka takeyi tsakanin ta da Allah, sai ya saki hannun a hankali ya tashi itama ta mike, ya kalleta zan baki kudin ki ne karki gudu ya fada a hankali kawai ya rasa menene yasa jikinsa yin sanyi.
    Yana juyawa ta kwasa da gudu zata bar dakin ya bita ya riko, ke me yasa kike da kafiya? Ya daka mata tsawa tare da sanya ma dakin key, ya saketa ya juya ina zakije hannunki da ciwo haka ko baki ga yanda kika bata man jiki da daki da jini ba?
  Hello gaya nan ya kulle daki zai dakeni......... Ya waigo da sauri yaganta tsaye tana waya, sai kawai ya juya yaci gaba da abinda yakeyi, first aid box ya dauko...... Zo in miki dressing.
Bana so,
Yayi mata wani kallo cike da takaici don zan taimaka miki?
Bana so da in baka hannun nan ka taimakeni na gwammace in tsaya haka jinin ya tsiyaye. Zai yi magana yaji bugun kofa *madaki* bude kada ranka ya baci........ Ya kalleta rai a bace kawai ya wuce. Da sauri ta shigo me ta maka zaka dake ta?
    Karya takeyi gashi nan yankewa tayi zan taimaka mata take man rashin kunya zata fita na rufe kofar shine fa naji tana kiranki a waya,
  Ya akayi ta yanke daga karbar kudi? Ta daga mishi tsawa, zaiyi magana kana hauka ne?
  Menene ke damunka wai?
Ganin ranta yayi mugun baci yasa yayi shiru kawai ta ci gaba da fada sosai ya kura ma umaimah ido ko zatayi bayani amma tayi shiru,
  Mamee tambayar ta ina ta sami reza wallahi da abinta ta tazo, na rantse da Allah babu ruwana. Ya daga hannuwa sama yanda yara keyi.
   Uwani ina kika sami reza ya akayi kuma kika yanke?
Gabanta ya fadi. Anya zata fada wa mamee wurin guje guje ne? To me yasa su hakan rashin sallamar da tayi kuma ta bishi da rashin kunya....... Wallahi babu ruwana ai kinji tayi shiru, kai wannan wauta taki uwani Allah ya rabaki da ita. Ka hanzarta daure mata hannun na baro baki ciki.
    Ta juya har ta kai bakin kofa ta tsaya ganin ta biyota, ta ruko kunnenta ina zaki bini haka je ya daure miki hannun ki sauko ina jiranki zaki raka ni unguwa. Taja kofar.
   Ta isa gun dan akwatin ta fiddo bandeji ya rike mata hannu. Sakarni zan yi da kaina. Ya kura mata ido wallahi mamaki take bashi ba za a saki ba ya damke hannun tayi tayi ta kasa kwacewa, ya da dauko auduga da spirit ya goge jinin da hannu daya hannu daya rike da ita,
  Mtseww na tsani shisshigi wallahi, na ce bani so bani so kamar dole, ya kalleta har zaiyi magana sai kawai ta bashi dariya . yayi Dan murmushi kadan yaci gaba, ya daure wurin.
     To ka sakeni tunda ka kare malam........idan  kika kara magana zan dauko rezar can da kika yar in farfade hannun kin San kuwa zan iya...... Kut ta hadiye wani miyau a tsorace. Ya kusa sakin dariya ga tsinannen tsoro ga jan fada ya fada a zuci.
    Yasa hannun aljihu ya dauko daurin kudi na dari biyar biyar ya wurga mata a jiki sannan ya saki hannun *kilgi dubu talatin kudin aikin ki*
     Ta yi saurin kallon sa
Koni yaron ki ne da zan kilga in baki?.
  Ta kalli kudin ai duk kwara biyu dubu daya kenan kada ya fahimci bata iya lissafi ba ya kara rainata sai kawai ta kwance, ya kura mata ido ta daddage tsakanin ta da Allah tana hada biyu biyu tana cewa *daya, biyu, uku, hudu....* ke yi a zuci kin cika mun kunne.
  Ta balla mishi harara Da Allah ni ka rudani. Ta kara lalowa sai kawai ya bushe da dariya. Ta kara hararar sa taci gaba sai da ta kai sha takwas ya ce malama kina batan lokaci kilga kamar kina lissafin gero...... Innalillahi ta rafka salati ta watsa mishi kudin ungo kilga tunda bazaka iya yin shiru in kilga ba.
   Ya daure fuska ya watsa mata kudin itama wallahi sai kin kilgi kudin ki yau ko ki rasa. Mtsew ta buga tsaki.
  Mamee ta gaji da jira ta kirata a waya ya fige wayar yasa hands free uwani ko in tafi?
  Tafi mamee ta na gyaran daki ne. Zatayi magana ya to she mata baki,
  Saboda rashin imani zaka sanya ta aiki ga yankewa, ya kalli umaimar ita ce ta ce zatayi..... Sai ka biye mata...... Hello hello mamee ba 'aji ya latse wayar.
  Yaudaraaaaa to wallahi sai na fada mata karya....... Ya buge bakin idan kika zageni sai kin wahala kilgi kudin ki kiban wuri.
  Ta zumburo baki mugu. Ta fada ciki ciki,
Me kika ce?
Ban sani ba ta fada tare da fara kilga .
Kallonta yakeyi tsakani da Allah.
  Tana da kyau yarinya ce karama. Ya danyi jimm may be tayi 14-15. She's preety and  crazy. Yarinya karama amma ta raina shi. Wai me yasa bata tsorona?
Kawai sai yaji yana son Sanin amsar dalilin da yasa ba ta tsoron sa...........
Qala kus kaci kanka ta tofa mishi miyau. Yayi firgigi ke kina hauka ne?
Ni ce kai, tun dazun ina cewa na gama ka kuran ido. Ta watsa mishi ragowar dubu ashirin dinsa, ga ragowarka ta damtse nata zata mike. Ya janyo ta ina zaki?
Zaki fidda mun dubu goma wacce zaki ringa biyana kayana da kika 6ata a baya ko zan dauki asara ne sabbin shaddoji na ko wane kin wulakantar?
Zaki fidda dubu uku kudin mai na dana kaiki gida ranar da kikayi dare, zaki fidda dubu biyar Wanda shima zan ringa cirewa yankan da kikayi mun nayi asarar jini na, sai dubu biyu kudin energy na dana yi waste yau kika sanya ni gudu a dakin nan. Sannan Zan fidda dubu biyar bisa ga alfarmar baki San dokar ba daga yau zata fara, duk rashin kunya da maganganun da zakiyi man nan gaba zan fitar da kudin su sai ki ware dubu biyar kiban sauran...................

Maman Abdallah


No comments:
Write Comment