Wednesday, January 30, 2019
Yan Nigeria- Hattara Martaba da darajar Buhari da kuke gani dodo-rido ce ___Obasanjo
Yan Nigeria- Hattara Martaba da darajar Buhari da kuke gani dodo-rido ce ___Obasanjo
Olusegun Obasanjo ya bada tabbacin cewa Alhaji Atiku Abubakar, shi ne zai lashe zaben shugaban kasa mai zuwa domin ya cire kasar daga cikinkuncin da Take ciki Obasanjo ya ce martaba da darajar da jama'a ke kallo a jikin shugaban kasa
Muhammadu Buhari dodo-rido ce Ya ce ya yafewa Atiku Abubakar akan dukkanin wasu laifuka da ya yi masa, yana mai cewa ya soke duk wata yarjejeniya ko taimakekeniya da ya kulla da Buhari a baya Tsohon shugaban kasa Olusegun
Obasanjo ya bada tabbacin cewa dan Takarar shugaban kasa karkashin Jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, shi ne zai lashe zaben shugaban kasa na Ranar 16 ga watan Fabreru, saboda shine mutumin da ya dace ya cire kasar Daga cikin halin kuncin da take ciki.
Da ya ke jawabi a ranar Laraba a wani Taron lakca da aka shirya kan harkokin kasuwanci na Island Clube 2019 da ya gudana a birnin Legas, Obasanjo ya ce martaba da darajar da jama'a ke kallo a Jikin shugaban kasa Muhammadu
Buhari dodo-rido ce, yana mai cewa dukkanin matakan da shugaban kasar ke dauka na tabbatar da rashin dattakonsa. Obasanjo ya ce ya yafewa Atiku Abubakar akan dukkanin wasu laifuka da ya yi masa, yana mai cewa ya soke duk wata yarjejeniya ko taimakekeniya da ya kulla da Buhari a baya
Kalli wasu kaya tattun hotunan Maryam Yahaya
Jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan hotunan nata da ta haskaka, ta sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri
Dada mujallarhausa.com.ng
Tuesday, January 29, 2019
Macen Farko Mai Digirin Digirgir A Fannin Shari'ar Musulunci --AMINA DIYALLO
Mace Ta Farko 'Yar Kasar Guinea Da Ta Samu Digirin Digigir A Fannin Shari'ar Musulunci A Fadin Kasar Guinea Baki Daya MADALLAH DAGA WWW.MUJALLARHAUSA.COM.NG
Download [Video] Dadin Kowa Sabon Salo Episode 88
Domin kallon cigaban shirin dadin kowa na satin | da ya wuce ku kasance damu. ACIKIN WANNAN | SATIN:- Kawai ku biyomu domin ganin yadda | zata kasance a cikin shirin. Asha kallo lafiya | |
yar kwalisa kalli wasu zafafan hounan BILKISU SHEMA
F
Fitacciyar Jarumar Kannywood wadda Kowa yafi saninta Da Bilkisu Shema Tace kullum mu kasance Cikin Godiyar Allah Alhamdulillah Ala Kulli Haal DAGA WWW.MUJALLARHAUSA.COM.NG
Duniyar Kwallon Kafa Yadda Hada-Hadar Zaratan Kwallon Kafa Ta Duniya Ke Gudana
Ajiya Messi yakarbi kyautar MVP wadda yalashe A season din 2017/18
Antabbatar da ranar 26-march za afafata wasan Sada zumunci tsakanin Argentina da Morocco Afilin wasa na Moulay Abdellah dake burnin Rabat
Dan wasan Real James Rodriguez Wanda yake Amatsayin aro a Kungiyar Bayern munchen ya Tuntubi Kungiyar ta Bayern munchen din cewa shifa ayanzu yana so yabar Kungiyar Kuma ana danganta dan wasan DA komawa
gasar premiere league Arsenal ce kangaba wajen Zawarcin fitaccen dan wasan kasar Colombia
As Monaco tafara nazarin daukar dan wasan Bayan inter Milan Miranda dan kasar Brazil Kungiyar kwallon kafata Duhail Sport Club ta kammala daukar dan wasan bayan Juventus Mehdi Benatia
Jaridar (ESPN) Ta bayyana cewa dan wasan
baya na Leicester Ben Chilwell shine dan wasan da Manchester city ayanzu ta kwallafa rai akan Atletico Madrid tabayyana dan wasan bayan RB Leipzig Dayot Upamecano Amatsayin Wanda zai maye mata Gurbin kaftin dinta wato Diego Godin
Manchester united da Chelsea sunbi sahun Real Madrid wajen zawarcin fitaccen dan wasan Tsakiyar Tottenham Christian Eriksen
Bayan Juventus ta sallamar da Mehdi Benatia Ayanzu ta koma kan dan wasa Matthijs De Ligt Na Ajax domin daukar matashin dan wasan bayan yamaye mata gurbin sa
Kaftin din Manchester united Anthony Valencia Ka'iya barin Kungiyar acewar jaridar (Sun Sport) Newcastle da Fulham ne kangaba wajen zawarcin dan wasan
Ac Milan tashirya dawoda tsohon dan wasanta Gerrard Deulofeu daga Watford akan kudi €24
Akaro na biyu Chelsea takara yiwa Bayern munchen gargadi karta kara tuntubar dan Wasanta Cullum Hudson-Odoi
Bayern munchen dai tayiwa matashin dan wasan tayin £85.000k sabanin yadda Chelsea take
biyansa £75.000k Sannan kuma Bayern munchen din taiwa dan
wasan tayin Riga me lamba 10 idan Robben ya bar Kungiyar akarshen season din nan
West Ham takusa daukar dan wasan tsakiyar Sheffield United John Fleck akan kudi €4M
Atletico Madrid takammala daukar Alvaro Morata daga Chelsea Amatsayin aro natsahon watanni 18 akan kudi £9M tareda yarjejeniyar daukar sa Akan kudi £48.5M
Fc Schelke 04 ta amince zata biya Manchester City £11.3M domin daukar matashin dan wasan Manchester city mesuna Rabbi matondo meshekaru 18
Manchester united Barcelona Ac Milan Leicester City neke rububin daukar dan wasan tsakiyar Monaco Youri Tielemans dankasar Belgium
Tottenham da Liverpool neke zawarcin dan wasan Paris St-Germain Adrian Rabiot Wanda ake dan gantashi da Barcelona
Paris St-Germain tayiwa Bayern munchen tayin €20M akan dan wasan tsakiyar ta Renato Sanchez amma Bayern munchen din tayi watsi da tayin Bayan Rashin jituwa tsakanin Özil da Unai Emery Inter Milan ta shirya daukar Özil din awannan wato
Espanyol takammala daukar tauraron dan wasan Chinese super league na Kungiyar Shanghai SIPG mesuna Wu Lei Wu lei dai shine top score a league din Chinese
kuma Kungiyar Espanyol ta tatabbatar da daukar Dan wasan meshekara 27 ya rantaba kwantaragin
shekara Chelsea na nazarin tura tayin £40M akan dan wasan bayan Bournemouth Nathan Ake Real Betis tafara tuntubar Paris St-Germain akan Dan wasanta Jese Rodriguez tsohon dan wasan Real Madrid Manchester city tashirya kashe £35M akan dan wasan Schelke Sebastian Rudy SAKAMAKON WASA TAKANIN ABBA DIKKO BOYS MUSAWA - FC KIRA
KUNGIYAR KWALLO KAFATA JUVENTUS SUN
DAIKI SABON MAI HORASWA MESUNA (AUWALU BAHAGO) BAYAN SALLAMAR R.OZIL DAKUGIYARTAI
Sako daga bangis mai Madrid karamar hukumar danbatta dake jahar kano
AKWAI WASA RANAR LARABA TSAKANIN BOCA JUNIOR GARGAI ACADEMY VS KUKI
UNITED
Daga MUJALLAR HAUSA
AUREN FARI PAGE 35
AUREN FARI 35
..... Mamaki ya kamata ganin da gaske ya fara barci, ta zuba mishi ido yanda yake barcin kamar wani karamin yaro.
Matashi Dan gayu mai kyau. Tayi murmushi Allah ya bani gaskiya madaki Nada kyau yana da kuruciya ga kudi, yaro matashi Allah ya bashi arziki na ban mamaki ga mu'ujizar mutane da Allah ya bashi.
Ta bi jikinsa da kallo, fatar sa lumuy lumuy Hutu ne kadai da jin dadi, bata lura ya farka ba sai kawai taji kiss a bakin ta.
Tayi saurin yin baya, ya yunkura *Almura* ashe kina nan zaki cinyeni da kallo.. Gaskiya dole in warware miki kunyar nan ta na wahalar dake,
Ya dauko sandwich da coffee ya ce bisimillah cikan ciki.
Tayi murmushi , ya kalleta fadi kar ta kashe ki, ta dunguna mishi katon sandwich a baki ni dai amshi.
Ya ci gaba da mata dariya.
Suna isa taga yanda ake ta kyarma da madaki, abin ya daure mata kai wai har Dubai an San shi? ( umaimah kenan ), wani makeke gida suka isa, turawa,indiyawa da larabawa ne ma'aikatan gidan kowa yasan sunan sa, gidan har yaso yafi na Nigeria tsaruwa saboda shi bai kai girman wancen ba.
Ya kalleta hajiya da kafar dama zaki sha kinzo gidan ki na Dubai.
Gabanta ya fadi haka su goggo suka ce da ita lokacin da zata shiga gidan sa.
Ya danyi murmushi sukayi ciki.
Ta kalleshi ya na kokarin hawa bene, kai wannan mutum da son bene yake kamat tsuntsu.
Ba abinda babu gidan.
Bani iya misaltashi.
Ya fara bubbude drower abin mamaki ta ga kaya tsangare ciki.
Tayi shiru ta na kallan ikon Allah.
Ya fara watso ruwa sannan ya ce ta shiga tayo.
Sai wani basarwa yakeyi yana dan shan kamshi alamar za ayi wulakanci da rai.
Ya shirya cikin kananan kaya yana ta faman jiranta,
Ita kuwa har ta bushe data leko ta hangoshi sai ta koma ciki.
Ya kalli agogo au yarinyar fa kasa fitowa tayi.....mtsew yaja tsoki, ya dauki hijab ya Dan bude kewayen kadan ungo ki saka idan fitowar ne bazaki iyaba....... Ta miko hannu tana karba ya yi saurin bude kofar ya fizgota saura kadan tawul din ya balle ta daddafe....... Ka rufa man asiri kayi hakuri don girman...... Ke bari hada ni da abinda yafi karfi na wallahi sai na fara rage miki kunyar nan ya janyo ta..... Na daina billahil azim bazan karaba amma inaa sai da ya kaita bisa gado yana fadin na ce ki saki jiki dani kin kasa bari kawai a kashe boss madam........ Na daina wayyo na shiga uku ta kankame jikinta zata fara kuka, ya saketa, jeki shirya fita zamuyi....... Ta yunkura da sauri duk ta rikice, ya harareta gulmammiya.
Ta shige bayan wodrop ta saka bra da pant tana kokarin sa dogon skirt din kayan da ya fiddo mata kawai taga mutum.....ta hade da bango *Madaki* wai meye haka don Allah na tuba....... Ya tallabo kugunta *Nawa gareki*......zo in koya miki sauri....... Duk iya kokarin da nakeyi? Tayi saurin janyo skirt din ta karasa sanya shi ya juyo ta karfi ke me yasa kike haka?
To meye din naga wannan?...... Kawai yakai hannu kirjin ta, .... Ta rikice gashi ya riketa gamm ... Ka dubi girman Allah kayi hakuri sai ta fara kyarma.
Tabb wallahi sai na taba....ta zaro ido ka taba me? Wayyo na shiga uku kawai taji yasa hannu ya ballo bra din ta kwalalo ido ni dai bani so wayyo mamee...... Ya kyalkyace da dariya nasan zaki kirata shi yasa na gudo dake nan.......
Ya zareta duka..... Ta fada jikinsa ta makalkaleta ka rufa man asiri madaki na tuba....... Ya yi dariya *Good* ko kefa?
Ya fara shafan bayan ta zuwa kugu yana mata rada a kunne idan ba kyajin yunwa muyi hakuri da abincin nan zuwa dare ........ Yunwa nakeji nidai mu tafi ta fada tana yan kwallahi.
Allah? Ya bukata
Wallahi yunwa nakeji don Allah ka kyaleni. Ya yi murmushi ya janye hannun sa to nima sakeni.
Tayi shiru, kinji?
Ko in ci gaba? To kaban bra ta in mayar .
Ya danyi dariya kin ganta nan a kasa sakeni in miko miki.
Ni dai tafi zan dauka. Ya kyalkyace da dariya to ki sakeni mana..... Ta Dan ja baya shi kuma ya juya kamar zai tafi. Tayi saurin dukawa ta dauko tashin da zatayi taji duka hannuwansa bisa su............ Ta kurma ihu Qalu innalillahi...... Na shiga uku.
Ya maidota ta jikinsa ta baya ai na ce wallahi sai na taba da banyi rantsuwa bane.
Yadan murza...... Kin San tun lokacin da nake hadiye masu miyau ........ Duk illahirin jikinta ya mace murus, ta rike hannuwansa shi kuma ya kara luma su.
Kafafunta suka kasa daukarta lakkar jikinta tayi sanyi, ba abinda tsikar jikinta keyi sai ta shi.
Da kyar ta bude baki don Allah ka yi hakuri na Tu......... Ya juyo ta da karfi kafin tayi wani motsi ya hada bakinsa da nata.
Ta karasa rikicewa ta tafi luuuuu zata fadi ya tallabo kugunta kawai ya sureta zuwa gado.
Hankalinta ya tashi ta fara kuka *Madaki* ka yi hakuri kuka takeyi sosai musamman da taji bakinsa akan nono........
Ta fasa kara ta ringa ruzgar kuka tana magiya hankali tashe,
Ya dade kafin ya dago idanunsa sunyi jawur tayi saurin kawar da fuska don bata iya jure kallonsa haka.......wai meye kike tsoro?
Don girman Allah kibarni ki kyaleni.......... Ta fashe da kuka don Allah kayi hakuri ....... Inyi hakuri in zuba miki ido ina kallo?
Ke baki son ko ido mu hada ya kara kai hannunsa kiyi hakuri in rabaki da kunyar nan a wuce wurin...... Na bari bani karawa.... Ya kalleta kamar zai yi magana ya buga tsoki ta shi ki shirya mu tafi, ya fice falo.
Ta Dan gyara fuskarta yana tsaye har lokacin idanun sa basu washe ba, ta fito simi simi....... Ya wuce.
Wani hadadden wurin cin abinci sukaje daganin inda suke, Musamman aka shirya masu, duk ya hade rai, yana satar kallonta, ita kuwa ta kasa dagowa ta kalli ko gefen ta, ya kara buga tsoki, kunya, kunya dai. Wallahi fiddata zanyi.
Suka Dan zagaya suna kallon wurare yana rike da hannunta sai sunsunkewa kawai takeyi. Ya kira mamee yace sun sauka lafiya ya karbi wayarta ya kashe.
Sai bayan isha'i suka koma gida, gabanta sai faduwa yakeyi ganin yanda yake ta shan mur,
Ya gama shirin sa tsaf ya kwanta tana ta yan kame kame, zuwa can taji alamar barci ya daukeshi ta sanyo wasu riga da wando na barci ta lallaba wai kada yaji ta kwanta bayansa, duk yana jinta.
Tana gama tofa addu'a ya juyo sai kawai taji mutum ya janyo ta , kirjinta ya buga da karfi.
Ya fara shafata a hankali, ta runtse ido da karfi, duk abinda yakeyi tana jinsa tayi shiru yana jin yanda kirjinta ke halbawa, ya ce cikin zuciya tsoron nan na iya haifar miki da matsala.
Bata motsa ba sai da taji yana kokarin raba ta da kayanta, ta ksnkame jikinta zata fara magiya yasa bakinsa akunnen ta, kiyi shiru kawai kamar yanda kika fara yi da farko komai zai tafi a hankali......... Ta fashe da kuka kiyi hakuri umaimah wannan tsoron naki yayi yawa bari kawai a wuce wurin, ya yi wurgi da rigar ta fara kuka yana bata hakuri........duk abinda yakeyi bai fasa magana a hankali ba, ina tunanin wata ce ta firgita ki da yawa gara ki san *Duk karya ce*
Tun yana magana shima sai wutar sa ta dauke........
Kuka takeyi har muryarta tashake.
A hankali tunanin sa ya dawo nan da nan kuma ya fara lallashi, ta ingijeshi ya danyi murmushi *Kut* nayi laifi ya janyo ta ya hakuri bani karawa.....ta kara fashewa da kuka,
Da kyar ya samu tayi shiru daya yunkura zai ta shi sai tayi tunanin dawo mata zaiyi sai kawai ta firgita dole ya hakura har barci ya dauketa mai nauyi wajen karfe uku da rabi.
Yayi shiruuuuuu zuciyarsa tayi fes!
Tausayinta ya baibayeshi. Ya lumshe ido yana tunanin yanda yakeji a zuciyar, ya yayi murmushi gobe akwai daru gidan nan, rigimar umaimah gobe Allah kadai zai kwaceni, a haka shima barawon ya sace shi.
Kukanta ya tayar dashi duk jikinta yayi dayi, ta kasa tashi, gaban sa ya fadi kada fa maganar abokan sa ko ya mata rauni.
Ya zo zai kamata *Umaimah* ta dan fizge, bata so.
Yayi murmushi ya hakuri tare da yaye bargon subhannallahi haka rana ta yi?
Ya wuce kewaye, sannan ya fito zo muje in taimaka miki....... Bana so ta fada cikin kuka, yayi yar dariya kawai ya sungumeta ta fara zille zille idan baki tsaya ba wallahi zan kara ....... Ta fashe da kuka.
Ya gaggasa mata jiki yana zolayar ta, jiki ne bana wahala ba ba a iya daukar bokitin ruwa amma an dauki madaki....... Ta ci gaba da kwallah shi kuma yana dariya.
Ya fi mintuna ashirin yana gargasa ta sannan ya kara sa mata wasu ruwan ya kalleta *Kin dai iya wankan janaba ko?*..... Ta dauko katon sabulu ta kwala mishi..... Yayi hanyar fita lallai karfi ya samu bari inyi ta kaina. Ya fice yana dariya.
Dadin ruwan zafin yasa taki fitowa sai da ta shafe kusan awa guda sannan.
Tana fitowa bata ganshi ba ya gama gyara dakin ya canza bed sheet amma bai iya shinfidawa ba ya dai dan badada shi kawai. Ta tabe baki ta sanya wata blue gown mai karamin hannu ta Dan shafa mai da turare kawai sannan ta kabbara sallah.
Raka'ar karshe ya shigo yana ta uban kamshi cikin farar t-shirt mai karamin hannu da blue jeans. Yana dauke da Dan tray.
Ya zauna tare da zabga uban tagumi yana kallonta, ji yakeyi kamar ya hadiye ta, , duk fuskar ta kode saboda kuka amma sai ta kara mishi wani kyau da annuri.
Ko kallonsa batayi ba ta ta shi tana ta fushi ta haye gado... Yayi murmushi yasan dole ayi haka.
Ya karasa shima ya hau gadon yana fadin Allah yayi miki Albarka kamar kin San nima ban gaji ba ya janyo bargo zai rufe su ta sauka da sauri ta kydundune jiki tana kuka.
Ya kyalkyace da dariya *Ke wasa nakeyi* ya zagayo inda take, ya hakuri nima na San nayi laifi umaimah bazan kara ba kiyi hakuri kinji?
Ka tafi kaban wuri ...... Yayi murmushi a a ina nan fa. Sai dai kiyi man duk hukuncin da zakiyi man amma fa ba inda zanje.
Ga kunya ga takaici ta rasa ya zatayi da shi.
Ya fahimci tabarmar kunya takeson nadewa da hauka sai ya janyo ta zo muyi kalaci kinji 'yar amaryata ban karawa jiya ma kuskurene ....... Zo in baki da kaina yana faman lallashi.
Ba wani cin da tayi sosai suka koma barci, basu tashi ba sai uku da rabi. Shine ma ya rigata tashi.
Tare sukayi jam'i na la'asar sannan ya kamo hannunta suka fito tana ta fushi.
Shi kuwa sai wani nishadi yakeyi yana satar kallonta.
Abinci kala kala suka tarar an kawo na lunch nan ne yasha mur ya sanya taci sosai sannan ya sungumeta sukayi bayan gidan wurin ruwa.
Daga ranar sabuwar rayuwa ta bude ma umaimah da madaki. Bai kara taba ta ba har kusan sati sai dai an fara shakuwa har ana guje guje da yar goyo. Duk wani wasan yan yara umaimah ta kawo mishi hada yar boyo.
Umaimah an gama shan kwana tunda hawan jikin madakin ya zama ba komai ba. Sun gama mallaka junan su zuciyoyin su.
Da daddare tana kwance bisa cikin sa, ya fara shafar ta yana canza salon firar ba kamar kullum ba nan da nan ta fara rikice mashi cikin matsanancin tsoro.
Ya tallabo fuskar ta *yau dadi zakiji* trust me mana. Ta fara kuka ya ce wallahi yau babu zafi kwantar da hankalinki.......... Hankalinta bai kwanta ba sai da ta tabbatar azabar bai kai farko ba.
Amma dai an dan wahala.
Daga nan ya kyaleta kusan kwana hudu sannan haka ya ringa stepping back na kwanakin yana ragewa kafin a koma kullum.
Ma'aikatan gidan Kansu sai da umaimah da madaki suka ringa birgesu.
Soyayya akeyi ruwanta watan su biyu Dubai kafin su ka tafi *France* nan ma aka balle bushashar sati biyu suka wuce *Pari* satin su daya umaimah tace kasar batayi mata ba saboda mugun sanyi suka wuce gidan sa da ke London anan labari ya canza umaimah aka fara amaye amaye.
Duk wani turare da madaki zai saka bata sonsa.
Ta ce bata son warin gidan. Ya ce to ko mu tafi hotel, nida gidana ya gagareni?
Wani abokin sa ne yake fada mishi juna biyu gareta, ya kuwa dauketa sai asibiti likita na tabbatar mishi da gaskiya ya kwala wa mamee kira. Yana shaida mata itama ta hau murna.
Sai Sabon kulawa ga hajiya umaimah.
Ya ce to ke kina ma iya zuwa hajji kuwa?
Sai da suka wuce umara sannan suka koma gida.
Umaimah ta zama kamar gwal.
Amma in da tayi Kyan kai hakan bai taba sawa ta fasa yi wa madaki duk abinda yake so ba wani lokacin ma shine ke tausaya mata.
Yaya Abba ya dawo dumur dumur madaki ya bashi manager gidan daya daga cikin gidajen man shi.
Hajiya kuwa ko 'yayan cikin ta bata jin dadin su yanda takejin dadin umaimah, umaimah ta bayar da mamaki yanda duk ba'a tunani.
Allah ya sauki umaimah lafiya ya bada zuri'a dayyiba. Ayi hakuri labarin ya tsaya daga nan saboda wasu dalilai.Allah ya kara hada mu da masoyan mu.
Kadan mai albarka ........... Ina kara bada hakuri
*TAMMAT BI HAMDU LILLAH*
SAI KUN KARA JINA GA WANI SABON LABARIN IN SHAA ALLAH.
Na gode nagode da kaunar Ku gareni.
*SUNANA ZAINAB DAHIRU WOWO DUTSINMA
Maman Al'amyn Amynatu da Abdallah.
Ina bada shawara don Allah duk Wanda zaka so to ka soshi don Allah.
*THE END*
Jarumar Bollywood ta kwatanta Iwobi da gwaggon biri
Fitacciyar Jarumar fina-finan Bollywood na India, Esha Gupta na shan caccaka daga magoya bayan Kungiyar Kwallon Kafa ta Arsenal sakamakon kalaman nuna wariyar Launin fata da ta furta kan dan wasan Najeriya da ke taka leda a Arsenal, Alex Iwobi Da ta bayyana shi a matsayin gwaggon biri. Gupta wadda masoyiyar Arsenal ce ta hakika, ta wallafa hoton tattaunawar da ta yi da wani a Shafinta na Instagram, in da ta bayyana Iwobi a matsayin gwaggon biri. Hakan kuma na zuwa ne sakamakon kashin da Arsenal ta sha a hannun Manchester United a gasar FA a ranar Juma’ar da ta gabata. Kazalika Jarumar wadda ke yawan ziyartar Birnin Londo domin kallon wasan Arsenal kai Tsaye, ta yi korafi kan rashin ajiye Iwobi a banci, Yayin da ta bayyana shi a matsayin Shirmammen dan wasa.
Sai dai tuni magoya bayan Arsenal har ma da mahukuntan kungiyar suka mayar ma ta da martani, in da suka nuna rashin amincewarsu da Furta ire-iren wadannan kamalai masu raba Kawunan jama’a. Tuni Gupta ta share hoton kalaman na Kaskanci bayan ta sha caccaka, yayin da ta Bayar da hakuri.
Sunday, January 27, 2019
AUREN FARI 34
AUREN FARI 34
......... Ta zumburo baki.
Ya kalleta da kyau bazakije ba ne ko kuwa Dubai din ke bakya so?. Ki fadi kasar da kike so umaimah you have that right.
Ni ba tafiyar ke bana so ba zolayar nan ta jirgi idan zai tashi nake tsoro wallahi hanjin cikina kamar zasu fito........ Har kwanciya yayi saboda dariya ta yi murmushi wallahi ka fiye mugunta kai kuwa.
Sai da yayi mai isar sa sannan ya ce ba irin wancen jirgi zamu hau ba, wannan na daban ne sha kurumin ki wifee.
Ta ce *Hmmm*
Ki matso muci ko na kamoki yanzu nayi miki dura,..... Ta matso da sauri saboda tasan duk abinda madaki ya ce zai yi to zai iya, suna ci yana janta da fira.
Wayar sa tayi kara, gaban sa yayi mummunan faduwa ganin sunan samira, ya dauka idan ta gane mace ce ya shiga uku, ya ki dauka shima matsala.
Ta dan saci kallon sa ganin waya nata ringing har tana niyyar katsewa, ya dan bata fuska ya daga yana kallon fuskar ta..... Hello Aunty har kun isa?
Samira ta dauke wayar daga kunnen ta tayi saurin kallon screen din tana zargin ko ba *Madaki* ta kira ba,
Yaji shiru, yaci gaba da cewa amin na gode Aunty Allah yabar zumunci ya latse wayar. Dai dai ta mayar da ita kunne itama.
Toooo faa! Ta fada tana zaro ido, wai ya akayi? Ta mike tsaye, lallai abinsa azimun ne wannan yarinyar tsoron ta yakeyi kamar rai da ajali. Abinda yafi na shafa ma kaina lafiya da *Matashin yaro* idan ya nemeni welcome idan bai nemeni ba kuma umma ta gaida asshhaa ina dalili.
Ya kalleta tana ta tura dankalin da kyar sai kawai ya sha mur, ke juyo ki fuskance ni.
Gabanta ya dan fadi ta juyo tana kallon sa kanta a kasa,
Na lura sai na biyo miki ta bayan gida sannan zamu shirya ko? Kin dai san yanda mukayi jiya da ke ko?
Ta daga kai *Eh*
To ina nan akan baka na babu abinda zan miki, sai dai dole ki sauarara kin kindaya miki sharudda saboda yanda na ke kokarin tsara zaman namu bazai taba tafiya dai dai ba.
Kin dai San yanzu ke matata ce ko? Ta daga kai *Eh*
Good to bazan jure wannan makurewar ba wallahi kinji na rantse. Na farko anan zan kwana yau nida ke saman gadon can...... Ta zaro ido wallahi na tuba zan yi yanda kake so.......... Jira da Allah malama, kawo man ke akayi in kalla? Na ce ba abinda zan miki kin kuma San abinda nake nufi da hakan sai dai bazan iya hakurin wannan makurewar ba, idan kin hana in taba ki baya yanzu dai baki da iko.
Magana ta biyu zaki ringa bani abinci daga yanzu a baki har in koshi, sannan ba maganar zama nesa dani ko kusa dani kin ga nan? Ya bugi cinyar sa nan ne mazaunin ki Allah. ......zatayi magana ya daga mata hannu *umarni nake baki* ba wai ina neman shawarar ki ba.
Tayi narai narai, sai magana ta uku idan ina barci zaki tasheni dole kema ki kwanta kusa dani kina shafani a hankali kina kiran sunana har na farka ko kin gane?
Ta daga kai *Eh*
Good taso ki dawo nan toh ya janyo hannunta , tayi sukutii ....ya kalleta wallahi ki ware kawai don baki ga komai ba game da dokokina ba.
Ta fara debo dankalin zata bashi ya ce hajiya ajiye chokalin da hannu ake ba mai gida abinci........
Na bani kawai.....ta fada azuci.
Da ta bashi ta kara debowa sai ya rike hannun ranki ya dade ba a sauri *Slowly*........ Ya kashe mata ido.
Ta yi dai sukuy, yana koshi ya gyara zama sannan ya rungumeta kamar jaririya yana bata, ( yau na ga ta kaina ni umaimah ) ta fada kamar ta nutse.
Karfe biyu ya shirya ya ce mata zai je cikin gari.
Tana fitowa ta kira su bilky ta kwashe bokitan gara duka ta ce a mayar sashen mamee hada manshanu.
Tana ciki tana harhada kudin gudunmuwa bata san wainar da suke toyawa ba, umaimar ta shiga . Tana ganinta ta washe fuska 'yar halak yanzu nake tunanin ki a raina.
ta zauna tana tayata harhadawar mamah kuma ba sai ki kirani ba?
Tayi dariya kawai, ashe gobe zaki kara katari da nutumen? Duk sukayi dariya sannan ta turo baki wallahi bana kaunar abinda ka kara hawa dani jirgi mamah ki ce a bar tafiyar don Allah.
Uwani ina ni ina hana tafiyar da an gama komai gobe goben nan?, to ki shirya mu tafi tare don Allah mamah......... Ke bani son iyashege, haka kawai sai in biku?
Ta langabe idanunta suka kawo ruwa wallahi zanfi jin dadi idan muka tafi da ke don ni tafiyar gaba daya bana so........ Ta ajiye kudin hannun ta kafin ta kamo hannuwanta duka biyun.
Uwani ki kwantar da hankalinki ba abinda zai faru sai alkhairi, idan kuka tsaya garin nan tabbas ke kanki abin sai ya dameki saboda fitar nan da kika ga yayi office ya tafi, wallahi matukar madaki na garin nan bazai huta ba.
Kuma kema dama ce gareki da zaki San me mijinki keso meye baya so........ Bata san lokacin da bakinta ya kucce ta ce humm ba.
Bata bi ta kanta ba taci gaba da cewa, kuma kya gano gari kiyo kallo tunda naji yawo zakuyi kasashe don jirgi ai sabawa zakiyi wancen ma don karonki ne na farko.
Ta fara janta da yar firarraki har ta dan saki.
Suna zaune falo ya shigo tara da rabi har ta gota, uwani da mamee ya fada yana murmushi, ina so inji yanda firar ku take kasancewa yanzu su uwani an zama matar madaki,
To rasa kunya beran tanka,zaka fara ko?
Uwani tashi ki tafi daki kada ya hanaki sakewa kinji, tayi zumbur ta wuce simi simi ya bita da kallo iyye yarinya sama tayi yau bad akin mamee ba…….itama mikewa tayi ta wuce ciki, yana waigowa yaga har ta kusa shigewa y ace mamee ina zuwa? Ko waigowa batayi ba barci nake ji kasan akwai gajiya tayi ciki.
Ya danyi murmushi kai mamee karshe ce wallahi.
Tana ta kakkabe kakkabe tama rasa me zatayi hankalinta a tashe wai gado daya zata kwana da madaki. Ta yi kasa da murya ba abinda ke cikin aure sai fargaba, takura, zullumi da tsoro.
Wallahi kamar in gudu nakeji………….ki tafi ina?
Tayi firgigi ko kadan bata ji shigowar sa ba. Ta danyi kasa da kai, ya kamota zo nan meke tayar miki da hankali kike tunanin guduwa?
Ya bata rai umaimah dana san baki kaunata da ban aure ki ba…..Allah bah aka bane, to menene?
Tayi shiru, ya zauna bakin gado ita kuma ya dorata bisa cinyarsa, umaima wallahi aure da kike ganin sa babu abinda ke ciki sai jin dadi, farin ciki,walwala da nishadi. Shi yasa Allah SWA cikin suratul rum yake cewa : kuma na halitta maku matan aure sannan na sanya soyayya da nutsuwa a tsakanin ku lallai wannan ayar mutane ce masu yin tunani.
Saboda haka ki saki jikin ki wallahi zan jiyar da ke dadin da ba’a taba jiyar da wata mace shi ba, zan shagwabaki yanda ake shagwaba yaro daya tilo wanda iyayensa suka samu bayan sun dade suna rokon haihuwa kuma daga shi basu karaba, zan kula da ke yanda duk baki tsammani na jiyar da ke dadin da ba kowa ce zata sameshi ba.
Abinda duk kike tsoro sai ya faru yau, gobe , jibi ,next month,next year ke any time but zai zo miki lokacin da baki tsammani lokacin da baki tsorona, lokacin da kika saba dani, lokacin da kika san dadin madaki…….. kawai ki saki jiki dani wannan shine abinda nake bukata umaimah saboda ni mutum ne mai son kula, kuma ina sha’awar taba jikin ki wanda baki isa ki hana ni ba duk tsoron ki duk wata makurewa da zakiyi.
Tun kafin in fara gwada miki karfi kawai ki ware hajia, ya tallao fuskar ta. Ya harareta wallahi matukar baki rage wannan kunyar ba tabbas zan gaggawar wancakalar da ita a wuce wurin….
Kinji ko?
Ta daga kai tana murmushi.
Kilibabba irin ku kunfi jaraba sumimu kasau, ni yanzu gashi dai na karya record yau idan kinji wayoyin abokai dana amsa wani dan iska ma cewa yayi zai zo ya rakani in kaiki asibiti. Basu san cewar ni madaki ba haka nake ba lokacin da ake tunanin da zanyi abu sai na kiyi ko laifi akayi man lojkacin da ake tunanin zan dau mataki sai anyi shiru, wallahi umaimah sai kin zauna zaki fahimceni bani da fitina da kike ganina na mugun miskili ne ni kawai ke baaki gane bane saboda yanayin chakwakiyar mu ko kuwa? Duk suakayi dariya,
ta ce wai chakwakiya, eh mana ko kin manta yakin da muka gabza kika farden hannu? Ya kyalkyace da dariya kai naga bala’I ni ummaru.
Tayi murmushi, ya mike ya fita sai gashi da gyalen hajia wanda ta bata aro lpkacin da suakyi ma juna wankan miya a fatin asma’u, ta fara tafa hannu tana salati, daman yana hannunaka? Ya yi murmushi ke wannan gyalen ai kusan haukatani yayi lokacin da muna cikin fitinar idan na dauko shi zuciyata har hayaki takeyi don azaba. Da kuwa na kamu da son ki da kin gudu kin barni sai na zo na daukeshi ina bege. Ta kyalkyace da dariya ta ce wai bege.
Nan da nan ta sake kawai suka hau fira hada tafawa, sai kusan sha biyu ya watsa ruwa yayi yayi da kyar ta shiga kewaye ta janzo kayan barci wata guntuwar riga iya cinya fitowa ta gagara sai shine ya fiddota da tsiya tana hawa gado tayi saurin yayo bargo ta lullube , ya hawo yana taunar cingam…. Yarinyar nan wallahi da gangan akayi budurwar kauye ai ke sunan ya dace da.
Ya janyo ta zo kiga yanda ake barci da miji hancinsa da nata ya haduya matseta ganin zata zulle malama jira haba, ya kura mata ido kaii ya naga hancinci bai kai nawa tsawo ba lallai cewa zakiyi akwai ragi ga abinda na bayar…….. yayi dariya idan kunya kike ji rufe ido in miki kallon tsaf!! Ta rasa in da zata sanya kanta, ya kura ma dan bakinta ido, ALLAH sai nayi kissing…..ya ayyana azuci.
Ke bude kiga wani abu ….bude bude bude…….ya fada kamar ga ma abin nan ya taho gadan gadan… tayi saurin budewa ya fiddo cingam din bakinsa ungo kici…..tayi saurin runtse ido gashi ya riketa ta ce nag a ta kaina anya bawayau zai mun ba?......bata karasa tunani ba taji bakin sa cikin nata……wata kunnanniyar wuta ta dauke mata, ta rasa duniyar da take . yafi mintuna goma sai da yaji network na neman dauke mishi ya sa kawai ya zare a hankali. Ta tafi da kanta luuuuu ta soke cikin kirjinsa ya maida hannuwansa bayanta ya rufe su da bargo ………………mu kwan lafiya.
Na bakin madaki lallai umaimah anji network. Don sallar asubah ma sai da ya dawo masallaci sannan ya tada ta,
Ya tasa ta gaba ya dinga mata dariya wai taji network barci harda minshari. Ta yi ta hararar sa, dai taci gaba da lazimi. Da kansa ya hada masu kayayyakin da zasu tafi daasu cikin yar karamar jaka daya. Cikin ranta tace kilan jibi zamu dawo.
Mamee bata koma ciki ba sai da taga fitar su gate, umaimah nata matsen kwalla duk tunaninta airport sukayi sai kawai taga sun dau hanyar gidan su. Wani dadi ya kumeta, musanman da ta hango baban tsaye kofar alamar isowar su yake jira.
Kafin ta fito kofar gidan ya cika da jama’a ta dan raba tayi gidan hajiya da sauri, gudu gudu ta fito har ya shiga mota yana jiranta, yana hangota ya fito ya isa wurin ta ya fakaici mutane ya saka mata kudi a jaka y ace bakauya idan mutane sun taru haka don kai alheri ake masu , tayi sukuti daman taga ya yi rabo cikin gida su luba har da rawa da taga umaimah.
Ta dan juya ta hango auwalu mai manja ta yahuto shi da hannu ta damka mishi daurin kudi ta ce raba muku tayi mota da sauri, suna dagawa ya kalleta yana dariya ina cewa zakibi kowa ne ki bashi.
Tayi yar dariya tabbb! Da sun karya ni kuwa……au ashe kin sani ta harareshi kawai.
Suna zuwa jirgi na slow, ko zama basuyi ba ya cacumeta wa kike ma harara dazun, sukayi bisa doguwar kujera rikichaaaaa ya fara mata chakulkulo tun tana zullewa har ta fara kyalkyatar dariya tana zillewa…… ana haka yaji jirgin ya tashi har y agama saisaituwa sararin samaniya…. Ya dan saketa, tayi jimm tana gyara cucukuyar kayanta tana zullumin tashin jirgi sai kawai ta hango hazon gajimare, nan da nan ta fahimceshi.
Ya kwantar da ita jikin sa yana fadin dumaman jiki in dan runtsa please…………..Maman Abdallah.
Saturday, January 26, 2019
AUREN FARI NA 33
AUREN FARI NA 33
........ Duk ka tsorata 'yar mutane don ubanka.
Ya kyalkyace da dariya, yarinyar can wallahi bazaku gane ba gwala ni takeyi kamar kwallon kafa.
Karya kakeyi kai da kace babu macen da zaka bi, baka ba mace hakuri, baka......Alhaji anji.
Suka kwashe da dariya. *waya fada maka barno gabas take*
Umaimah nata, kuka mamee sai lallashi takeyi, jamila ta turo baki *Yaya dubi mutanen ki*.... Ta tabe baki sa ji dashi kilibabbu.
Kinga sarkar da ta sanya jiya? Murja ta fada tana tabe baki.
Jamila ta ce ki duba wuyanta kiga ta yau tafi ta jiya sau hudu.
Aikin banza waccen figaggar yarinyar cinye su zatayi har babu.
Ai kunji tayi shiru har yau taki cewa da mu komai saboda munafunci da shegen zurfin ciki. Yaya ta fada tana mazurai.
Ku jira Ku gani waccen maryam din data fifita fiye da mu zanci ma uwa munafukan banza..... Yo yaya bakiga kudi ma ita take ba ajiya ba?
( uwa daya uba daya gaskiya basu duba wa mamee ba. Allah ya raba mu da hassada )
Hassada ciwo ce wallahi, uwa daya uba daya akwai ta kawai ta wasu tafi ta wasu fitowa,
Mamee ta ringa raba atamfofi super, da barguna masu kyau na kasashen waje, ga wasu robobi, bokitai, glass cups, kai kaya barkatar, su yaya sai tabe baki sukeyi *Karyar banza*
( wai arziki kamar na madaki a kirashi da karya )
Akayi budar kai, kowa na ba umaimah kudi kamar yanda al'ada ta nuna su yaya na zaune turus!
Bayan an maida umaimah sama suka baje bisa carpet, yaya ce me korafi *Naga ana wucewa da tuwo mu banda mu?*
Hafsat tayi tsagal, tuwo zakuci? Yanzu kuwa, ta lodo masu har sai da yaya ta ce wannan tuwo kamar rugaye?
Ta yi dariya tare da yada masu magana ta ce wai don kuci Ku dauka kamar kullum* Duk sukayi damama ta wuce bata bi ta kansu ba ta ciko wata yar roba da man shanu ta kawo masu da ruwa da lemu sannan ta rike kugu da yake takadara ce ta ce *Sai me?
Yaya cikin yake ta ce tuwon ya mana yawa da akwai leda dana dauki biyu saboda dumame....... Jamila ta yi karaf nima zan dauki biyun nan........ Hafsat ta ce baku da matsala yanzu zaku ga tuwo, ta je ta sami ledoji hada Wanda zataci ta lodo masu sannan ta ciko wasu robobi da miya ta ce duk gashi ai tuwo baya hada fada gidan mamee.
Duk abin nan mamee ma bata San wainar da ake toyawa ba. Kawai masu tare fada ne Allah ya kawo mata.
Dama hafsat hake take dasu wurin party ance iyaye su fito kawai su yaya suka kalleta suka ce *Sai kuje iyaye* haka kuwa akayi ta tafi ta dunga rawa daman mamee ta bata himilin kudi ta ringa watsama ango da amarya.
Ganin yanda hafsat keyi duk sai suka tsargu rashin kyautawa ya dan damesu. Suna gama cin tuwon suka sulale ko bankwana.
( kai Allah ya ganar da masu irin wannan hali ).
Karfe tara abokai sukayi sukayi su rakashi ya ce wallahi shi zai kai kansa.
Sai da ya sallami kowa sannan. Suka mishi addu'a sosai saboda sunji dadin bikin sa yanda ba a zato ya bada gidan man shi daya duk Wanda zai tafi yaje yayi full tank.
Banda kayayyaki da ya raba, generator, spare tire , mashin mashin, kai abubuwa barkatai.
Ya shigo karfe goma da kwata, mamee na ciki ita dasu hafsat, ya leka suka gaisa ya fito mamin ta biyoshi, ya zauna falo, mamee na gaji.
Ta yi dariya da gajiya *madaki* sannu da kokari wallahi ka cika *Da* na gode Allah ya shirya maka iyalinka ya baka zuri'a dayyiba.
Ammkinnnn mamee love, ya kukayi da mutanen ki?
Tayi yar dariya kai lafiya qalau, girgiza kai kawai kawai yayi yasan fada mishi ke bata son yi.
Uwani duk ta tayar da hankalin ta. Ta fada tare da langabe kai.,
ya danyi murmushi kawai,
Ta kalleshi don Allah ka dubi maraicin yarinyar nan kaji tsoron Allah. Wallahi rikon maraya yana da matukar muhimmanci ga rayuwar dan Adam. Da mutane zasu gane falala da kuma dunbin rabon da mutum ke samu idan ya kyauta ta wa maraya lallai da wasu sun ringa bi gida gida suna sallamawa duk in da yake su dauko.
Mamee zan kwatanta na sani.
Ta harareshi na san ka da zafin kai madaki uwani yarinya ce kada ka biye mata don Allah.
Kadai ji yan surutan da yan uwana keyi idan ka rike kanka idan kuma ka banzatar wallahi zan dauki mataki....... Zan kiyaye mamee.
Jikin sa duk yayi sanyi.
Ta mishi nasiha sosai yayi shiru kawai.
Ta mike mu kwana lafiya sakonka nacen sama an kai. Ta shige ciki.
Ya mike a hankali yana zuwa yaga katon tire cike da gasassun kaji an rufe da foil paper.
Gaban sa ya fara faduwa, kamar bazai iya Shiga ba.
Tana zaune bisa gado kuka kawai takeyi , kukan maraici na ban tausayi.
Ya bude kofar a hankali.
Ta hadiye wani miyau dunkulalle cikin ta ya kada ya bada kulululu.......
Ya zauna shiruuuuu...
Ya dake ya fara magana cikin kakkausar murya . idan kin gama kukan zo nan in magana dake.
Tayi shiru ya daka mata wata tsawa..... Ta matso da sauri.
Ya yaye gyalen malama ki man shiru kinji.
Ta sunkuyar da kai.
Yayi kasa da murya, umaimah kamar an miki auren dole? Wannan kukan naki yayi yawa gaskiya, ya kamota ya maidota kusa dashi.
Umaimah wallahi ba abinda zan miki kinji har na rantse, zan tafi dakina ma in kwana, amma sai kin mun alakwarin zaki daina wannan kukan kuma zaki ci abinci...... Tayi saurin daga kai. Yayi murmushi good.
Sha re hawayen toh, ya fada yana gogewa da hannu.
Jeki yo alwala muyi sallah tukun .
Ta mike tayo alwala sannan shima ya shiga, bayan sunyi raka'a biyu kamar yanda sunna ta koyar ya dafa kanta yayi mata addu'ar da manzo SAW ya koyar sai ya fita ya dauko naman da ice cream.
Tana zaune ta zabga uban tagumi ya dan kalleta, ni zan baki ko zaki...... Tayi saurin kai hannu ta dauko ta fara ci.
Yayi yar dariya *Mrs madaki*...... Ta harareshi ya kyalkyace da dariya ba injini ba inji *yan jarida*
Da ta janye hannunta sai yace au kin koshi? To kawai in kwana anan......sai ta mayar da hannu haka har taci sosai, ya mika mata ice cream din sha kiban muyi kama kama inji yara.
Ta dan harareshi kadan, yayi murmushi.
Ya kalli jerin akwatunan lefenta ya ce *umaimah an bani da rowa* haka kika dawo da kayan baki ba dangi ba? Ana rabawa iyaye da yan uwa fa,
Ai na basu, ta fada kamar mai koyon magana.
Haba? Ya fada ganin ta danyi magana.
Ta ce Allah.
Su wa kika ba?
Ta dan kalli jakunkunan
Na ba baba shadda goma, su goggo atamfofi uku uku, itama luba na bata lesuka da kayan shafa, baba ma na bashi turaruka, an dibar ma dangi yankunnaye da atamfofi suma, sannan na bada *Hajiya ta* leshi uku, atamfofi biyar.
Cewa zakiyi kin rabar da kaya kaf! Sai kawai Tayi murmushi shi fa ya kirata da mai rowa yanzu kuma ta bayar yace ta rabar.
Ya kalleta yaushe rabon da ya ga murmushin ta?
Haka ya dan jata da fira har daya saura sannan ya ja mata kofa ya tafi dakin sa.
Yana fita ta saki ajiyar zuciya *Ohh madaki ikon Allah*
Barci ya dauketa saboda gajiya ga kuma kuka anci.
Shi ko sai kusan uku ya samu yayi barci yana ta gyare gyare.
Cikin kunnenta aka kira sallah, ta tashi da sauri ta shiga tayo wanka gudu gudu ta sanya wani material ruwan kwaiduwar kwai,sai da ta gama sallah sannan ta dan shafa mai ta zauna lazimi, shidda da rabi ta shiga ta wanke kewaye, sannan ta zo ta gyara gadon ta jera jakun kunan duk ta dan gyara fasalin dakin sannan ta kunna abin turaren kamshi mai kamar kwanon glass ga sanyin A.C, ta dauko wasu turarukan ta na cikin lefe ta feffesa ma labulan daki., nan da nan dakin ya rikice da wani irin kamshi.
Ya dan kwankwasa, tayi saurin zama kamar tana lazimi kafin ta ce *Shigo*....Yana sanye da jallabiyar da ta siyo mishi, ya dan turo a hankali sanyi da kamshin dakin ya daki hancin sa,
.......ina kwana, ya dan lumshe ido *Morning sweetheart* yayi suka bisa gadon mamee ta ce idan kin gyara gado baki so a bata miki, ta mike tana ninke abin sallah tana murmushi.
Shi ne kika bari na makara ko? To Alhaki kanki.
Ta dan saci kallon sa kadan, ya tashi zaune miko mun littafin can, tana zuwa ya damko hannunta, kilibabba kina ta wani satar kallon miji kedai umaimah baki waye ba, ta kyalkyace da dariya tana noke fuska,
Ya cacumota bari dai in fidda miki kunyar nan ta daina takura mu........ Ta fasa ihu wayyo na shiga uku wallahi na daina wayyo mameee.......... Ke tsaya saurara wasa nakeyi ya tallabo fuskarta, wasa nakeyi ya jaddada mata da kai.
Duk illahirin jikin ta ya rikice da kyarma.
Ya kwantar da ita bisa kirjinsa yana bubbuga bayanta, ya hakuri wallahi wasa nakeyi.
Ya dan runtse ido, lallai yana da babban aiki wannan tsoron na umaimah yayi yawa.
Ya dagota, ki saki jikin ki dani ki yarda dani please bana son wannan tsoron da dararewar.
Ta danyi murmushi, ya ja hancin ta yar rainin wayo kamar ba matsiwaciyar yarinyar nan ba.
Kwanta muyi barci...... Ta zaro ido mamee zan gaido.
Ya dan muskuta ya cire jallabiyar daga shi sai vest da dogon wando ta dan basar don tana motsawa zai jata jikin sa.
Ya mika mata, malama to lunke tunda cirewar ma kin kasa taimakawa, ke kam kina ban kunya, idan miji zai cire riga sauri akeyi a cire mishi kar ya wahala...... Ta danyi murmushi . ita dai duk bata amince da shi ba.
Ya maida kansa bisa filo don Allah kizo mu koma barci....... Bana ji. Ta ce a hankali.
Ya fizgota ke bazan dauki wannan gidadancin ba.
Na shiga.....yayi saurin rufe mata baki da hannu shiru kiyi barci.
Tayi lamoooo kirjinta na harbawa, ya kai hancin sa a wuyanta lallai amaryar nan kina zuba kamshi. Gabanta ya fadi ta fara raba ido.
Yana ta faman zolayarta, a hankali a hankali taji ya fara saukar da numfashi alamar barci ya daukeshi.
Ta saki ajiyar zuciya ciki ciki a hankali. Ta bashi kamar minti biyar sannan ta zame jikinta a hankali ta maida mishi filo, har zata fita taga yadan ja kafarsa alamar kamar yana jin sanyi, sai ta koma a hankali ta rufe shi da bargo sannan taja kofar ta fice,
Ta sauka, dakin mamee tayi ma tsinke, bata ciki ta zagaya dakin baki wadanda basu kai ga tafiya ba su naryam hamza, hafsat, Aunty Aisha, duk dai aminan ta suna nan.
Sai kawai ta fada toilet ta wanko shi fes!
Sannan ta shiga gyara mata dakin, duk wani sako da loko sai da ta sharo shi,
Sa'annan ta goge ta feffesa abun kamshi, ta kusa karasa gyaran wodrop kenan taji mamee ta rafka salati bayanta.
Mi zan gani ni *Rabi*, uwani??????
Ta yi sauri ta isa kusa da ita tana murmushi tare da zukunnawa *Mamah* Ina kwana,.
Ta kamota ta mike, wanene ya turo ki wannan aika aika? Ina madakin?
Ta dan dukar da kai *Yana barci*........koma sama maza ga kalaci can an hau dashi...... Kuji mun yarinya ni jikar buzaye kai *Uwani* al'amarinki sai ke.
Ta danyi dariya kai mamah bari in karasa gyaran...... Ke bani son iyashege kinji zaki koma daki ki huta ko sai..... *Kai mamah* ta fada kamar zatayi kuka, ta dauko kwadon zuba shara ji fa abinda na sharo dakin nan in banyi ba waye zaiyi?
Su mansurah ta bata amsa. Ta zumbure baki ta juya tana ci gaba da lunkewa.
Ta matso kusa da ita, zaki wuce ko sai na kwakkwada miki wannan ludayin da ke hannuna. Maza kije ki tado mun shi kice yazo su Aunty salma zasu tafi dasu Hafsa....
Ta danyi murmushi Allah dawowa zanyi ko na kirashi ta wuce ...... Ta bita da kallo tana yar dariya *Uwani* ....... *Uwani* ikon Allah.
Allah dai ya baku zuri'a dayyiba. Wannan kuruciyar taki gara yazo ya daukeki kubar kasar can kya dan natsu kisan kin girma ja'ira.
Tana buda kofa ya farka, amma sai yayi shiru cikin bargo.
Ta zo tayi tsaye kansa tana alwalar kuda, ya fara dariya saboda tabbas yasan kiransa zatayi.
Ta dan juya *Kazo inji mamee*, yayi shiru
Ta kara cewa, shima ko motsi,
Ta ce *Madaki*........ Ya lumshe ido kamar bakinta sunan ya fara fitowa,
Kaji mamee na kira shima yayi shiru,
Ta dan sa hannu ta yaye bargo kawai ya fizgota ta fada saman sa,
Innalillahi dama kana jina?
Ba'a sani ba, ke dai ba kauya ce an fada miki ko a kauye yanzu ana tada miji haka?
Ya kara matseta, haka zaki dan hawo sannan ki dan mun kiss kamar haka...... Ya mata a goshi sai ki fara cewa *Honey*......... Kina dan shafani.......ta wuntsula ta sauka ya kyalkyace da dariya.
Mikon rigar in saka, tana daukowa ta wulla mishi ta sauka da gudu ya fara dariya.
Shi ya kai su Aunty bintar airport da kan sa.
Kiri kiri mamee ta hana umaimah saukowa dole ta tafi daki tayi zaune.
Ya shigo da sauri rike da kayan kalaci, yarinyar nan abinki akwai son kai shine kika gama cika cikin ki ni ko in gane?
To zo muci mamee ta koroni yau. Tayi murmushi nima koroni tayi.
Ya kyalkyace da dariya kyaleta gobe kamar yanzu mun bar mata gidan.
Ta kalleshi da sauri,
Ya kai dankali a baki Dubai zamu honeymoon......................
Good morning Maman Abdallah
Godiya ta musamman ga *Salamatu dahiru* ( MZ) Ayi mun uzuri yau post daya zanyi. Wannan.
ME NENE AMFANIN ROOTING KUMAMIYE AMFANINSA A ANDROID DA
Shide Rooting samun dama ce akan operating System din wayar ka, domin sarrafa ta yadda Kake so, idan kai masanin computer ne rooting Kaman samun dama ne akan windows Dinka ko administrator rights, misali a café idan zakayi wani abu se ace you do not have Permission to do dat, sabida administrator din
ya iyakance maka abunda zaka iya yi, ko kuma in kana da laptop kai as me computer Zaka iya komai amma me amfani da guest
account bashi iyawa… rooting kenan zata Baka daman yin komai da administrator yake
yi, idan kai masanin wayar symbian ne Kaman Yadda amfani da x-plore take nuna maka
komai nakan folders din ka haka android zata Koma idan anyi rooting, koda kuma ba’ayi Rooting ba zaka iya installing application me buqatar rooting sede bazatayi aiki ba, zata rubuta root access denied ko tace no root privileges Rooting tana bada daman shiga lungu da Saqon wayar ka, akwai restrictions ada yawa
a wayoyin android amma sanadiyar rooting se Kaga ka samu dama ka wuce restrictions din Kena a taqaici yin haka a Android kaman Hacking ne a Symbian, kunsan itama symbian
ana mata hack domin samun dama nayin wasu abubuwa akanta cikin sauki wanda Rashin yi mata wannan hack din xai iya hanaka yin wani abun sannan kuma Kaman Jailbreaking ne a iOS (iPhone, da iPad)kuma Android kadai akeyiwa rooting
.
MENE NE AMFANIN ROOTING? KUMA DOLE NE SE NAYI ROOTING NA WAYANA NA ANDROI?
A’a ba dole bane kayi rooting wayar ka ta Android idan kai ba irin wanda baya riqe waya dan fashion bane sai dan sirrikan da ke wayar Tare da karantar ita kanta wayar ta inda duk wata matsala zaka iya sanin dalilin ta… Idan Burin ka shine kaga ka riqe wayan kana kira koka hau 2go ko fb, ko kayi chatting a whatsapp, ko kallon videos da daukan hoto to baka da buqatan rootin…. Amma idan kai burin ka ka cika wayar da application ne kuma kai ma,abocin browsing ne da son ganin kana upgrading version din android dinka Kaman yadda masu bb sukeyi, ko ka canza ma wayar fasali ta yadda wani can me irin wayar ka zeyi mamakin ganin naka domin banbancin su a Application to kana buqatar rooting…
.
AMFANIN ROOTING SUNA NAN KAMAN HAKA
1. Zaka samu daman installing HD game masu girman gaske, kuma ya hau wayar ka Koda kuwa ba HD bace.
2. Zaka samu daman installing applications Kowani iri, Kaman file explores masu bude zip files harda ganin qoqon cikin wayar, da Applications Kaman anti virus wanda ze kare Ka daga virus gurin browsing ko ta Bluetooth.
3. Rooting ze baka daman using VPN service wanda shi aikin VPN shine ya boye ip address dinka ta yadda idan kana Nigeria kana browsing, ze riqa nunawa Kaman kana wani qasa ne can waje, kuma idan akwai Restrictions misali Kaman MTN to VPN din ze hana mtn blocking dinka… (Har Free Browsing zaka iya yi idan kayi rooting)
4. Rooting zai baka daman qara RAM din wayar ka, idan kai masanin computer ne zaka fahimci mene ne RAM, shi, RAM wani Hardware ne wanda ke taimaka wa gurin saurin sarrafa abu a na’urar ka, saurin wayar ka ta Android is determined by the availability of your RAM, wasu RAM din wayar su rabin 1gig Wannan shine dan takaitaccen bayani akan
root Bisssalam Allah yasabada Sa a, Amin
WANE NE UMAR?KUMA MENENE KADAN DAGA FALALARSA
WANE NE UMAR?KUMA MENENE KADAN DAGA FALALARSA?Umar shine umar ibn khaddabi,da ga kabilar bani addiyyi kuma idan ka bi silsilar kakannin umar daga na daya zuwa na takwas zaka taras sun hadu da manzon Allah s.a.w saboda kuraishawa ne gaba dayansu.Umar yana daga cikin manyan mutane tun a cikin jahiliyya,haka kuma a musulunci,har kuma mutuwarsa.kafin musuluntarsa Annabi xayi masa addu'a sau biyu shi da Abu jahal,sai Allah ya zabe shi don ya musulunta kuma musuluntar umar ta kawo ci gaba da daukaka ga wanna addini.[bukhari ya ruwaito].ABUBAKAR SIDDIKU R.A shi ya zabi umar da khalifanci lokacin da yazo mutuwa.kuma har yake cewa "idan na mutu Allah ya tambaye ni me yasa na baiwa umar shugabanci?to zance wa Allah "lallai na wakilta musu wanda ya fi su tsoron Allah".haka umar xayi shugabanci da siyasa da adalci irin wanda ba a taba gani ba, kum hakan ya bayyana ne saboda tsawon lokaci da yayi a mulki,idan ankwatanta shi da abubakar.ANNABI S.A.W yana fada a wani hadisi cewa:"Nayi mafarki sai na ganni a kan wata rijixa tare da Abubakar da umar.sai na debi ruwa na sha.bayan na sha sai Abubakar ma ya debo ya sha amma a cikin dibannasa akwai rauni,sanna sai umar bin khaddab ya karba yana karba sai abin diban ruwan yazamo kato<babba>umar bai gushe ba yana ta diban ruwan nan har ya shayar da mutane gaba daya[bukhari ne ya ruwaito]A wanna hadisin manzon Allah xa nuna cewa bai taba ganin mutum mai kokari da jarumtaka irin ta umar ba.don haka malamai ke cewa wanna Annabi s.a.w yana nuna ci gaba ne da kuma bunkasar da daular musulunci za ta samu a lokacin sayyidina umar.saboda a lokacin umar ne r.a akayi yake yake manya manxa wadanda suka zama rabewa tsakanin karya da gaskiya.a lokacin umar ne akayi yakin kadisiyya,da Nahawali wanda ya karya daular maguzawan farisa ta iran.wanda shi'a ke jida ita.a lokacin akayi yakin yarmuk wanda ya karya kiristoci.YANA DAGA FALALAR UMAR ANNABI S.A.W KE CEWA:A CIKIN BANI ISRA'ILA ANA SAMUN MUTANE WADANDA ALLAH YAKE SA MUSU DACEWA DA ABINDA SUKA FADA ZAI ZAMA DAI,DAI TO A WANNA AL'UMMAR KUMA SHINE UMAR.YANA Daga cikin falalar umar annabi s.a.w yace Nayi mafarki kowa da riga wani ta dangale masa,amma shi umar tasa har jan kasa takeyi.sai aka tambayi annabi s.a.w mene ne fassarar wannan?sai yace Addini ne na umar cikakkake "kuma annabi s.a.w yace duk lokacin da umar ya hau hanya to shaidan sai ya canja hanya.zamu gaji don falalar dayawa,amma dai zanci gaba akan mutane goma da aka musu busharan aljanna lokaci guda.ALLAH YA TAIMAKE MU
Thursday, January 24, 2019
Labarin transfer na yañ wasan kallon kafa na duniya
Kungiyar kwallan kafa ta Chelsea ta kammala daukar Higuain a matsayin aro loan na watan 6 tareda zabin sayensa akan zunzurutun kudi har kimanin $32 idan Dan wasan yayi musu.
( daga jaridar Sun Sport) Kungiyar kwallan kafa ta real Madrid tace ta shirya tsaf a kokarin da takeyi na ganin ta Rabauta da daukar Dan wasan kasar Argentina da Kungiyar kwallan kafa ta juventus wato Paulo Dybala.
Kungiyar kwallan kafa ta Ta Barcelona Tayi Nasarar kammala daukar matashin Dan Wasan
Ajax Frankie De Jong*
(Daga jaridar Tuttosport Ta rawaito .)
Dan wasan bayan Kungiyar kwallan kafa ta Real Madrid Marcelo ya bayyana sha'awarsa nason barin Kungiyar kwallan kafa ta Madrid inda Danbwasan yakeso ya hade da abokin wasansa a Madrid wato cristiano Ronaldo. (Daga jaridar Tuttosport
Kungiyar kwallan kafa ta Real Madrid ta shirya tsaf domin ganin ta doke Kungiyar kwallan kafa ta Manchester united akokarin da Madrid din keyi na zawarcin Dan wasa malito dake potor.
Kungiyar kwallan kafa ta Bakseksehir dake fafatawa a Turkish super league ta kammala daukar Dan wasa Demba Ba
Kungiyar kwallan kafa ta Carpi dake fafatawa a Serie B ta kammala daukar Dan wasa Muhammad kuolibaly daga Kungiyar kwallan kafa ta Udinese. A matsayin aro loan.
Kungiyar kwallan Kafa ta Derby county ta kammala daukar tsohon Dan wasan baya na hannun daman kasar England wato Ashley Cole.
Kungiyar kwallan Kafa ta Genoa ta kammala daukar Dan wasa baya na hannun dama mai suna Giuseppe Pezzella, Daga Kungiyar kwallan Kafa ta Udinese dake Italy. A matsayin aro na watan 6 tare da zabin sayensa idan Dan wasan
yayi musu.
AC Milan sun kammala daukan dan wasan gaba na Genoa mai suna Piatek.
Kungiyar kwallan kafa ta Borussia Dortmund ta fara tuntubar wakilan Dan wasan Kungiyar kwallan kafa ta Crystal palace wato Wilfreid Zaha a kokarin da Kungiyar kwallan kafar ta Dortmund din keyi na daukar Dan wasan Anasaran cewa Dan wasan zaikai kimanin $50
Mario Balotelli ya koma Marseille da taka-leda kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana, bayan da ya bar Nice.
Rahotanni daga kasar Jamus sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich zata kalubalanci kungiyar Manchester United da Chelsea wajen neman dan wasan kungiyar Real Madrid, Gareth Bale a kaka mai kamawa.
Scott McTominay ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da rabi domin ya ci gaba da zama a Manchester United bayan an dauki dogon lokaci ana tattaunawa da dan wasan da kuma
kungiyar.
Wednesday, January 23, 2019
Kasuwanci na
1
Official
By
AsmaBaffa
BISMILLAH
Alhmdllh fans Allah ya kara kawo mu sabon Novel dina KASUWANCI NA da fatan zaku bibiyeni muji yadda zai kasance,Fatana Allah yasa mu karu da juna,Allah yasa masa Albarka ya fadakar ya kuma nishadantar daku.ina matukar Godiya masoyana,masoya novels dina,masu sharhi musamman AsmaBaffa fans club,Taskar fiddausi sodangi,da kuma House of Hausa Novels ina miko dubun gaisuwa ta gareku na gode da Sharhi.
Da fatan zaku ci gaba da Sharhi a kai Kai sabo da shine yake guiding writer ta rubuta muku me dadi da ma'ana,idan ba Sharhi baya tafiya dai dai,Dan Allah a dinga Sharhi fans ana nishadi musamman yan gp na.
Akwai gps da dama da basa Sharhi ko tnx baza suyi ma ba,zaka ta musu posting shuru,sai ranar da ba ayi posting ba sai a fara neman novel ci gaba.duk gp din da basa cewa ko Hi zan daina musu posting wlh,da nayi daya biyu naji duf to shike nan sai suji duf nima🤣🤣
Wannan page na farko na Sadaukar dashi gareki sweet frnd FLOWER.
Kudin cinikin awarata nake irgawa duk da ba kudin arziki bane amma dukkansu daga yan goma sai yan biyar sai ko ashirin,kanwata na shiga kwalawa kira MEENAT wai baza ki fito ba sai na shigo na mareki,Maganar AMMA naji tana daga gefena a kwance saman yar tabarma tace Haba MUFEEDA ta wannan wacce masifa ce haka dan Allah ki dinga dagawa yaran nan kafa kannenki ne fa,Amma kina dai jin tun dazu nake jiransu su fito su tafi Islamiyya amma sai nauyi sukeyi kuma sun San cewar anjima zan soya Awara,gashi gobe zasu zo suna takura mana a basu kudin Break, to ai sai bisu a hankali dan Allah kinga ni ba lafiya ce dani ba kece komai nasu kece uwarsu kece Ubansu Mufeeda kece komai dinmu,Zuciyata ce tayi rauni nace to Amma ba komai na Dena kiyi hakuri Allah zai baki lafiya kinji,ga kudin nan Amman mu bari na gyara gidan na daura mana tuwo naga muna da ragowar garin masara,Murmushi Amma tayi tare da kallona tace Mufeeda Allah ya miki albarka Allah ya baku miji na gari,ya baku yara su rama muku abinda kukayi mana na alkhairi,Mufeeda yau shekarar babanku Sha uku da bacewa,har yau ina Sa ran watarana zai bayyana da Zanfi kowa murna ya ganku Ku uku kun Zama yan mata gaku kyawawan gaske kamar indiyawa,musamman ke Mufeeda kunfi kama da Shuwa sosai mahaifinku kika biyo domin shine fari kamar balarabe haka yake har kin fishi Hasken fata ma,su kuma su Meenat sune masu kalata wato su ba farare ba su kuma ba wanda zai kira su bakake duk gaku Allah ya bani Ku kyawawa farare daku amma duk kyan nan sabo da talauci ko Sallama ban taba ji ance ana sanku ba,wanda na tabbata da masu kudi ne komai muni auruwa sukeyi,musamman ke Mufeeda kin kai har 16yrs amma nafi so na aurar dake tunda ba makaranta kike zuwa ba,Baki na turo gaba tare da sakin shagwaba ina shure shure kamar yarinya ina kukan sangarta Allah Nidai Amma bana son aure kuma ma nawa nake,hmmm Mufeena Mufee tawa ai gashi nan kin fara girma har da Irgan dangi,Ammah mene Irgan dangi? tace gasu nan a kirjinki Kin fara Nono Mufeeda akwai maganar da za muyi anjima idan yaran nan sunyi bacci,kunya ce ta kamani nace to Ammah Allah ya kaimu bari na gama aikin ko kina da bukatar shiga bayi na taimaka miki? Ae rikeni muje Mufeedata Allah ya miki albarka,
kama Ammah nayi da kyar tana rike da sandar karfe wacce a asibiti aka bata ita na kaita har bayi ta tsuguna tare da Dafe jikin bango,sai na fito bayan ta gama abinda zatayi ta kwala min kira na koma nace Ammah ko na goyaki? Dariya tayi tare da cewa na gode Yata baki ji me Doctor yace ba?na dan dinga takawa,murmushi nayi wanda yasa hakorana kanana farare suka bayyana,dimple dina ya lotsa riketa nayi muka fito tare,sai Lokacin kannena MEENAT da MA'EESHAH suka fito cikin shirin makarantar Islamiyya,na kallesu cikin tsafta kayansu yasha guga,sun bani sha'awa naji inama nima haka nake zuwa kullum amma ina bazan samu dama ba,amma Alhmdllh tunda kannena suna zuwa ba matsala.Amma ce ta kalleni cike da tausayawa tace Mufeedata? Da sauri na dawo daga tunanin dana lula na kakalo Murmushin dole nace Ammah ki huta bari na gama aikin naje na siyo kayan alewar madara,kinga gobe kuma da safe Kosai yana jira shima,amma ni naga awarar tafi riba ma,Ammah tace Mufeeda wannan satinfa naji zuku yi Allurar polio vaccine da kukewa yara,Mufeeda tace wlh Ammah ba sauki abin ni haushi na ma gidan masu kudi kantama kantama na GRA Ammah ayi ta wulakanta mu da kyar mukeyi muna Shan wahala,wani gidan ma kafin ka shiga tashin hankali ne ko ina securities ne,aikina naci gaba da yi muna hira da Ammah mahaifiyarmu,saida na gyara gidan tas na kunna turaren Wutar kamshi duk da gidan ba wani me kyau bane amma ita tsafta bata buya,Allah ya haliccemu da tsananin Tsafta wanda duk Bala'in mutum bazai ce gidanmu akwai digon wani abu na kazanta ba haka muke gaba dayanmu,miyar Kubewa busashiya na kada,na tuka tuwon masara na kwashe cikin wata tsohuwar Cooler dunmu,nayi wanke wanke da wanka na shirya cikin kayan gwanjo na Riga blue me layi layi na fari,tare da skert shima ruwan goro,farar Powder na shafa da Vaseline a lebena,Hijab me hannu nasa wanda ya wuce gwiwata nace Ammah bari na siyo kayan nan nazo na fara soya Awarar dare kinga magriba ta gabato,Fadada murmushinta Ammah tayi tace a dawo lfy Allah kiyaye hanya.
Ameen nace tare da fita waje ina dan wasa da kudin dake hannuna cikin unguwarmu layinmu na bari nayi tafiya me Nisan gaske Allah yasa ma ba rana sai da na gaji sosai kafin na karasa wata yar kasuwa karama da ake saida kayan abinci da fruits etc, inda na saba siyen waken kosai da sauran kayan Sana'a ta na karasa da fara'a dukkanmu munyi sabo da juna sabo da yau da kullum,kudin na mika ina bi ko wanne layi duk na hada abinda nake bukata kaf aka hado min a wani katon buhun bacco na fito da kyar nake dagawa ina nishi haka nake tafiya a hankali, wani dattijo ne yace yarinya kawo a daura miki a kai ai zaifi ko? Murmushi nayi masa ya amsa ya daura min na masa godiya naci gaba da tafiyata da kyar,sai da nayi nisa na shiga wani layi wanda manyan gidajen masu kudi ne na gani na fada,GRA ce ta masu kudi nabi ta ciki sabo da kullum ta hanyar nake wucewa ko sabo da nasha kallon hadaddun gidaje tare da Lambu masu kayatarwa duk kuwa da cewa na saba shiga sabo da rigakafin polio na nake aikin dole muna neman Izni mu shiga sabo da tare da masu Unguwanni muke yin rigakafin dole su yarda a shiga ko Police su kama me gidan haka aikin yake.
Wasu motocine a kalla sun kai guda takwas a jere dankara dankara ban taba ganin irinsu ba sai yau da suka shararo da uban gudu kamar zasu tashi sama cikin layin,dai dai wani gida suka Parker wanda gidan yafi kowanne kyau a layin da gudu na matsa tare da rakubewa a jikin ginin gidan ina kallon ikon Allah,
da sauri naga sojoji sun fito daga sauran motocin tare da zagaye wata uwar shahararriyar mota me kyau da tsada na fitar hankali,wani dattijo ne ya fito fari kar dashi yana sheki da Alama kudi sun ratsashi a matukar hasale ya fito daya bangaren ma wani wani mashahurin matashi ne ya fito da sauri a matukar hasale cike da isa hade da Izza Saurayin kamar balarabe ko Bature haka yake duk Haske da kyau na da ake fada sai naga wannan ya wuce nawa ya zartani a komai nan take na raina kaina musamman yanda na kalli shigata babu maraba da Almajira mara gata.
Saurayin bazai wuce 35years ba ya kai karshe a haduwa gashinsa abin kallo kansa style din askinsa abin kallo ne abin birgewa da sha'awa,idonsa ya bude,ban San sanda nace wow a raina ba idonsa kamar madara yana wani lumshewa gasu Dara Dara,girarsa har kamar zata hade,ga wani dan saje da gemu masu matukar kyau da suka kawata fuskarsa,hancinsa me matukar kyau kuma baiyi tsini da yawa ba,dan bakinsa wow masha Allah ga wasu pink lips duk da cewa nima bakina kamar cokali bazai shiga ciki ba gashi lips dina jajir dasu amma sai naga wannan kam nasa sunfi nawa komai,kuma sai na tashi me duhu a kansa ko dan shi Hutu da Naira sun ratsashi ne oho, Kana nan kayane a jikinsa wandon pencil Jean brown color,rigarsa fara tas da top Brown ya daura sama takalminsa fari half cover flat shoe,shi ba gajere ba shi ba dogo da yawa ba,haka ba ramamme ba kuma bame kiba ba,kai masha'Allah da a mafarki na ganshi ba shakka Aljani zance.
Dattijon cikin farar shadda kar cike da Fada yake magana da alama da Saurayin yake,AAYAN will u hear me out pls,da sauri Saurayin ya bata rai cike da fushi yana shagwaba kamar dan yaro cikin muryarsa da ta girgiza ni sabo da dadinta yace pls Abbi I knew it just leave me alone For God sake,Hajja she is ur mother not mine so Abbi kaine ya dace kabi Umarninta ba ni ba,taya zata dinga takura min ni kadai ne jikanta gasu nan da yawa maza da mata,ko kawai dan ni bani da Mahaifiya bata raye,sannan mahaifina bashi da lafiya bakwa kaunata shi yasa ni kadai ake ma haka yanzu ina Abuja kace dole sai na dawo Kano da Zama kusa da Ku,ban taba wani rayuwa a kano ba ka sani sabo da kana matsayin mahaifina nake maka biyayya,sabo da gudun saba maka na bar muku gidanku,bana amfani da sisin kudinka,Allah ya bani nawa Abbi har na fika ma maybe kudin,But why me,why are u doing this to me,kowa a Family kaf maza da mata nine ba a so me nayi musu?idan sabo da Umma ne bata raye sai na huta,Abbi ban shirya aure ba kunsa nayi ba muguntar da ba ayi min ba,haka mun rabu,kun kara aura min wata itama mun rabu sabo da matsalar dake damuna na rashin lafiyar haihuwa Abbi kun San bani da lfy bazan iya Rayuwar aure da mace ba akan me zaku ce na kara auro wata so kuke mata su kasheni bazan iya musu amfanin komai ba,dalilin bacin rannan da nake Sha kasan yanzu Hawan jini gareni me karfin gaske ko wanne lokaci zan iya rasa raina,sannan kasan Ina da diabetes dalilin Hawan jini yasa ya kamani tawakali da addua nakeyi,Abbi why not bakwa tausaya min,bakwa tausayin rayuwata tun tasowata a wahala na tashi a duniya,wannan yasa na tsani mata wlh Bana kaunar duk wata budurwa komai kyau da hankalinta,dalilin haka bana Hulda da kowa family da frnds etc ni kadai nake rayuwata sabo da bakin ciki da halin da nake ciki shi yasa nayi nesa da kowa,gwiwoyinsa ya dire a kasa hawaye na kwarara a idonsa kamar ruwa tare da rike kafar dattijon yace Abbi ka fadawa Hajja zan zauna daku amma pls kar ayi min aure again ko me kuke so wlh zanyi amma yanzu banda aure,Abbi ka tuna kusan mutuwa nayi yanda mata suka ci min mutunci.
Kallonsa Dattijon yayi tare da cewa tashi Aayan,zan yi shawara da yan uwana, muyi deal duk abinda mukace zakayi ka yarda? Ba tare da yayi tunanin komai ba Yace ae Abbi na yarda indai bazanyi aure ba shike nan,Abbi yace an gama ko ka samu Lfy kana haihuwa sai na yarda zakayi aure ka tabbatar?Kuma ko kaga wacce kake so baza ka aureta ba har sai in mune muka yarda?cike da murna yana murmushi ya daga kai alamar yes ya Amince,Abbi yace Good for u,kar kaga bani na haifeka ba kace zaka min butulci zan iya yi maka abinda baka tunani,ka dinga tunawa da halina kasanni sarai zan iya yi maka ko mene ne ba ruwana,Shi dai Bayan murna yake yace ya yarda,Tashi muje daga yau ka dawo Kano gida daya zamu zauna sai dai jefi jefi kaje Abuja harkokin business dinka shima sai idan da yardata idan kuma kaki zan iya haram tama Business dinka gaba daya kasan nasan komai akan hanyoyin da zan lalata duk dukiyar daka mallaka,
Aayan ne yayi murmushi tare da cewa Abbi matukar baza kuyi min aure na zauna da mace ba zan iya mallaka muku komai nawa,na tsani mace a duniya ni bana son Zama dasu wlh ko yan uwana banso,kallon tsana Abbi yayiwa Aayan tare da cewa dan kawai baka da lafiya ne Man amma wa yaki mata?ai mata sune jin dadin duniya,kaga duk son kudina?Saurayin ya daga kai yana murmushin takaici,Abbi yace to duk kudin da nake nema sabo da mata nake nemansu,mata mutanenmu in ba su mene amfanin kudi.
Kai Aayan baka da amfani a duniya fa da kai da gawa daya kuke Banga Amfaninka ba sam,to kai baka haihuwa,baka iya Yiwa mace komai me kakeyi kake wahalar da kanka wajen neman kudi,gaka a haka kamar Namiji Amma na tabbata in dai ba mune muka zaba maka mace ba irin almajira ko talakawa sune suke neman kudi sune yan wahala sune wahalallu wanda basu san kansu ba,basu san me duniya ke ciki ba,basu da wani amfani da irinsu ya dace a nema a aura maka sune watakil ka samu me son kudi tayi kasuwanci da kai ta samu kudi ta zauna da kai da hakuri.
Aayan yaji matukar zafin kalaman Abbi wanda gaba daya ji yayi kamar ya mutu Sabo da bacin rai,haka ya hakura ya danne bakin cikinsa Amma idonsa ya kada yayi jajir,sai da Abbi ya gama gasa masa bakaken maganganu masu zafi sannan yace tashi muje ciki kasa a kawo ma motocinka kasan ko aron nawa ko na gida babu me baka kamar yanda kace kowa yayi amfani da kudinsa,Aayan yace ai duk new nayi Order an siyar da wancen saban yayi za a kawo min gobe,dariyar mugunta Abbi yayi tare da cewa kana kokari fa wlh ni da kai da gawa haka nake kallonka baka da amfani a duniya me zaka amfanawa wani?ko mace baka amfana mata komai ba sai wa? Bakin ciki ya tokare zuciyar Saurayin yana tsaye a gate har Abbi ya bawa Sojojin da suke can gefe dasu Umarnin su shigo da motocin gida,nan suka bar Aayan wanda ya dafe saitin zuciyarsa da hannunsa,har suka shige da motocin gidan,suna rufe gate din ya fadi a wajen ya sankame kamar ya mutu,gashi unguwar shuru ba kowa bare a taimaka masa.
Ni da nake Rabe ina jin komai da Sauri na jefar da kayan dake kaina nayi kan wannan Saurayi cike da tausayawa,tunani na sumewa yayi,na rasa ya zanyi na tasheshi robar ruwa dake hannunsa na Eva na fisgo da Sauri hannuna na rawa na bude tare da kwara masa a fuska Amma shuru bai tashi ba,hannayena biyu na daura saman kirjinsa ina dannawa kamar yanda nake gani likitoci nayi,yi kawai nakeyi ba ji ba gani danna kirjinsa nakeyi sosai ina nishi,a rude na kara kwara masa ragowar ruwan na sunkuya a kansa kamar zan shige masa ciki,kamshin turarensa yasa kamar na sume Sabo da dadi,fatarsa laushi kamar auduga lumis,wukil naga ya bude ido mun hada ido dashi kafin na kifta ido naji an sharara min uban Mari sai da na daina gani na wasu yan lokuta,kafin na dawo hayyacina yasa kafa ya harbar dani da mugun karfin da sai da nayi uwar Sufa na tuntsira naci ta ka na kife can gefe yaraf,nan take lebena ya fashe fuska ta ta kumbura,sabo da rashin Imani bai kyaleni ba takowa yayi har inda nake ya kara Sa kafa yayi ball dani sai da kaina ya bugu da wata yar bishiya,kafa yasa ya take hannuna dake yashe kasa ya murza,idonsa yayi ja da hannu daya ya damki wuyana ya shake tare da rabani da kasa ina kakari,Mari ya shiga yarfa min ban san iyakacinsu ba sannan ya jefar dani kasa kamar wani kayan wanki,Kuka me karfi na saki duk dauriyata ban san inda kaina yake ba,tunani na mahaukacine dama ashe,ina ta kuka a wajen Fuskata ta kumbura sosai jikina duk wani wajen ya farfashe Sabo da ball da ya dinga yi dani,tsorinsa ya shigeni ina nan wajen har ya shige cikin gidan da motoci suka shiga,Allah ne ya taimakeni wani dattijon kirki yazo wucewa a motarsa yace yarinya motace ta bigeki?Ban san me zance ba kawai sai nace kare ne ya biyoni shine na dinga faduwa,mutumin bai yarda ba Amma ya Kira Driver dinsa yace ka dakko mota ka kai yarinyar nan asibitina ka samu Sajeeda tayi mata dressing ka maidata gidansu kayi Sauri dare ya fara,godiya nayi masa ina kwance a kasa ina tunanin zalincin da Saurayin nan ya gwada min tare da rashin Imani daga taimako sai naci Dukan tsiya,
haushinsa naji sosai a raina ga tsoronsa da ya dasu a Cikin raina bana fatan sake ko kallonsa Sabo da tsoronsa nake ji yanzu.
Ina tunani a kwance Dattijon Driver ya karaso tare da bude min mota da kyar na iya shiga motar,Driver ya saka min kayana a Cikin motar wanda na siyo a kasuwa,wani hadadden asibitin kudi ya kaini nan take akayi min komai da ya dace aka bani magunguna da Alama asibitin dattijon mutumin ne da ya Bada motarsa a kaini gida,Driver na gwadawa gidanmu ya kaini har kofar gida sannan ya miko min dubu biyu yace na sha Maltina inji Alhaji me gidansa,da kyar na yarda na karba,shima sai da Driver ya nuna baiji dadi ba sannan na karba tare da zuba godiya na dauki kayana na shige gidanmu shi kuma yaja mota ya tafi,ina shiga gida Kannena Meenat da Ma'eeshah har sun yanka awarar suna jirana da gudu suka taso suna Sister Mufee me ya sameki?lfy?hatsari kikayi ko motace ta kadeki,kinga yanda kika koma kuwa,Da Sauri Ammah ta fito da Rarrafe kamar zata kifa Sabo da rudewa tana Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un shine Abinda Ammah ke furtawa tana Hawaye tare da cewa me ya samu Mufeedata?Me ya samu katangarmu? Kuka na fashe dashi me karfi tare da Rungume Ammah ina cewa ba komai Ammah a wani layi ne kare ya biyoni na dinga gudu na fada cikin kwalabati da kyar wani ya taimakeni ya kaini asibitinsa kinga an bani magani harda kudi dubu biyu na shan Madara da Maltina,Ammah tace wannan waye me kirki haka?Wlh Ammah wani ne Doctor ne Babban mutum ya sa Driver dinsa,to ku dai kiyaye da mazan zamani a tsare mutunci,Alhmdllh tunda komai yazo da sauki,Meenat ki dafa mata ruwan zafi ta gasa jikinta taci abinci tasha maganin ta kwanta,ke Ma'eeshah jeki kofar gida ki fara soya awarar kafin yan siya su fara taruwa, mikewa mukayi tare da aikata abinda Ammah ta ce.
Bayan nayi wanka na gasa jikina Mai na shafa sannan na Sa doguwar riga mara nauyi itama yar gwanjo ce,abinci na dauko tuwon da nayi dazu naci na koshi domin ni cuta bata hanani cin abinci,komai rashin lafiya sai naci na koshi nayi luf,bayan naci Ammah ta dinga ballo min maganin tana bani ina sha har na gama,tace kawo na shafawa na shafa miki,Ammah zan shafa ki barshi kinga ke ba lafiya gareki ba, bayan na shafa jikin Ammah na koma na kwanta ina tunanin Saurayin dazu tare da maganganun da naji sunyi nake ta faman tunani shi kuwa mene tarihinsa me mutanen nan suke nema dashi ne haka,tunowa da nayi irin rashin Imaninsa nan take na firgita tsoronsa ya kara shigata na kankame Ammah har bacci ya kwashe ni,. Washe gari da asuba da kyar na tashi na gabatar da Sallah tare da Azkhar kamar yanda muka saba gaba dayanmu,Bayan gari yayi haske naje da Sauri na hada wutar itace na daura ruwan zafi yana tafasa na dama koko sannan na kafa daya kaskon gefe daban na fara suyar kosan siyarwa ta,ana sallama ana siya sai kuma ruwan zafi ya tafasa na kwalawa su Ma'eeshah kira suzo suyi wanka su wuce schl,da Sauri sukayi wanka suka shirya tsab cikin Uniform dinsu wanda yasha wanki da guga,Kokon dana dama musu suka eba tare da kosan suka ci suka koshi sannan suka kaiwa Ammah nata itama,Nima ina aikin Suya kosan siyarwa ta ina shan koko da kosai na ,Sister ya jikin naki gashi kumburin ya baje,murmushi nayi tare da cewa Alhmdllh kuje kar kuyi late ayi karatu da yawa banda wasa,bani da burin da ya wuce naga kunyi karatu sisters ku dage cikinku mu samu lauya da Doctor dariya suka dingayi Ammah ma tana tayasu cike da tausayawa Mufeeda,kudin Break na mika musu nace gashi yau ba ashirin za a baku ba Hamsin Hamsim zan baku kuci me dadi,murna suka dinga yi suna tsallen murna tare da godiya,Nace kuje mana Gashi karbi Meenat kece babba kuyo mana Cefane muyi miyar egusi da tuwon shinkafa ki taho da nama na dari Uku muma muci dadi ko Ammah? Murmushin farin ciki Ammah ta saki tare da kallona tace Allah ya muku albarka dai yaran nan,
bayan sun tafi na gama siyar da kosai na ya kare kaf ,ina ta faman murna na lallaba jikina na gyara gidan fes na tattaro kayanmu har na Ammah da kannena na wanke su fes na shanya,Ammah wacce ta rarrafo ta zauna saman tabarma tace Mufeeda me za a dafawa yan makarantar ne yau? Na gaji taliya zan dafa da mai da yaji kafin dare sai muyi tuwon,eh hakan ma yayi ai tunda muna samun na sawa a bakin Salati ba kamar lokacin baya ba,tashi ki kokarta ki gama ke ma ki kwanta ki huta idan sun dawo yau ba Islamiyya sai suyi girkin daren,amsawa nayi da to na mike nayi abinda ta Umarceni,na hada mata ruwa na kamata har Nayi tayi wanka fes na koma na riko ta muka dawo naa tayata shiryawa tsaf muna hira.
ina gamawa na hada yaji me dadi yasha hadi na soya manja,na gyar dan kitchen dinmu wanda yake na karfen langa langa ne,Ammah na zubawa na kawo mata tare da ruwa,taimaka mata nayi ta zauna nima nasa hannu muka ci muka koshi muna Bada dunkulen Maggi star,Sallah muka gabatar ta Azahar,sai ko mukaji Sallamar Yan makaranta su Meenat,da gudu suka shigo suna sallama suka rungumeni,Ido na waro mene hakan? Sis wlh wani ne yace yana son Ma'eeshah mu kuwa muka zabgo da gudu,ke kin ganshi wlh in banda wari ba abinda yakeyi wai yanzu Ammah duniya ta lalace me kudi bazai Hulda da talaka ba komai kyanka indai ku talakawa ne babu me kulaka sai talaka dan uwanka,Ammah tace ai duniya haka ta koma idan da gate a gidanku to me mota ne zaizo idan babu kuwa sai dai dan uwanka talaka,Yanzu kalli irin kyawu da Allah ya zuba muku Amma babu me zuwa wajenku talakan ma ya gagara sabo da talakan ma gudun talakawa yake Allah kayi mana magani,dan baki na na turo Ammah ke komai kice aure wai shekarunmu nawa,dan gidanku gata nake nema muku yanzu ko idan da kunyi aure ai kuna da yancinku ko ba komai sai kiga kun huta shine burina,Ammah wa zai kula dake to aini aure bai taso ba a wajena Ammah wlh Bazan iya aure na barki a haka ba ko da kuwa zan dawwama ba aure ne a duniya,ki daina zancensa indai kina so hankalina ya kwanta,Maeeshah tace Sis manya bari muyi girkinmu,harararsu nayi nace kuje dai ku cire Uniform kuci abinci kuyi sallah ku huta sai kuzo ku fara aikin,ni yanzu kun san kasuwa zanje siyo kayan da nake siyarwa citta,kaninfari,barkono,wake,kanwa,Sabulu,omo,maggi kala kala,har su Aya duk siyarwa nakeyi duk wasu kana nan Abu na amfaninmu kayan girki ina siyarwa a gidanmu,haka ina saida su Aya,ridi,kantu,alewar Madara,albishir etc su Ma'eeshah nake sarowa suna Tafiya min dasu makaranta su siyar min,ina kosai na siyarwa,da rana na siyar da su Zobo kunun zaki da dare kuma nayi Awara,ina kitso da zanen lalle sosai kudi idan sunzo zanyi na karbi kudina,sannan ina cikin masu polio rigakafi,duk wani neman kudi na Sana'a kanana na gida ina yi,kusan komai ma siyarwa nakeyi,kullum bani da lokaci bana zama sam sai neman kudi dashi muke ci muke sha,muke Sutura tare da makaranta,
biyawa Ammah kudin magani,yanzu kasuwanci a duniya shine buri na wanda har ya kai ga dasa min matsiyaci son kudi tare da tattali,iya lissafi da planning,sabo da yawan Hulda da mutane yasa na kara gogewa na waye sosai,akan kudi ba mutunci ko bashi ya shiga tsakanina da mutum akan dan Kasuwanci na to fa zan iya rufe ido dole a bani ma,kamar zanyi sata haka nake matukar neman kudi.
Yau Monday Su Meenat suna schl na gama komai na fita naje wajen saro kayan Yara na sha,ina siyowa kala kala har su tuwon madara na wuce schl na kaiwa su Ma'eeshah domin su siyar,ina zuwa na hango Malam ya sa Ma'eeshah kamun kunne ya hanata ko shiga aji wai sun makara.
Ina matukar Jaje gareku fans da raguwar shekaru da muka samu domin ba karuwa shekarunmu suka yi ba raguwar suka yi,ana ta happy new year a daina addua ya dace muyi Allah yasa mun shigeta a Sa'a tazo lfy ta wuce lfy,Allah yasa ta Zama shekara me amfani a Rayuwar mu,ta zame mana farin ciki da samun ci gaba a cikinta,Allah ka kara mana lfy da Nisan kwana me amfani,Allah ka kara mana imani,Allah yasa muyi karshe me kyau idan tamu tazo,Allah ya azurtamu da mutuwar shahada,Allah ya rufa mana asiri duniya da lahira Ameen.
Hausa novel daga muallarhausa.com.ng