WANE NE UMAR?KUMA MENENE KADAN DAGA FALALARSAmujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Saturday, January 26, 2019

Home › › WANE NE UMAR?KUMA MENENE KADAN DAGA FALALARSA

Subscribe Our Channel




WANE NE UMAR?KUMA MENENE KADAN DAGA FALALARSA?Umar shine umar ibn khaddabi,da ga kabilar bani addiyyi kuma idan ka bi silsilar kakannin umar daga na daya zuwa na takwas zaka taras sun hadu da manzon Allah s.a.w saboda kuraishawa ne gaba dayansu.Umar yana daga cikin manyan mutane tun a cikin jahiliyya,haka kuma a musulunci,har kuma mutuwarsa.kafin musuluntarsa Annabi xayi masa addu'a sau biyu shi da Abu jahal,sai Allah ya zabe shi don ya musulunta kuma musuluntar umar ta kawo ci gaba da daukaka ga wanna addini.[bukhari ya ruwaito].ABUBAKAR SIDDIKU R.A shi ya zabi umar da khalifanci lokacin da yazo mutuwa.kuma har yake cewa "idan na mutu Allah ya tambaye ni me yasa na baiwa umar shugabanci?to zance wa Allah "lallai na wakilta musu wanda ya fi su tsoron Allah".haka umar xayi shugabanci da siyasa da adalci irin wanda ba a taba gani ba, kum hakan ya bayyana ne saboda tsawon lokaci da yayi a mulki,idan ankwatanta shi da abubakar.ANNABI S.A.W yana fada a wani hadisi cewa:"Nayi mafarki sai na ganni a kan wata rijixa tare da Abubakar da umar.sai na debi ruwa na sha.bayan na sha sai Abubakar ma ya debo ya sha amma a cikin dibannasa akwai rauni,sanna sai umar bin khaddab ya karba yana karba sai abin diban ruwan yazamo kato<babba>umar bai gushe ba yana ta diban ruwan nan har ya shayar da mutane gaba daya[bukhari ne ya ruwaito]A wanna hadisin manzon Allah xa nuna cewa bai taba ganin mutum mai kokari da jarumtaka irin ta umar ba.don haka malamai ke cewa wanna Annabi s.a.w yana nuna ci gaba ne da kuma bunkasar da daular musulunci za ta samu a lokacin sayyidina umar.saboda a lokacin umar ne r.a akayi yake yake manya manxa wadanda suka zama rabewa tsakanin karya da gaskiya.a lokacin umar ne akayi yakin kadisiyya,da Nahawali wanda ya karya daular maguzawan farisa ta iran.wanda shi'a ke jida ita.a lokacin akayi yakin yarmuk wanda ya karya kiristoci.YANA DAGA FALALAR UMAR ANNABI S.A.W KE CEWA:A CIKIN BANI ISRA'ILA ANA SAMUN MUTANE WADANDA ALLAH YAKE SA MUSU DACEWA DA ABINDA SUKA FADA  ZAI ZAMA DAI,DAI TO A WANNA AL'UMMAR KUMA SHINE UMAR.YANA Daga cikin falalar umar annabi s.a.w yace Nayi mafarki kowa da riga wani ta dangale masa,amma shi umar tasa har jan kasa takeyi.sai aka tambayi annabi s.a.w mene ne fassarar wannan?sai yace Addini ne na umar cikakkake "kuma annabi s.a.w yace duk lokacin da umar ya hau hanya to shaidan sai ya canja hanya.zamu gaji don falalar dayawa,amma dai zanci gaba akan mutane goma da aka musu busharan aljanna lokaci guda.ALLAH YA TAIMAKE MU

No comments:
Write Comment