Mujallarhausa.com.ng: ADDINI mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Showing posts with label ADDINI. Show all posts
Showing posts with label ADDINI. Show all posts

Saturday, January 5, 2019

Banbancin duniya da lahira

BAMBANCIN DUNIYA DA LAHIRA

DUNIYA: babu tabbas
LAHIRA : akwai tabbas
DUNIYA: akwai mutuwa
LAHIRA : babu mutuwa
DUNIYA: akwai samu idan aka rasa
LAHIRA : babu samu idan aka rasa
DUNIYA: akwai rashi idan aka samu
LAHIRA : babu rashi idan aka samu
DUNIYA: karya ce
LAHIRA : gaskiya ce
DUNIYA: akwai najasa
LAHIRA : babu najasa
DUNIYA: tana gushewa
LAHIRA : bata gushewa

DUNIYA: akwai tsanani ga muminai
LAHIRA : akwai dadi ga muminai

DUNIYA: akwai dadi ga mushrikai
LAHIRA : akwai tsanani ga mushrikai
DUNIYA: masu tsoron Allah sune ake wulakantawa LAHIRA : masu tsoron Allah sune ake girmamawa

DUNIYA: mafi yawan masu kudi suna cikin jindadi LAHIRA: mafi yawan talakawa suna cikin jindadi
DUNIYA: gidan da ba'a bambanta mumini da kafiri LAHIRA : gidan da ake bambanta mumini da kafiri

wannan shine kadan daga cikin bambancin duniya da lahira,
ya kai 'dan uwana a musulunci, ina maka nasiha da kaji tsoron Allah kayi adalci a cikin addininka ka guji zalunci, domin zalunci yana kama da shirka, ka guji karya domin tana kama da bautawa gumaka.

ya kai musulumi ka sani cewa ba zaka zama mumini ba, har sai ka kasance kamar haka:

1 sai kaji tsoron Allah a cikin sallar ka
2 sai ka hakura da yawan wasanni
3 sai ka zama mai bada zakka
4 sai ka kiyaye farjin ka daga zina
5 sai ka zama mai alkawari
6 sai ka zama mai amana
7 sai ka zama mai kiyaye sallolinka

haka kema 'yar uwa sai kin kiyaye da wadannan abubuwan sannan zaki zama mumina kuma kamilar mace a cikin al'umma sannan kuma ki zama uwa ta gari

Allah yasa mu dace, idan ka samu dama ka tura wannan bayanin zuwa, wasu al'umma, yin hakan zai sanya ka samu lada mai yawa a wajen Allah, domin ka yada abun da yake mai kyau, amma idan baka tura ba babu laifi a gareka, sai dai kawai ka zama marowaci, kuma ka zama daga cikin wadanda basa hani da mummuna, kuma basa umarni da kyakkyawa,  Ya Allah kajikanmu ka yafe mana kura-kuranmu kada ka vssanya riya a cikin ayyukanmu 

Hira Mai Ratsa Zuciya Daga Majalisar Annabi (SAW)



Hira Mai Ratsa Zuciya Daga Majalisar Annabi (SAW)

.

Wata rana Manzon Allah (SAW) yana zaune tare da Sahabbansa, sai ya fara tambayar su daya bayan daya, sai ya fara da Sayyidina Abubakar 'yantaccen wuta

Yace Yaa Abubakar! Me kake so a duniya? Sai Sayyidina Abubakar yace: abinda na fi so a duniya_

1: zama a gaban ka,

2: kallon ka,

3: ciyar da dukiya ta gare ka.

Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar dan Khaddabi mai abin mamaki

Manzon Allah (Saw) yace: yaa Umar! Me ka fi so a duniya?

Sai Sayyidna Umar yace : abinda na fi so_ 1: a mini umurni da kyakkyawan aiki ko da a boye ne, 2: a mini hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne, 3: da kuma fadin gaskiya ko da tana da daci.

_Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman dan Affan, yace masa: "yaa Uthman! Me kafi so a duniya?_

_Sai Uthman dan Affan yace: abinda na fi so a duniya_ 1: ciyar da abinci ga mabukaci, 2: yada sallama, 3: yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci.

_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma ta wajen Aliyyu dan Abi Daalib, yace masa: "yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?_

_Sai Sayyidna Aliyyu yace: abinda na fi so a duniya_ 1: Azumi a lokacin rani, 2: Karrama bako, 3: yakar abokan gaba da takobbi.

_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari, ya ce masa: "yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya?_

_Sai Abaa Zarri yace: abinda na fi so a duniya_

1: yunwa,

2: jinya,

3: mutuwa.

_Sai manzon Allah (Saw) yace: "sabida me yasa kake son su?_

Sai Aba zarri yace:

*ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,n*ina son jinya ne don zunubi na yayi sauqi, *ina son mutuwa ne sabida saduwa da ubangiji na

_A wannan lokacinne Mala'ika Jibrili ya sauqo zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ), sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku_

1: isar da sako,

2: bayar da amana,

3: son nakasassu.

_Daga fadin haka kuma sai ya tashi zuwa sama Sannan ya sauko a karo na daban sannan yace Allah madaukakin sarki yana karanta muku sallama Hirar manzon Allah da sahabbai tayi dadi, harma Allah yana gaishe su sannan Allah yace yana son abubuwa uku a duniyar ku_

1: harshe mai ambatonSa,

2: zuciya mai tsoronSa,

3: jikin da aka jarrabce shi da balaa'i kuma yayi hakuri.

_Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah Girma da tsarki sun tabbata ga Allah_ Adu'o'i guda uku kada ku manta su acikin sujjadarku Ya Allah ina rokonka kyawawan halaye".

"Allah ka azurta ni da tuba zuwa gareka tabbatace Ya ALLAH mamallakin zuciyata ka tabbatar da ita akan addininka"

Lalle wannan ya cancanta ku tura zuwa ga waninku domin ya amfana.
Dauki darasin ka a cikin wannan hadith, ka aikata shi, za ka yi nasara.

Majalisar Manzon Allah makarantar mai imani ne, yi kokari ka fita a sahun farko na daliban makarantar. Kayi sharing a sauran groups domin yan uwa sugani su amfana