HAUSA NOVEL IN SO CHUTANE NA 1mujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Saturday, February 16, 2019

Home › › HAUSA NOVEL IN SO CHUTANE NA 1

Subscribe Our Channel



*Godiya ga Allahu (S.W.T) mai kowa mai komai da ya bani ikon fara wnn novel cikin koshin lafiya.*

*Alhamdulillah Hamdan katheeran d'ayyiban mubarakan fiih.*


*Fatan alkhairi gareku masoya aduk inda kuke ,ku ke bani kwarin gwiwa ako wani lokaci nagode kwarai da gaske Allah ya bar k'auna.*


****** ***** *****


Da d'add'aya suke fitowa, dan zuwa ganin Wannan mai sa'a da ya sace zuciyar yayarsu har ta fita ta saurareshi. 


Ba ma fitar ne yafi basu mamaki ba, sai jimawar da tayi wajen zance daga cewa bari Inga waye ne in dawo. 


Kanwarta mai bi mata Nusaiba,wacce kusan kansu d'aya ita ta fara zuwa ta gaisheshi, sai Fati, itama taje da sunan taje gaisheshi, daga nan sai kannenta maza Nafi 'u da Hamza .


D'an autansu khalil ne kawai baije ba .dan shi d'an ba ruwana ne.

Gulma ajali. 

Hhhh gulma harda maza. 


Abinne kam da mamaki dan ko Mamansu da suke kira da Ummi ma cikin mamaki take fitar 'yar tata da rashin Dawowarta da wuri.


 Ummussalma kenan 'ya ga Mal. Abdullahi. 

Mahaifin Ummussalma Babban malami ne wanda yake karantar da manyan mutane da matasa. 

Har islamiyya na musamman ya bud'e kusa da gidanshi dan koyar da yaranshi da na makwabta. 


Cikin ikon Allah islamiyyar ta hab'aka har daga wasu anguwanni zuwa karatu akeyi .


Ummussalma wacce aka fi kira da Salma, kunnenta kuma suke ce mata Aunty Salma, itace 'ya ta uku a wajen iyayenta amma itace mace babba a gidan. 

Yayyunta biyu maza ne Allah yayi wa d'ayan rasuwa Saura d'aya wadda suke kira da Ya Al-amin. Wani lokaci su ce mishi yayanmu.


Tun tasowar ta tashi da burin ta zamo likita, ita kuwa a rayuwarta babu abinda yake burgeta irin taga nurses sanye da fararen kayannan Suna bawa mara lafiya taimako. 


Sosae take son karatu dan ita a rayuwarta babu abinda ya fiye mata karatunta muhimmanci. 


Tun gamawanta secondary school mahaifinta yaso ya aurar da ita amma ganin yadda ta nace kan karatu kuma bata da wani tsayayye dan ita Sam bata sauraron samari dan a ganinta b'ata lokaci ne, kuma hakan zai iya hanata karatunta yadda takeso. 


Babban abinda take gudu shine, kada babanta yasan tana da wani yace zai mata aure. 

Shi yasa Shima babannata ya hakura da batun aurar da ita kuma ya nema mata karatu a school of nursing.


Karatu take ba wasa dan samin cikar burin ta, kuma cikin ikon Allah tana samun nasara dan tunda ta fara bata tab'a samun matsala da karatun ba. 


Duk yadda wasu suke nuna mata Suna son ta, wasu ta hanyar kannenta suke bi,wasu kuma ta wajen yayanta wasu kam direct wajen Mal. Suke zuwa da bukatarsu ta aurenta, saidai yace musu sameta Su daidaita kansu dan shikam alk'awari ya daukarwa kanshi bazaiyiwa 'yarshi auren dole ba, ko wacce zai bata dama ta zab'i wanda takeso, nashi dai yayi bincike ne idan an dace da nagari Falillahil hamdu. 

Idan kuma akasin haka ne sai ya bata shawarar da zai amfaneta sai kuma ya bisu da addu'a. 


Samun ta a daidaitan shine matsalar dan ko kad'an bata bada fiskar da za'a kawo mata irin wnn maganar ta soyayya. 

Ko yaya mutum yaso tunkarar ta sai abin ya gagara dan Allah ya bata baiwar k'warjini, ga uwa uba d'aure fiska da takeyi idan ta fita waje, ko da mutum yayi dauriya da k'arfin halin yi mata magana ma daga kallon da Zata maka zaka San babu nasara ,gata kullum cikin zumbuleliyar hijabi ,zaiyi wuya Kaga dariyarta shi yasa Yawancin mutane suke ganin zata yi wayar shaani. 


itakam haka yafi mata Dan babu wanda zai kawo mata cikas a Karatunta.


Kannenta ,Nusaiba da Fatima duk suna da masu zuwa wajensu, fatimar nema Salma take hanata fita a cewarta idan auren takeso ma ta bari sai ta K'are secondary school. 

Itama Nusaiba dan ta K'are ne.


Wani lokaci haushi suke bata idan taji Suna maganar soyayya, ko kuma idan aka ce wani yazo wajensu taga suna rawan Kai. 


Yawancin mutane Suna gani girman kai ke damunta ko kuma dan taga tana da kyau yasa takeyin  hakan wasu kuma cewa suke mai kud'i take son ta aura. 


Saidai abin mamakin masu kud'in ma ba sauraransu takeyi ba. 

Abinda basu sani bama shine ita Sam a tsarinta bata son auren mai kud'i dan gani take auren mai kud'i sawa Kai damuwa ne. 

Na farko gani take kamar baza ta samu attention d'inshi yadda ya kamata ba.


Ta iya yiyuwa ta zamo kamar abokiyar gabar danginshi dan zasu sa mata ido sosae ganin d'an uwansu na da kud'i. 


Gani take shi dinma zai ga kamar dan kudinshi takesonshi ba dan Allah ba. 


Shi yasa take da burin idan Zata yi aure ta auri talaka d'an uwanta mai rufin asiri wanda kuma zai barta tayi aikin asibiti su zauna lafiya su rufawa juna asiri.


No comments:
Write Comment