NAGARTA WRITERS BA MAKAUNIYAR HANYA BACE Daga alk'alamin mujallarhausamujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Saturday, January 5, 2019

Home › › NAGARTA WRITERS BA MAKAUNIYAR HANYA BACE Daga alk'alamin mujallarhausa

Subscribe Our Channel


Daga alk'alamin mujallarhausa Wannan labarin ban yi shi dan cin fuska ga wani ko wata ba, idan har yazo dai-dai da rayuwar ki/ka akasi aka samu Ina rokon Allah yanda na fara lafiya yasa na gama sa lafiya. Allah yabani ikon rubuta abinda yake alkairi

Dedicated to my mentor Lubabatu Sani Maitafsir Jinjina ta musamman ga Meemi Bashir (queen) Page (1)

TWO MONTHS EARLIER
Sassanyar yammaci ne mai d'auke da iskar damina, yanayin iskar garin cike yake da ni'imar dake sanya
natsuwa a zukatan mutane musamman wad'an da suka kasance masoya Amma a bangaren ta akasin hakan ne ya kasance, duk da dad'i da yanayin da garin yake ciki tafe take tana jimami cikin zuciyarta.
'Wannan wace irin rayuwa ce haka ta
same ni! Ace ba kada 'yancin zama bisa inuwar wani? Sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya A wasu 'yan shekaru baya kad'an da suka shud'e, tana d'aukar kanta cikin jerin Mata masu tsananin nasara da cikakken sa'a a rayuwa, amma sai gashi lokaci guda d'aya tak! Ya zamo sanadin sauya saitin agogon rayuwarta gaba d'aya Lokacin da yafi komai tsada a gareta Ya janyo sanadin kasancewarta tamkar mujiya musamman wajen
mutanen da watanni kad'an baya suke d'aukarta a matsayin wata fitila wacce zata zamo mai haska birnin
zukatan su uku K'arar birkin daya
taka ne da k'arfin tsiya, shine yayi sanadiyar dawo da Zuciyarta daga
kogin tunanin da ta kasance ciki
dak'ik'u kad'an baya wanda suke barazanar aikawa da ita garin da ba a dawowa Sai dai Koda ta farka daga duniyar tunanin data fad'a
hakan bai sanya ta iya k'ara ko da
taku d'aya ne daga inda take tsaye, wanda zai iya kai rayuwarta ga
matsera ba. Cikin izza ya fito daga motar tasa ganin matashiyar
yarinyar da a kallon sura na zahiri ba
tayi kama da mai tab'in hankali ba, amma gata akan tsakiyar hanya tana tafiya, ba tare da tayi duba ga gudun fad'ama ababen hawan dake ta zirga-zirga bisa kan hanyar ba.
Baiwar Allah lafiyar ki kuwa kike
tafiya bisa tsakiyar titi ba kya gani sosai ne Kyawawan fararen idanunwanta ne suka samar wa
kansu masauk'i cikin nasa idanun,
wanda nan take hakan yayi sanadiyar kunna wani hasken wuta cikin zuciyar natsattsen matashin saurayin dake tsaye gabanta "Tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi wannan kayakkyawar halittar

Bai san maganar tasa a fili yayi ba,
gabaki d'aya zuciyarsa ta shagaltu ga kallon kyakkyawan yarinyar
dake tsaye gabansa. Da alamu shimaya shafa'a da
cewa a tsakiyar hanya suke.
Wani k'arar horn din ne ya sake
karad'e kunnuwansu,
sai dai a wannan karon da alama
masu tab'in hankalin
su biyu ne bisa tsakiyar titi.
Ganin ba ta da wata alama ta motsawa daga inda take
tsaye, yasa shi janyo ta daga kan
hanyar. Hak'uri ya koma yana bawa mutanen da suka soma
hayaniya a wurin, kasantuwar motar
sa daya bari rabi
da rabi kan hanya, ya yi sanadiyyar
had'a d'an matsak'aicin hold up a gun Kafin ya gama fakin d'in motar nasa inda ya dace, ya
hango wannan yarinyar ta ci gaba da
tafiya da alama
jiri take gani, cikin hanzari ya fito
daga motar nasa,
amma kafin ya isa gareta hangowa
yayi ta yanke jiki ta
fad'i k'asa. Cikin bugawar zuciya wanda tun sa'ar da suka kalli
juna ido cikin ido da yarinyar yake
jinsa, ya kuma rasa
menene mak'asudin hakan, ya k'arasa wurin da take.
Da taimakon wasu mutane suka sanya ta cikin motarsa, Medicity hospital dake G.R.A
malali ya nufa da ita Yana kwance a kan shimfid'arsa na bacci tunanin
yarinyar nan daya ci karo da ita
kawai yake, yanayin da
ya ganta ciki ya jefa zuciyar sa, cikin
kogin tunani,
muhimmin abinda yafi damun sa
shine rashin Sanin
hak'ik'anin wacece ita, bata dawo
cikin hayyacinta ba har ya baro asibitin, gashi ba waya a
tareda ita balle
yasan a ina yan uwanta suke.
Haka yayi ta faman birgima da
tunane-tunane kafin
b'arawo barci ya sace shi
A zahiri kuma tunda ya koma gida
duk lokacin da
tunanin ta ya fado masa, sai ya rinka
jin fad'uwar gaba.
Bai fad'awa Mahaifiyar sa wani labari dangane da had'uwarsa da yarinyar ba, ya d'an jira tukunna domin akwai hadafin da yake da a kanta, mai yuwawa ita ce
silar samun mafitar sa!.
Wata k'anwar abokinsa ya nemi
alfarma ya kaita can
asibitin ta zauna da yarinyar, domin
k'anwarshi Saudat tayi tafiya ba ta gida, kuma ko da tana nan ma bai so
su san da batun ta tukun

2DAYS LATER
Yau kwana biyu kenan da kai
matashiyar yarinyar nan
asibiti amma har zuwa yanzu bata
farfad'o ba. Sai dai
a yau likita ya bashi tabbacin cewa
ana sa ran zata iya
farkawa a kowane irin lokaci.
Shigowar sa gida kenan daga asibitin yake, bayan sun gaisa da Mahaifiyarsa Hajiya Aisha, ya doshi matakalar benen da zai sada shi zuwa d'akinsa. "Irfan!" Hajiya Aisha ce ta kira sunan d'an
nata. Cike da damuwa shinfid'e bisa fuskar tasa ya waigo,
inkiya ta mai da idanunta alamar ya
dawo gareta, jiki a
sanyaye ya k'arasa kusa da inda take zaune bisa kujera, a k'asan lallausan kafet d'in
dake malale cikin
d'akin ya zauna, domin nuna
girmamawa gareta yace
"gani Mommy Akwai abinda yake damunka kwana biyun nan ina lura da kai, ko sharad'in da Abban ku ya
gindanya maka
ne? Ya gyad'a Kai alamar A'a.
"Amma kuma nayi dogon nazari akan ka na gano wasu
sabbin canji a tare da kai, dan harta
da yanayin shigowar ka da fitar ka gidan nan duka sun canza In har yarinyar ce ka samu to menene kuma ya kawo damuwa da rashin walwala, ina son jin dalilin damuwar
ka?". Soshe-soshen k'eya ya fara da 'yan kame-kame Domin a zahirin gaskiya bai san ta ina ma zai fara ba. Yace mata ya samo yarinyar da zai aura alhali yarinyar bata ma san inda kanta yake ba? Yarinyar da bata san ko wanene shi ba, bai da tabbacin
ma shin za ta amshi tayin soyayyar da zai yi mataKa samo yarinyar ne nace ka yi shiru Shin 'yar gidan wanene kuma a ina take, tambayar ka nake? Hmm mommy
dama dama bandakatar dashi tayi da hannunta. Bana bukatar b'oyo ka fito fili kawai kamin bayanin abinda na tambayeka, shin ka sami yarinyar ne Eh! Ko A'a  Eh! Na same taYa tsinci kanshi da furta kalamomin da bai san daga ina harshen sa ya lalubo su ba, har suka kai ga k'ok'arin fitowa daga bakinsa. Har ga Allah ba abinda yayi niyar fad'a ba kenan amma dama 'baki shike yanka wuya To 'yar gidan wanene, a ina suke da zama 'yar nan garin ce ko ko?

Kalamanta suka yanke mai zancen
zucin da yake yi. Ban san ko 'yar gidan wanene ba Mommy, kuma yanzu haka ma maganar da muke yi tana asibiti Asibiti! Meya Kai ta asibiti kuma? Itace ba lafiya ko wani ne dai...?". Bayi da wani zab'in daya wuce ya fayyace mata komai. Nan dai ya zauna ya zayyane mata
abubuwan da suka faru tun daga farko har karshe, bai so sanar da ita halin da yarinyar take ciki ba a yanzu, ba tareda ta farfado ba, yaso sai ya fara sanin ko
ita Wacece, daga inda ta fito, ya kuma ji ra'yinta akansa, dan yau kwana biyu da tsintarta da yayi, amma ya na jin zuciyarsa dumu-dumu cikin soyayyarta!. Sannan gashi yanzu ya na gabatar da ita gun mahaifiyarsa, a matsayin wacce zai Aura Lallai wannan shine riga malam masallaci'. Ya fad'a cikin zuciyar sa

No comments:
Write Comment