KARANCIN TAUSAYI DA TAIMAKO A AL'UMMARMU TA YAUmujallarhausa.com.ngMujallarhausa.com.ng mujallarhausa










Home Hausa Novels| Sabbin Hausa Novels Sirrin Android Addini Hausa fim Fitattun Labarai Hausa Novels Downloads Kannywood MTN Music-Promoted Labarai wasanni

Sunday, January 6, 2019

Home › › KARANCIN TAUSAYI DA TAIMAKO A AL'UMMARMU TA YAU

Subscribe Our Channel


KARANCIN TAUSAYI DA TAIMAKO A AL'UMMARMU TA YAU Rayuka da yawa sun salwanta sakamakon hakan

YADDA KUDIN HAYA SUKA ZAMA AJALIN WANI MAGIDANCI
Ana qoqarin rufe gidanshi saboda bai samu kudin haya ya biya ba...Sai ya nemi bashin kudi a hannun manajan kamfanin da yake aiki bai samu ba... Ya tuntubi attajirin unguwarsu nan ma bai samu ba... Sannan ya kira yan uwanshi a waya nan bai dace ba...

Sai yayi post a facebook wall dinshi yana neman taimako, amma iyaka abin da ya samu shine: 2likes da kuma 0 comments ...

Sai ya tura messages guda 120 zuwa ga abokanshi da suke contact list dinshi yana neman su rantamar dubu #100,000:00... Abin haushi mutane 10 ne kawai suka yi reply na message din... 6 daga cikin 10 suma suka ce basu da abin da zasu bashi.. Mutum daya daga cikin 4 ne kawai ya bashi dubu 20 amma sauran sai uzuri suke badawa qarshe ma suka daina daukar wayarshi...

A hankali har lokaci yayi maigidan haya ya kulle gidan, Ya bar iyalinshi a kofar gidan tare da tarkacen kayansu... Ya shiga lungu da sako bai samu tallafi ba har dare yayi... Yana tafiya a cikin duhu yana neman mafita sai ga babbar mota ta bi ta kanshi nan take ya mutu...

Washegari sai labarin ya cika gari da labarin mutuwar shi... Facebook friends dinshi mutane dubu 2220 su kayi posting a wall dinshi suna jimamin mutuwar shi tare da fadin kyawawan halayenshi...

Maigidan hanyar da ya samu labari da gudu ya zo ya budewa iyalinshi gidan yace su shiga ciki domin amsar ta'aziyya...

Attajiran unguwarsu wadanda suka hanashi bashin kudi suma suka kwaso kayan abinci da kudin cefene a ba iyalin mamacin domin dafawa baqi masu zuwa karbar gaisuwa.

Daga bisani sai aka fara shirye-shiryen binneshi... Inda anan take kwamiti na abokanshi suka tara kudi masu yawa ta hanyar karo-karo... Domin ciyar da bakin da zasu zo daga wurare daban-daban...

Abokan wajen aikinshi suma suka tara kudi masu yawa domin kar6ar rumfuna da kujeru da kuma sauran abubuwa...

TO WAI DUK MENENE WANNAN DIN? Me yasa ba zaku taimaki mutum a lokacin da yake buqatar taimako ba har sai mai kasancewa ta kasance?

Me yasa bazamu bi koyarwar addinin musulunci ba, ta hanyar taimakawa 'yan uwantaka da zaman tare?

Ire-iren wadannan halaye namu sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama? Mata da dama sun zama zawarawa...' Ya'ya da yawa sun zama marayu. 'Yan mata barkatai sun zama karuwai. Mutanen kirki da yawa sun fada ga  halaka.

AKWAI BUKATAR MU SAUYA IRIN WADANNAN  MUNANAN HALAYE, TARE DA TAUSAYAWA NAKASA DAMU DA KUMA JIN KAI GA MASU KARAMIN KARFI DA MARAYU. DA WANNAN SAI ALLAH UBANGIJI YA YALWATA MANA ARZIKINMU YA TAIMAKI IYALANMU KO DA BAMA RAYE.  ALLAH YA BAMU IKON TAIMAKAWA AMIN

No comments:
Write Comment