Wannan shine KO MENENE RELAY?
KUMA MENENE AMFANIN SA ?.
Relay wani component ne wanda
akesamunsa acikin na,ura daban
daban. Wanda aikinsa shine kunna
wani bangare daga jikin na,ura ko
kuma kashe wani sashi daga jikin
na,ura domin tsayar dashi daga aiki.
AMFANIN RELAY GA AJIKIN NA,URA.
1. Yana daga cikin amfanin relay
acikin stablazer wajen saita wuta mai kyau domin kare duk wani hatsari wanda zai kaiga konewar tv ko freezer koma duk wani na,uran
dayake jikin stabilizer. Relay ne fa
kakejinsa yake wani Qara ajikin
stablazer idan wuta yanayin Rawa
zakaji stabilizer yana wani dan Qara
kamar haka *Qat Qat*. yanayin haka
ne idan yaga wuta ya rago saiya kara, ko kuma idan yaga wutan ya karu sai ya rage wutan yadawo normal tayadda bazai kona maka appliance (na,uran wutan lantarkin da suke jikin stabilizer din kaba). Duk relay shike wannan aikin.
2. Relay ne fa yake tayar wa ko kuma
ince kunna wutan ignition din duk
wata mota. Shiyasa idan mai karatu
ya lura da kyau, aduk lokacin da kake
cikin mota , idan motar tana kashe.
Idan kuna jin radio a misali, idan
driver yazo zai kunna motar kalura
zakaji radio din motar sai ya dauke
sai bayan tagama tashi sai kaji radio
din motar yaci gaba da playing, to
duk wannan yana faruwa ne adalilin
relay, saboda relay ne yake raba
layin wutar radio din motar daga
jikin batir din saboda load din dake
jikin batir din ya ragu domin batir din
yasamu Qarfi sosai tayadda zai iya
tayarda motar idan anyi mata key.
Duk wannan relay ne keyin wannan
aiki.
3. Yana daga cikin aikin relay kunna
waifa, wanda yake sharewa ko kuma
ince goge glass idan ana ruwa, idan
kalura zakaga waifa din idan yagoge
glass din sai kuma kaga yana hutawa.
Can anjima kuma still sai kaga yaci
gaba da goge glass saikuma yasake
hutawa. Duk irin wannan aikin relay
ne.
4. Relay ne fa yake aiki ajikin na,uran
dake kera mota da jirgin sama da
kamfanin mashin dakuma kamfanin
duk wani na,ura shi yake kunna duk
wani machines don yin aiki. Saboda
shi relay yana da high tolerating na
current.
5. Relay shine yake aiki a traffic na
hanya, wanda yake tsayar da motoci,
bayan ya sallami wannan hanyan sai
kuma ya sake sake bama wasu hanya,
wanda zakaga koyin wuta red green
da yellow. Duk wannan aikin relay ne
yake kunna wannan koyayen ,idan ya
tsayar da wancan sashin saikuma ya
kunna wuta ma wanda zai ba ma
dayan hannun matafiya daman
wucewa
7. Kuma shi relay yana aiki hatta
awajen sadarwa tsakanin wancan da wannan, domin yakan datse layan
sadarwa tsakanin wancan da
wannan, yakan kuma jona wannan da wancan. Aduba littafin the encyclopedia of electronics volume 1 2+
No comments:
Write Comment