A DAURE A KARANTA DON ALLAH.
SHIN KA TABAYIN ZINA?
Fitinar Sha'awa kashi na 04.
Tsaya kuji irin mummunan Bala'in da zina ke haifarwa. Zina tana cikin manyan laifuffuka, wanda dukkan shariun da Allah ta'ala ya saukar sun hadu akan haramcin zina.
Al kur'ani mai girma da Sunnar Annabi (S.A.W) da dukkan Malamai sun hadu akan haramcin zina.
Qofofin zina guda biyar ne kamar haka:
1- Kallo zuwaga Abinda Allah ya Haramta.
2- Shigar batsa
3- Kalaman Batsa
4- Kebancewa da matar daba muharrama ba
5- Sha'awa Mai karfi babu aure
Allah taala yace:
"kada ku kusanci zina"
Manzon Allah (S.A.W) yace: Mai zina ba zaiyi zina ba, yayin da yake zina, sai an cire masa imani.
Abdulllah Dan Mas'ud Ra yace: Duk Al'ummar da take zina, ta jawo wa kanta fushin Allah, da halaka.
Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa guda shida sune kamar haka:
1-Addini.
2-Dukiya
3-Rayuka
4-Hankali
5-Mutunci
6-Nasaba
Amma zina ita kadai, tana rusa wadannan duka. Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar jifa. Saurayi mara aure Bulala dari da daurin shekara.
Ana tabbatar da zina ta hanya uku.
1-Shaidu guda hudu.
2-Mutun yayi ikirari da kansa.
3-Samun mace da ciki, babu aure, ko shubha.
Bisa sharudda da aka sanyawa ko wanne. Zina wata babbar musiface da bala'i da dukkan sharri, datake ruguza al'umma, take wargaza iyali, take tarwatsa gari, take rushe mutunci, take jawo karayar tattalin arziki, da fatara, da tsiya, da annoba, acikin rayuwar dai dai ku, da gidaje, da unguwanni, da gururuwa, da kasashe, da duniya baki daya.
Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun dukkan sharri kamar haka:
1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3- Karancin Imani
4- Rashin kunya
5- Rashin kishi
6- Rashin mutunci
7- Rashin kwarjini
8- Rashin hasken fuska
9- Duhun zuciya
10- Rashin kima
11- Rashin Nagarta
12- Rashin Nutsuwa
13- Rashin Amana
14- Fushin Allah
15- Cikawa babu imani
16- Azabar Allah.
Allah ya tsare mu da zuriyar mu, da dukkan
al'ummar musulmi daga afkawa bala'in zina.
Wadanda sukeyi Allah ya shiryesu.
Gabatarwa
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci
No comments:
Write Comment